Ticker

6/recent/ticker-posts

Gilashi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa: Mai gidan gilasai,

Tubalen gilasai,

Ginshiƙin gilasai,

Mai gidan gilasai.

 

Amshi

Mai gidan gilashi ba jimirin wargi yake ba,

Mai kaza a ƙugu ba jimirin as-as yake ba ‘yan uwa.

 

Kaliƙi buwayi ban yi nufin saɓa maka ba,

Rabbi ka sani ni ban yi nufin cutar wani ba,

Rabbi kaz zame mini jagora kar in yi zamba,

In isar da saƙona da sani ba da kangara ba.

 

Hannunka mai sanda na kama ba zamba ne ba,

Arashi nake jama'a ba cin fuska nake ba,

Je ka maza gyara in ka tsinci kanka wanga zamba,

Ƙarƙashin azanci don a sani don kauda zamba.

 

Shure-shure ba shi hana mutuwa ɗan’uwa ka duba,

Mai fagamniya bari-bari ba za tai fa'ida ba,

Hali na dangin dangira ba zai yi ma ba,

Tuni an gaza da daren kure ba fa'ida ba,

Arziƙi ake nema da sani ba da ɓata ba.

 

Tafiyar sahara malam ba da kare ake ba,

Shumuli na kaya ba jaki aka wa izo ba,

Kiwo na doki ba wai don a ci fa ake ba,

Daina taka sahun giwa ba san amala ne ba,

Ɗaukaka ake nema da sani ba da ja’iba ba.


Sabo da kaza ba hana yanka ta yake ba,

Mai gidan gilashi ba zai so wasan jifa ba,

Haka nan makaho ba zai so wasan jifa ba,

Magana nake da azanci kai ɗan uwa ka duba,

Nasara ake nema da sani ba da fittina ba.

 

Aikin fasaha ba fa dauki saka ba ne ba,

Baiwar hikima ba kyautar ɗan’adam ne ba,

Aiki a kan ilimi mai rinto ba zai iya ba,

Kai mai ƙwanƙwamai aljannu ba za su ma ba,

Riba ake nema da sani ba da riggima ba.

 

Rigar isgilanci ba rigar sawa ba ce ba,

Suttura ta iskanci ba kayan sawa ba ne ba,

Maza kai shaƙiyi daina tinƙaho bari duba,

Komai kake an yi shi a baya ka je ka duba,

Rahama ake nema da sani ba rashin sani ba.

 

Ina Fir'auna da Hamana ɗan’uwa ka duba,

Ina Ƙazaza Ƙaruna ko ba ka tuna ba,

Izgili ba kay yi Abujahil, Abulahabi ba,

Kusa-kusa je ka fa Ƙonbaro shege ka duba,

Lafiya muke nema da sani ba da yin ƙazab ba.

 

Tsumagiya takan hanya fyaɗe yaro da babba,

Yinwa ba ta jumurin Lahaula ka je ka duba,

Wa'azi yana kan kowa ba ware nake ba,

Ai nazari fa da taka-tsantsan duba-duba,

Buɗi ake nema da sani ba da kokawa ba.


Allah gafurun rahimun mai rahama ta duba,

Ya Sattaru Alimun mai mulki a duba,

Ya mutaƙadduran Allah na duƙa a duba,

Ina nufin saƙo gun bayinka ka sa su duba,

Yarda nake nema da sani na zo a duba.

 

Adali na sarki bai tserewa zamani ba,

Shugaba karimi bai kuɓucewa zamani ba,

Malami waliyi bai tsira a zamani ba,

Mumini ganiyyi bai tserewa ƙasƙanci ba,

Masanin fa kenan balle Kasgi Ɗanma’abba.

 

Ko wane tsuntsu kukan kinkarsu yake fa,

Saniyar gaba ita ce makwafin ‘yan baya duba,

Da hankali ake aikin neman hankali a duba,

Kunya ma'aunin ɗan sunna ba ɗan agwai ba,

Falala ake nema da mutunci babu zamba.

 

Alan Kanawa mai waƙe na a zo a duba,

Ɗan Nasarawa ne na Tudun Murtala a duba,

Ke kira da sauti a sauƙaƙe ba cakuɗa ba,

Sautina yau nazarinsa ake ba zo ka wuce ba,

Dace muke nema da sani ba da tsokana ba.

 

Mai gidan gilashi ba jumurin wargi yake ba,

Mai kaza a ƙugu ba jumurin as-as yake ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments