Ticker

6/recent/ticker-posts

10.11 Murnar Aure - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 492)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Ga gaisuwar iyaye Shehu Ɗalhatu ne da mama Khadija,

Na gurguso taya ku murnar kun yi biki na auren sunna.

 

Shimfiɗa

Nana Khadija ga ki,

Na yaba nassabarki,

Na kalli salsalarki,

Kabar tsaka na ganki,

Dama da hauni naki,

Dukka jinin saraki,

Jini na Dabo sarki,

 

Sannu uwar iyaye,

Uwar maƙera sannu,

Uwar masaƙa sannu,

Ga inuwar marayu,

Khadija sannu sannu,

Rumfa gurin marayu,

Ga inuwar Kadaura mai lumshi ga ɗiya da ma jikoki.

Na zo bikin taya ku murnar kun yi biki na auren sunna.

 

Allahu Wahidi da ake yi wa bauta a rukkuni mai tsarki,

Na zo a durƙushe a gareka Buwayayye Gwani mai tsarki,

Sarkin da ke da tsarki bai karɓar lamarin da ba shi da tsarki,

Na tsarkake niya ta zan yi yabo ka hane ni in saki baki.

 

Na gai da shugabanmu annabi wannan da an ka ba cetonmu,

Mai nasaba cikakka annabi wanda ya zamto gatanmu,

Baba gurinsu Fati kakan Alhasanaini tsatson kimu,

Allah ka ƙara yarda gun ahali na gidansa mai shabbaki.

 

Hujja ta wagga waƙe murna ce na taho in yi wa Khadija,

Na ƙara ƙarfafarta kan tahamidar Ubangiji bisa hujja,

Baiwar da yai gareki Hajja Khadija uwargida bisa hujja,

Ki ƙara gode Allah yai maki ‘ya’ya a yanzu ga jikoki.

 

Farar uwar iyaye Nana Khadija uwargida gun Shehu,

Kai haihuwa da rana Nana Khadija uwar gida gun Shehu,

Samun uwa irinki Nana Khadija abar yabo gun Shehu,

Mai asali da da'a, na da wuya koko ma in ce jan aiki.

 

Almalu walbanuna Allah kansa ya ambata Ƙur'ani,

'Ya'ya da dukiya ne kyakkyawa daga arziki insani,

Komai na duniya aka san yaya fa da dukiya yai rauni,

Ki ƙara godiyarki ga Allah wanda ya ba ki halin kirki.

 

An ce abin cikin ƙwai ya zarce ƙwai a soyuwa insani,

A yau biki ake yi ga ‘ya’ya da iyaye ga kakanni,

Ranar farin ciki ce kowa na habaran yana alhini,

Rana ta walwala ce yau aka shirya bikin ɗiya na gurinki.

 

Murna na zo taya ku na yi kiɗa na bishi da sautin taushi,

Badujala sArewa na busasu sarewuka na tashi,

Har da kiɗi na Sudan duk don nuna farin ciki mai ƙanshi,

Murnar bikin amare Hauwa da A’ishatu mu ke wa ɗauki.

 

Hauwa'u ce amaryar barista bashari da auren ƙauna,

A’ishatu amaryar Muktar Musa amintaka ga ƙauna,

Na zo bikin taya ku murnar kun yi biki na auren ƙauna,

Allah ya ƙara ƙauna, kuma kuy yi ɗiya da 'yan jikoki.

 

Saddika Aminu matar Mubaraku Muhammad sade,

Ango gurin Sadiƙa Mubarak na Muhammadu ɗan Sade,

Na zo bikin taya ku murnar kun dace da zaɓin dede,

Allah ya ƙara ƙauna kuma kuy yi ɗiya da 'yan jikoki.

 

Khadijatu sabo matar Suleman yamai Abdallah,

Suleman yami Abdallah angon Khadijatu madallah,

Na gurguso taya ku kun zaɓen da ake ta masha'allah,

Allah ya ƙara ƙauna kuma kuy yi ɗiya da 'yan jikoki.

 

Dr. Bello Bello Katagun angon Farida 'yar Shinkafi,

Farida amarya Dakta Bello haɗinga yai masu zafi,

Haɗin so da ƙauna dole ya yi wa mahassadan nan zafi,

Allah ya ƙara ƙauna kuma kuy yi ɗiya da 'yan jikoki.

 

A gaisuwar yabawa ban manta Jibirilla nawa,

Jibrin Ɗanfillo yake gaisuwar isarwa,

Fata na alkhairi da murna yana isarwa,

Allah ya ƙara ƙauna mai saiwa da dubun zumunci mai auki.

 

Farin cikin iyaye sug ga ɗiyansu a rayuwa alfarma,

Buri gurin iyaye sug ga ɗiyansu a rayuwa mai girma,

Aure taki na girma Nana Khadija ina yabo mai girma,

Allah ya ƙara yelwar aure sunnar ubangidanmu ma'aiki.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments