Ticker

6/recent/ticker-posts

Bikin Fadeela

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

A yau gidan Sardauna za ni da baituka a biki na Fadeela,

Gimbiyar Abdallah Halliru ce Fadeela ɗiyar Ibrahim.

 

Shimfiɗa

Ayyururi ga amarya,

Acan-acan da amarya,

Asin-asin da amarya,

Gwaɗas-gwaɗas! da amarya,

Charan-chaɗas! da amarya,

Tsatsaf-tsatsaf! da amarya,

Sha kurruminki amarya zaɓin kanki ne,

Auren soyayya.

 

Duk inda an ka bi ƙamshi,

Sarewuka na tashi,

Ga dumdufa na tashi,

Kiɗan bishi ga taushi,

Ado ya armasa ƙamshi,

Bikin ɗiyan Sardauna masu abin yabo da gwadin soyayya.

 

Ubangiji masarauci mai kyauta yaba ka ya koma ya ƙara,

Idan ya ba ka ka ce alhamdu sannadi na gareka ya ƙara,

Wannan da shi ke amsa kiranyen mai tsumi da na masu dabara,

Muna yabonka da bauta taka da arzikin danƙon soyayya.

 

Allah ka ƙara salati gun Mahamudu mai horo a bi Allah,

Nurul huda mahabubi annabi mai izo a bi hanyar Allah,

Da alihi da sahabbai masu biyar ɗafa a bi hanyar Allah,

Muna riƙo da biyarsu har ƙaunarsu mai nason soyayya.

 

Sunnar ma'aikin Allah aure yau muke waƙar soyaya,

Sunnar ma'aikan Allah aure annabawa na soyayya,

Mu ƙanƙame igiyarsa mu yi dabaibayi da riƙon soyayya,

Da fallala fa a aure tun banlantana a yi kan soyayya.

 

Biki da an saka rana an ƙare bikin ya zam tarihi,

A kwana kwanci da tashi ga gangar jiki mai ɗaukar ruhi,

A yanzu murnar aure gobe kuwa biki ya zam tarihi,

Mu kama murnar suna aure an ci riba kan soyayya.

 

Riƙe mijinki amarya aure dukkaninsa abin haƙuri ne,

Zaman gidanki amarya ya fi zaman gidan duka ko wane ne,

Haƙin uba tarbiyya sauran ayyukan fa haƙin ango ne,

Riƙe masoyin ƙauna ku yi zaman ƙalau kuma ga soyayya.

 

Auren gidan mulki ne malam Ibrahim tsohon gwamna,

Sardauna ka cira tuta ka riƙe shugabanci riƙo na amana,

Mutan Kano sun gode sun yaba martaba da riƙo na amana,

Na zo ina taya murnar aure na Fadeela ɗiyar tarbiyya.

 

Ga gaisuwa ga Amina sannu abar yabo da riƙo na amana,

Farar uwa ga amarya Hajja Amina mata gun Sardauna,

Ina taya ki da murna don aure Fadeela ɗiyar Sardauna,

Allah ya armasa auren nan da akay yi kan turbar soyayya.

 

Albishirinki Amina zango ya taho na halin tarbiyya,

Halin uba da uwa ne zai naso gurin ta Fadeela amarya,

Don illimi tarbiyya shike sa amarya tay yi biyayya,

Da izinin Lillahi Nana Fadeela babu ta sa ku a kunya.

 

Ga gaisuwa gun mama Zainabu Shekarau Sardauna gwamna,

A gaisuwa ta iyaye Zainabu ba ni manta yabo fa da ƙauna,

Ga jinjinarki da hannu babu nuƙu-nuƙu kuma babu khiyana,

Allah ya ɗaukaka auren ‘yarku Fadeela auren kan soyayya.

 

Ga gaisuwa ga Halima matar Shekarau mashahurin ƙauna,

Yabo nake fa da waƙe don albarkacin auren ‘yar gwamna,

Fadeela ta tafi aure sunnar Musɗafa jikan adanana,

Yau addu'arku take so mai saka nuttsuwa a cikin tarbiyya.

 

 

 

Ga jinjina ga Fulanin Sardaunan Kano mai kwana sallah,

Uwargida gun ALA farfesa da ke komai don Allah,

Da illimi da kuɗi dai kin gaje su Faɗima baiwar Allah.

Farfesa Gaji Tata mai Sardauna masu dubun soyayya.

 

Allah ya ƙaro yalwa masu abin ake wa yabo don Allah,

Kin gaji ungo da karɓi ‘yar babban gida Gajiji ta Allah,

Idan batun asali ne ɗan babban gidan da ake da adala,

Halinka ko aikinka shike bayyana ka sahun tarbiyya.

 

Aminu Alan waƙa ke maku baituka na zuɓin tarbiyya,

A sanadin Algaji farfesar gidan zaɓin alƙarya,

Ta ce taho ka ji ALA waƙa za ka yi wa ɗiyar tarbiyya,

Fadila malam Iro Sardaunan Kano gatan tarbiya.

 

Farin uba ga amarya malam Ɗahiru Shekarau sambarka

Cikinsa wannan aure nai maku addu’a da yabon sambarka,

Fadeela ta tafi aure murna ce ta sa ni nake gaishe ka,

A rukkuni na iyaye malam Ɗahiru ga yabon tarbiya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments