Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Maryama Da Aminu

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Sanadi na aure muka zarce dabba,

Sanadi na aure muka zarce aiba,

Sanadi na aure mun zarci zamba,

Sanadi na ba a yi ya ɗan Adam ba,

Sanadi na auren da ake da hubba

 

Sababi na auren ga farin ciki ne,

Sababi na auren ga zumuntaka ne,

Sababi na auren ga yare tsatso ne,

Sababi na auren ga fa martaba ne,

Sababi na auren ga fa ƙaruwa ne.

 

Godiya ga Allah masani na ɓoye

Ya Ubangijina sharen hawaye,

Masanin zukata zahiri da ɓoye

Gani gunka Allahu kar ka bar ni karye,

Karbi baitukana na yabon amare

 

Gaisuwa ga Mamman abin koyin amare,

Sanadi na aure da bikin amare

Goɗiya da ba ƙaidi wacce ba ta ƙare,

Sanadin na tsarkin tsatso gare aure,

Mui rawa mu risa domin bikin amare.

 

Yau fa ‘yan uwa na ga farin ciki suke yi

Na ga ahli dukka farin ciki suke yi,

Har abokanai na ga rawar ƙafa suke yi,

Na ga ammara har wani rangwaɗa take yi.

Sanadi na Maryama Aminu sun yi aure.

 

Dole in taho in zuba baituka na aure,

In kira abokai na Aminu duk a jere,

In kira iyaye na Aminu duk a jere,

In kira iyaye na gidansa duk a tsare,

In kira ƙawaye na amarsatu amarya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments