Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
Girman ALA yana aure ranar auren masoya,
Alalo-alalo masoya dangin juna sai a taru.
Shimfiɗa
Ranar auren zumunta,
Ranar raya zumunta,
Ranar rainon zukata,
Ranar lele da bita,
Ranar nan babu mita,
Ranar taronmu kwata,
Ranar aure na mata,
Girma ya aure mata-
Fatan alkhairin abota.
Dokar Allah buwayi aure sunnar annabin nan,
Zancen Allah buwayi aure hanyar annabin nan,
Hanyar kare mutumi aure hanyar taruwar nan,
Girman ALA a wannan rana babu kamarka ɗin nan.
Allah tsira aminci ƙara dubun yardarka ɗin nan,
Allah darajar Fadhila har da Wasila taka ɗin nan,
Ka daɗa su ga annabin nan wanda ya ke ƙaunarka ɗin nan,
Mahamidu farin masoyi mai igiyar cetonmu ɗin nan.
Fatan khairi na zo yi domin soyayyar masoyi,
Ranar auren masoyi wannan rana babu shayi,
Komai aka nemi in yi zan gaba gaɗi ba bulayi,
Don mai ɓoyon kuskure na babu kama da farin masoyi.
Sanyi rani muna nan ba mu rabo da farin masoyi,
Bazara yananin lumana marka ba mu rabo masoyi,
Duka inda na sanya sawuna na ɗaga zai sa masoyi,
Daɗi ɗaci muna nan ba mu rabo da farin masoyi.
Ranar shanya ake yi zaki marmaza zo da gari,
Hantsin shanya ake yi Hannatu yaki taho da gari,
Ga solbator yana nan ga Maryam A. S. A garri,
Duba a hagun da dama Buhari Mansur zo da jari.
Nasara a gurin masoyi ai ya zamo zarci shayi,
Galaba agurin matashi ai ya zamo ya bar bulayi,
Falala da daɗin muƙami yau ka zamo ba ƙa-ni-ka-yi,
Nasarar dukkan masoyi yau ya zamo ya sam masoyi.
Jiya ne aka sanya ɗan ba,
Yau kuma har an kai ga ƙauna,
Jiya alƙawari na ƙauna,
Yau kuma sai a riƙe amana,
Jiya anka dashe na ƙauna,
Yau kuma ranar sada ƙauna,
Jiya ne aka tsai da rana,
Yau kuma har an iske rana,
Jiya anka zubin adashi,
Yau kuma ranar kwashe dashi,
Ai jiya ƙaunar nan ka tashi,
Yau kuma ayyururi da ƙamshi,
Yau ranar auren matashi,
Gobe ka zamma uban matashi,
Inda ka je ƙamshi ka tashi,
Masu hamayya na ta haushi,
Rojan ALA ya na nan,
Aka ce Jallaba na nan,
Rukunin dangi na juna.
Cikinmu Sa'ada na nan,
Rukunin dangi na juna.
Ummi a Ummarun nan,
Rukunin dangi na juna.
Sa'id Singa yana nan,
Rukunin dangi na juna.
Sadam Anchau yana nan,
Sadam zariyya na nan.
Kabur Burji yana nan,
Yusuffu na dabo nan.
Wawan ALA yana nan,
Limamin gawa yana nan.
Sultana Amir yana nan,
Auwal Kasim ya na nan.
Mai ratata yana nan,
Masanawa Hamisun nan,
Ishaƙ Zaria na nan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.