Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi 1
An gaida gimbiyar mata Maryama jinjinar girma,
Mai illimin cikin mata ba tai gamo da hoho ba.
Amshi 2
Maryama gimbiyar mata na zo yabo na halinki,
Tauraruwar cikin mata mai kyan hali da alfarma.
Shimfiɗa
Mai assali da salsala,
Haskensa ba shi nashewa.
Mai kyan hali da kyan niya,
Aikinsa ba ya ɓacewa.
Mai kyan gani da annuri,
Kallonsa ba a ƙosawa,
Mai walwala halin kyauta,
Ƙaunarsa ba a gogewa.
Tauraruwa adon mata,
Ga baituka ki amasawa.
Zan bayya naki bil haƙƙi,
Kan illimi adon kowa.
Mai illimin cikin mata,
Ba tai gamo da hoho ba.
Allah Ubangijin kowa nai durƙuso salon bauta,
Duk sanda zan yi waƙena sai na saka ka don bauta,
In ma yabo na cancanta don kai kaɗai nake bauta.
Domin ka kare harshena ba zai gamo da shirka ba.
Ga gaisuwa ta ban girma gun annabi abin ƙauna,
Mai tabbari abin ƙauna mai darraja uban Nana,
Al'arabiyu Abdullahi ɗan Abdallah da Amina,
Abin riƙo da ƙaunata kun san ba za na taɓe ba.
Zan yo yabon uwar ɗaki tauraruwar cikin mata,
Halinta tausayi kyauta mai illimin da ba wauta,
Maryama kuma alkyabbar mata uwar gidan mata,
In ta fito cikin mata ba za su ƙara haske ba.
Komai na ke faɗi ga shi a aikace abin duba,
Ba shaci rattaba zan ba hujja a aikace duba,
Sashe na illimin Mairo zan zo da shi ku dudduba,
Sashe na illimin hauni har dama ba bari zan ba.
Idan na ce fa Sheckh Khalid Aliyu ba zuwo ne ba,
Khalid Jama'atul Nasarul Islamu ba baƙo ne ba,
Shumagaban Jama'atu Islamu ban yi runto ba,
To ɗalibarsa Maryam ba don yabo nake yi ba.
Dukkan jihar Platou kaf ban ɗauke dukka gefe ba,
Ban san wata makaranta da tai ya su a ilmi ba,
Ban san wata makaranta da tai ya su a fanni ba,
Kun san makarantar Al-man ba sai nai maku bita.
A illimi na Maryama na batu da baitina,
Ta bar garin Platou ne ta zo gari na zaunina,
Sai tas shige a Shiekh Jafar domin na ƙur'ana,
Kun dai ji ita sheick ba ai mata sako ba.
Ta dai yi babbaƙu Maryam tai farfaru da an duba,
Ta san lugga ta san nahawu ta san furu'a ba wai ba,
Ta san tajwidin Ƙur'a ta san hadisi ba wai ba,
Ga tambari na Maryama mai illimi ba zai wai!! ba.
Na zo ga illimin boko ba tai ƙasa a gwuiwa ba,
A uniɓasity of Jos tai diplpma ba wai ba,
A ɓangaren theatre art tai diploma ba ƙi ba,
Tai degree a Turanci a unibasiti babba.
Yanzu tana haƙon masters Maryama ba da rinto ba,
Mai mallaki na Maryama barka nake yi ma babba,
Dukkan miji na Maryama dace yayo rabo babba,
Don laddabi da tarbiyya ba zan yi maka ƙarya ba.
Maryama mai halin kirki mai haƙƙuri abar duba,
Maryama mai ibada ce kira ta abida babba,
Uwa uba na Maryama na Mairo ba abar ƙi ba,
Suna ta sanya albarka kan Mairo mai halin duba.
Major janar na Maryama ga albishir inai gunka,
Ai za ka sami Maryama mai laddabi a ɗakinka
Ai za ka sami Maryama mai tarbiyar iyalinka,
Aurenku kai da Maryama ba za ku rinƙi hoho ba.
Giwar gurinta Maryama Laila ina yabo gunki,
Na tsara baituka gunki na fid da sunanki,
Giwa ta gimbiya Maryam Laila ki amsa sunanki.
Baitin Aminu ALA ne ke kambama ku ba wai ba.
Sauran Jamal majidaɗi na Umma mai halin girma,
Jamal jinin sarakoki ga gaisuwarka ɗan Umma,
Ga jinjina da bangirma Allah ya ƙara alfarma,
Maryama sai wata rana ALA ba za ya ƙosa ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.