Ticker

6/recent/ticker-posts

Ayyuriri Amarya Ango

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Ayyuriri amarya ango kun ji guɗa irin ta amare,

Marhaba marhaban lalayyo kun ji baiti irin na amare.

 

Aure a kai yi tafarkin ƙauna,

Mai isar wa masoyan ƙauna.

Aure na A’isha da Aliyu,

Kun yi dace cikin soyayya.

 

Warhaka an riga an kamu, ga amarya ado da turare,

Tuni an riga an ƙare, an gamai wa amarya jere,

'Yan uwa gami ƙawaye, ko’ina ka gano su a jere,

Acan-acan da ankon aure, sai fa ƙamshi irin na turare,

Waɗansu sun ado da ashobe, kansu ga gwagwaro fa a ɗaure,

Gwaɗas-gwaɗas cikin annuri, ga amarya da ango jere.

Ana yinin biki na amarya, an jima za a kai ta a jere,

Ranar farin ciki ga amare ba kamar ango da amarya.

 

Mai juya lammari Alhayyu kai na sanya da zan farawa,

Dukkan abin da na nufi zan yi sai da kai farkon farawa,

In nai hakan yana albarka sai abin ya zamo mai yalwa,

Na ɗau abin rubutun wake yau fa sunna nake waƙewa.

 

Sunnar abin yabo gun kowa Al-aminu abin dubawa,

Mai gargaɗi gami da bushara cikamakon abin aikowa,

Ya samu ne ta sunnar aure shi abin kwaikwayon dubawa,

Allah ka ba mu ladan koyin annabinka abin dubawa.

 

Aliyu A’isha kun dace matsayin ango da amarya,

Aliyu sahibin soyayyar A’ishi ango da amarya,

Na ɗan matso taya ku da murnar rayuwar ango da amarya,

In zam mujaddadi a gareku kan matakin zubin tarbiyya.

 

 

 

Ga gargaɗi ga sunnar aure gun amarya da ango aiwa,

Aure fa a riƙe shi ibada ginshiƙi ne na ai dacewa,

Nikahu sunnati inji manzo mai riƙonsa yana dacewa,

Mai banzatar da sunnar aure ba shi babu abin dubawa.

 

Aure fa jumlatan fa a sunna matsayinsa da an dubawa,

Amma hakin cikinsa farilla mui nazar da karatu nawa,

Aiki na ci da sha a farilla suke ba makawar bauɗewa,

Haƙƙin miji da mata tilas sui riƙo rukuni bautawa.

 

Asasi ko na ce fandesho na zama na lumanar aure,

Farko a tabbatar soyayya na gaba babu dole a aure,

Sannan mu san haki kan aure rukunin ango da amare,

Mu zam kiyaye haƙƙin juna babu hali na 'yan tere.

 

Mu ɗauki haƙƙuri rigarmu ɓangaren ango da amare,

Sannan zama zaman adalci za mu yi sai fa an daddaure,

Tsafta tana cikon addini armashin ango da amare,

Allah ya ƙara danƙon ƙauna ɓangare ango da amare.

 

Allah ya kai ƙazantar ɗaki shigifar ango da amare,

A yanzu baituka na amare gobe ka ji ana tere,

An sami ƙaruwar jariri arzikin ango da amare,

An taka kaddami na iyaye, an baro rayuwa ta amare.

 

Aliyu A’isha kun dace matsayin ango da amarya,

Aliyu sahibin soyayyar A’ishi ango da amarya,

Na ɗan matso taya ku da murnar rayuwar ango da amarya,

In zam mijaddadi a gareku kan matakin zubin tarbiyya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments