Ticker

6/recent/ticker-posts

Rakumi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Raƙumi raƙumi ya ɓad da sawun giwa,

Raƙumi raƙumi ya shanye ruwan kasko.

 

Amshi:

Raƙumi ya ɓad da sawun giwa ya zo zai shanye ruwan kasko,

Gaya wa kare ya bar kai sara da talla a tsangayar kuwa.

 

Allahu abin riƙon kowa,

Abin dogaro da bautawa,

Kukanmu kai muka miƙawa,

Allah mai share hawayenmu bayinka mun shiga damuwa.

 

 

 

Allahu ga wata annoba,

Ta zam a gare mu ja’iba,

Mata da ɗiyarta har baba,

Ba aiki Jalla ka yo duba,

Halin ƙa ni ka yi ba wai ba.

 

An ba ka abinci ba ruwa,

Ka san daɗi ba ya samuwa,

Domin da shi aka rayuwa,

Allah sarki mai zubar ruwa,

Ka fidda mu daga damuwa.

 

In ka ci abinci ba ruwa,

Ka san dole kai ta shaƙƙuwa,

Ƙarshe ya saka ka damuwa,

Ya sa ka gama ka galabaita,

Har ma ka zam ba ka moruwa.

 

Allah kai ka ƙirƙiro kowa,

Sannan kai ka san haƙin kowa,

Kai hanya ta ci da shan kowa,

Kai hikkima kuma taguwar gumin inda ya tsintuwa.

 

Bakin da Rabbi ya tsaga shi,

Abincin cin shi zai ba shi,

Kula lafiya suturta shi,

Ba wanda zai iya tauye shi,

Barai ya sa shi a damuwa.

 

Jama’a mu rinƙa tuna-tuni,

Wani bai canza halin wani,

Sai Rabbi yai masa izzini,

Tsaigungumi da guna-guni,

Ba ya saka mu a damuwa.

 

 

 

Mu yanzu mun yi fa dandazo,

Ba ma tsoron ƙurar hazo,

Bare fa ai yi mana gizo,

Mun tsallake tarkon gizo,

Mai son ya sa mu a damuwa.

 

Na ba da aman an ci min,

Ƙarshe zangon ƙasa anka min,

Da na aza gyara za a min,

Ashe kama karya ake min,

A gan ni a damuwa.

 

Yaudara ba halin ma’aiki ba,

Sannan ba halin sahabbai ba,

Ba tabi’ai suka gada ba,

Halayya ce ta kafiran farko masu zalunci da cutuwa.

 

Yau na ga ana ta kokawa,

Yaƙar masu hikima baiwa,

An tamke su sai ka ce bawa,

Madadin ai tasarrfin baiwar da Allah ya ba su tai yawa.

 

To rabon kwaɗo bai hawa sama,

In ya hau ma to ba zai jima,

Ba zai sakko babu tantama,

Ku dai ku bi ta a hankali in ma duniyarku ta jima.

 

Ƙasashen waje Super Power,

Malumma su aka ba power,

Sannan masu hikima baiwa,

Nan ga su su aka biznewa,

Kun ɗau gwadabe na gantsarwa.

 

Jazilatul Arab dubawa,

Latin Amurka dubawa,

Har Asian tafi dubawa,

European da Afirkawa,

Aikin fusuha suke kwarwa.

 

Mu namu muke ta buznewa,

Ba ma rabon aiki gun kowa,

Sai dai nakasa da tauyewa,

Yau gashi muna ta dambarwa,

Muna warwara da tufkawa.

 

Girman kai ba shi da magani,

Na jahilci da rashin sani,

Shi ke haifar da guna-guni,

Ciwon da ba shi da magani,

Girman kai ne na rashin sani.

 

Kai mai biɗar ka yi gundura,

Mun bar ka mun tafi ba jira,

Idan lahirarmu tai kira,

Kai ma da sannu fa za ka zo,

Ko bayan ɗari da sha tara.

 

Allah dan isa da izzarka,

Allah dan cika da girmanka,

Alla dan buwayar zatinka,

Don tsarki cika na sunanka,

Allah Al-musawwiru Allah,

Allah Al-mudabbiru Allah,

Allah Al-alimu ya Allah,

Allah Al-wahabu ya Allah,

Allah Al-jabbaru ya Allah,

Allah zahiri da baɗini,

A gunka ba su fa ɓoyuwa,

Allah kai mana maganin,

Mai sanya kanmu a damuwa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments