Ticker

6/recent/ticker-posts

12.3 ‘Ya’yan Sarki Ado Bayero - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 512)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Ban raina ba komai an yi man ‘ya’yan sarki Ado Bayero.

'Ya’yan girma ‘ya’yan Bayero,

'Yan alfarma jinsin Bayero,

Halin baiwa tsatson Bayero,

Ban raina ba komai an yi man yayan sarki Ado Bayero.

Allah Rabba Sarkin rahama ga baƙonka Ado Bayero,

Mai soyayyar mai son annabi gatan mai son ay yabi annabi.

 

Mai Horewa, Sarkin hikkima mai yarjewa, mulki ai aro,

Na keɓe ka, bauta kai kaɗai na duƙa ma har na tanƙaro,

Kai baiwarka fannin hikkima sashen waƙe in na warwaro-

Nai shillawa sashen ɗaukaka, mai suka na jirgin danƙaro.

 

Ni ma na zam ɗa gun Sankano domin ƙaunar Ado Bayero,

Nai kuka don na rasa shugaba mai ƙauna ta Ado Bayero,

'Da ne ni mai nisan nassaba ba na gadon Ado Bayero,

Gadon ƙauna ita ni nar riƙe, ƙaunar sarki Ado Bayero.

 

Bayan ƙauna wacce na wa riƙon, har ban raina, Ado Bayero,

Kayan gado wanda ya bar mani ƙaunar 'ya’yan Ado Bayero,

Kayan gado ya kuma bar mani gadon koyi Ado Bayero,

Gadon ƙarshe wanda ya bar mani gadon kewar Ado Bayero.

 

Ga ɗan sarki Lamiɗon Kano babbar gayyar Ado Bayero,

Mai alfarma Mamman Adamu babban ɗa gun Ado Bayero,

Mai murrabus chiroman Kano kai ɗai gayya jinsin Bayero,

Jikan sarki ɗan sarkin Kano ɗan ‘yar sarki tsatson Bayero.

 

In ya gan ni Alan Sankano hannu bibbiyu ke mani warwaro,

Lale-lale kullum kamma ni yai man kyauta, kyautar kwarkwaro.

Mai alfarma Sanusin Kano ban raina ba jikan Bayero,

In an jure barar albasa a iskewa a ciki farfaro.

 

Sai tauraron ‘ya’yan Sankano rumfar giwa Ado Bayero,

Jajirtacce turke ƙi gudu makasau ɗan Ado Bayero,

Babban gawo ne wamban Kano ɗan takawa Ado Bayero,

Caffar ƙauna komai an mani don alfarmar Ado Bayero.

 

Komai nat tsara in na gama zan kai kuka gun ɗan Bayero,

In taso shi ya zamar min uba alfarsa Ado Bayero,

Bai ƙosawa bai gajiya da ni wamban sarki Ado Bayero,

Ban raina ba komai kun mani ‘ya’yan sarki Ado Bayero.

 

Babban jigon ‘ya’yan San Kano mai zatin sarki ɗan Bayero,

Mai alkyabba mai kyau mai ado mai iko tamkar ɗan Bayero,

Duk ɗan sarki mai wata taƙama in ya gan ka sai ya gangaro,

Nasir Ado ɗan sarkin Kano chirroman yau mai kayan karo.

 

Rumbun kyauta komai kai mani Nasir Ado sarki Bayero,

Saƙon rannan ka sa ai mani kyautar girma mai iddararo.

Ƙasaitarka na nuna mani zakkar 'ya’yan Ado Bayero,

Ban raina ba komai kum mani ‘ya’yan sarki Ado Bayero.

 

Barde babba jinsin Bayero alkhairi tamkar shukar tsiro,

Dukkan ƙwaya daga ƙwayar iri kas shuka ta ce za tattsiro,

In kai binnen ɗan ƙwayar tsiro, wannan binne shi ne zai tsiro,

Duk juyawa kwana dai ake kwana tashi komai zai tsiro.

 

Burin mai son yaz zama alhaji yai sallah can inda muka baro,

Baitullahi alharamaini can birnin manzo mai indararo,

Badde ke bi Kabiru Bayero ka nuna min ƙaunar zahiro,

Insha'allah Allah zai maka sakayya don zuba jari aro.

 

'Ya’ya sittin sittin da uku 'ya’yan sarki Ado Bayero,

‘Ya’ya mata kana ga maza ‘ya’yan sarki Ado Bayero,

Kulliyarsu kowa nai mani kallon ƙauna don ɗan Bayero,

Zan jera su tun daga can sama har can ƙarƙas in ɗan gangaro,


Tarihi ne in na yo haka domin ƙaunar Ado Bayero.

Bakin cizo shi ke dariya 'ya’yan sarki Ado Bayero,

Hannun kyauta shi ke kokawa 'ya’yan sarki Ado Baywro,

Hannun karɓa shi ke basuwa ‘ya’yan sarki Ado Bayero.

 

Wayyo kaico kaicon duniya mai ruɗarwa mai siddabaro,

Kaico kaico kaicon muttuwa mai yankewa ba wani mai tsaro,

Linzamina mai tuntuntuni ke nuna min ga ɗan Bayero,

Giwar sarki ita ke taffiya ranar sallah idi an baro.

 

Ga takawa ga ‘yan gaisuwa dodo dodo tamkarzanzaro,

Ga ‘yan sulke nai masa rakkiya sautin harbi tamkar bambaro,

Ga zaggage ga ‘yan kagira ga ‘yan bakka ga 'yan sintiro,

Ga fadawa nai masa jinjina suna haikawa dai Bayero.

 

Can sai ƙwalla tai wata tattara cikin idona ta kuma gangaro,

Sai ciwon kai yai wata mamaya saman kayina in ɗan kantaro,

Kaicon sabo kaicon muttuwa gwanar yankewa duk al'ammuro,

Gadon kewar kewar Sankano tana damuna har tai man tsiro.

 

Da na rintsewa sai tuntuni ya min ƙawanya mai siddabaro,

Ina kallon sa ga shi ƙiri-ƙiri kamar na sanya kofin micro,

A saukar yara ‘yan tahafizu masu saukar hadda ni na makkaro,

Ina kewarsa inda na waiwaya kawai takawa ne ɗan Bayero.

 

A yau shi ke nan yanzu da ni da shi kawai sai bege in na hallaro,

Da hoton motsi hoton tarihi da hoton girke wanda ka sandaro,

Yana ruhina don haka ne yana sahun waɗanda in na hallaro,

Cikin roƙona in masu addu'a barmin Allah mai indararo.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments