Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Dakta Abdullahi Da Bara’atu

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 1

Tauraruwa ta amare ƙamshi ta ko’ina ke tashi,

Marhababin lale murna mu ke da auren sunna 'yan uwa.

 

Amshi 2

Dakta Abdullahi liman mijin Bara'atu Tata,

Kun yi auren ƙauna Allah ya bar zumunci ƙauna 'yan uwa.

 

Ga amaryar barka, albarkeke 'yar albarka,

Ta yi auren barka, ta sam miji irin albarka,

Mai sanin addini, albarkekiya ba shakka,

Mudahhira mai halin, a yo yabo da san albarka.

 

Ɗiya ga bawan Allah, Ibrahimu Allah jiƙansa,

Tausayi da salama, Allahu Rabbana kabarinsa,

Jika ga bara ce uwar iyaye ba sa - in- sa,

Rabbana ka jiƙanta farar uwa masada zumuncin 'yan uwa.

 

Jikar Madaha amarsu mai halin albarka,

Jikar ɗan Umma mai tangaɗin kuɗin albarka,

Aminu dogon naira Allah ya ƙara alkintaka,

Lafiya ya daɗeka ya ƙara yalwatar kwananka ɗan uwa.

 

Ga haɗakar aure, haɗin sani a wannan aure,

Kun ga da shi dakta, fannin sani ku san ya kere,

Ita kau barista fanninta sharri'a taƙ ƙware,

Ai gidan ilimi ne gidan sani fa wannan aure 'yan uwa.

 

Jinjina gun ango, mutafanninin addini,

Massanin addini dakta a illimin zamani,

Agogo sarkin aiki ko da nasara nai ma raki,

Jinin gidan man liman Allah ya ƙara shin albarkar 'yan uwa.

 

Yar gidan sani aka auro gidan imamu bawan Allah,

Shekarau Sardauna malam a bar ka ikon Allah,

Ga sanin zamani sardauna masu yi don Allah,

Dari a barmasa kwansa, in kiya a kwana a bola 'yan uwa.

 

Barista 'yar farfesa gajiji 'yar bara mai daula.

Ga sanin addini farfesa Gaji baiwar Allah,

Masu hannun baiwa mai basuwa fa ba ya lalala.

Alan Kano mai waƙa yana ta godiya bisa daula.

 

Na ga matan manya kala-kala a wannan daula,

Amma irin Gajiji, daban take ka ce min kala,

Mai basuwa tai ƙari halinki ne kina kan daula,

Uwargida farfesa Gajiji mai hali na zumuncin 'yan uwa.

 

Ɗiya take gun baba Ni'ima ko in ce fa Na'ima,

'Yan amanar juna farfesa Gaji baba Ni'ima,

Ga ta ga Faɗimattu Hasan ga ta ga baba Jasan ce ma,

Irin gidan albarka Allah ya ƙara ƙara zumuncin 'yan uwa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments