Ticker

6/recent/ticker-posts

Hasbunallahu wa Ni’imal Wakilu

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Hasbunallahu wa Ni’imal Wakilu

 

Farko da makkaɗaici sarkin da yai makaho,

Ya ƙagi mai gani yai shirwa ya ƙagi shaho,

Sarkin da don cikar hikima tai ya yo maloho,

Ilahu wanda yai suna yai icen maƙarho,

Ka ba ni hikkimar waƙa ya Al-muzillu.

 

Daɗo dubun salati gun sayyudul Aminu,

Yawan sanin da kay yi wa bawanka Mahhamudu,

Ga shugaban halitta gatan Arab da Hindu,

Mai taƙama da kai wanda ya zamma Mahhamudu,

Ka sa sahabihi da sharifai jinin batulu.

 

Allah kana gani maƙiya za su kassara mu,

Ka jefe su da cuta Allahu duka su samu,

Ka kama kawunansu ka ruguza su Alkarimu,

Allah ka mai da su bebaye da sun gane mu,

Haɗa su riggima Allah su da Jibbirilu.

 

Mai ƙin mu ko ina yake Allah ka jarrabe shi,

Da balbalin bala’i sa ac cikin jikin shi,

In ya yi addu’ar kuɓuta Rabbi ka shirye shi,

In ya ƙi yai nadama Allah ka murƙushe shi,

Ka rusa tanadinsu na sharri Almuzillu.

 

To wanda duk yake ƙin sana’armu nannaɗe shi,

In miƙaƙƙe ne shi Allah ka ranƙwafe shi,

In mai gani da ji ne Allah ka kurumta shi,

Ka ɗauki watta cuta ka sa cikin jikin shi,

Ka hallaka shi don Ibrahimul Kalilu.

 

 

 

In arziki garai Allah sa shi at talauci,

In wayayye ne shi sa shi ag gidadanci,

In kamilin mutum ne ka zubar mar da mutunci,

Karɓe baiwar da ka mar don ya yi ma butulci,

Haɗa shi riggima Allah shi da Jibbirilu.

 

Allah ka hallakar da daƙiƙin da yats tsane mu,

In ya yi aniyar cutar mu sa shi kar ya gan mu,

Kifar da maƙƙiyanmu don kar su hallaka mu,

Ya Almugni ya Shafi ka taimake mu,

Don martabar Muhammadu mai suna Jamilu.

 

Ya mai tsare halitta mun zo ka taimake mu,

Ka ba mu kariya kar wani ɗa ya addabe mu,

Allahu kai katanga ta tsari ga magautanmu,

Masu bibiyar ɓatanci ga sana’unmu,

 

Mun zamma sai ka ce jemagu da iyalanmu,

Mun zamma mujiya a cikin jinsin yarenmu,

Suna ta cin amanar bayinka cikin hammu,

Sun shigga innuwar al’adu addininmu,

Allahu don isarka da mu kai kaƙ ƙage mu,

Ka ba mu kariya don ƙaunar Abu Batulu.

 

Ya Ubangiji wanda ya zo da tanadin shi,

Yai nufin ya cuce mu kar ka taimake shi,

Ko tafiya zai yi ka bar shi yay yo da kan shi,

Idan ya ɗauki mota zai ja ta to ta ja shi,

Kwarab! Rugum! Kwatsam! Kakkarya shi Alwakilu.

 

Masu hassada Allah kar ka ba su sa’a,

Masu gulma Allah ka haɗa su das sana’a,

Wato irin sana’ar da cikinta babu sa’a,

Da sun yi yunƙurin sui gaba to ce musu a’a,

Haɗa su da aljan mai zafi Almuzillu.

 

 

Cuta ta ɗimuwa Allah sa a ƙwaƙwalwarsu,

Basir da shawara Allah sa cikin jikinsu,

Cuta marar iyaka ka raba wa ahhalinsu,

Ya Muzilzilun har ɗakinsu kar ka bar su,

Ka birkita su man rikirkita su Alwakilu.

 

Dukkan masu son mu ya Allah ka so su,

Ka rusa tanadi da shirin duk masu ƙinsu,

Ka ɗauke talauci ka kau da babu gun su,

Ka sanya mutane kowa ya dinga son su,

Don kakan Muhammadu Ibrahimul Kalilu.

 

Haka nan masu ƙin mu ya Rabbana ka ƙi su,

Ka jefa ƙinsu duk a zukatan masu son su,

Ka karya du lagonsu ka rusa tanadinsu,

Ka tsone idonsu ka bar su su da kansu,

Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

 

Ka bar su da ransu amma lafiyar ka ƙwace,

Su gan mu muna yi cuta kai musu tazarce,

Allah ka sa mu hanyoyin arziki mu dace,

Su suna gadon asibiti can suna a kwance,

Su ga ayyukanmu na yawo yarda Zuljalalu.

 

Muna da maƙƙiya wanda ka yarda mun ka gan su,

Akwai na ɓoye wanda kawai Rabbi kai ka san su,

Rugurguje shirinsu ka maida shi bissa kansu,

Da sun kira ka Allah don miƙa buƙatunsu,

Ka juyar da buƙatunsu ya Zuljalalu.

 

Cutar Gloria har cholera gami da tension,

Cutar hawan jini har Typhoid in addition,

Cuta ta kuturta da makanta a conclusion,

Cuta ta ƙanjamau mai hana ɗan Adam emotion,

Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

 

 

Cuta ta Asthma da Koshorko ka sa gare su,

Cutar Pneumonia da ƙarzuwa cikin jikinsu,

Ciwo na karkare da kurkunu ka sa gare su,

Cutar Malaria Feɓer sa ka kassara su.

Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

 

Cuta ta Anthraɗ Allah sa a jikkunansu,

Cuta ta Glaucoma a sa a maganansu,

Cuta ta Trachoma maƙala wa ijjiyarsu,

Ka mai da su kurame ka ɗoɗe maganansu,

Kowa sai ya amsa amin Zuljalalu.

 

Ƙara muke gare ka ya mai biyan buƙata,

Ka san abin da ke ranmu kafin mu furta,

Mai hassadarmu Allah to sa shi ya ƙasƙanta,

Mai ƙin mu ko ina yake to sa shi ya tozarta,

Don in ka bar su za su naƙasta mu Almuzillu.

 

Roƙon da nai ka amsa don martabar Habibu,

Don martabar Ma’aiki mai suna Najibu,

Don katimul wulaya da ya zamto Ƙaribu,

Don gausil agawasi ba mu kariya Mujibu,

Don martabar uba ga Fadila ya wakilu.

 

Ya mai tsare halitta mun zo ka taimake mu,

Ka ba mu kariya kar wani ɗa ya addabe mu,

Allahu kai katanga ta tsari ga magautanmu,

Masu bibiyar ɓatanci ga sana’unmu,

 

Allahu ga magauta nan za su kassara mu,

Ka ba mu kariya Allah mu da iyalanmu,

Su kassara mu sun ɓatanci ga mutuncinmu,

Sun mai da mu kamar shara a cikin garinmu.


Mun zamma sai ka ce jemagu da iyalanmu,

Mun zamma mujiya a cikin jinsin yarenmu,

Suna ta cin amanar bayinka cikin hammu,

Sun shigga innuwar al’adu addininmu,

Allahu don isarka da mu kai kaƙ ƙage mu,

Ka ba mu kariya don ƙaunar Abu Batulu.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments