Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
Tambarin na aure ne dundufar amare ce.
Alhaji Surajo Abubakar ango na Farida.
Shimfiɗa
Jinjinar ta aure ce,
Tamburan amare ne.
Sallamar amarya ce,
Baitukan na aure ne.
Sarewar amare ce,
Kakakin amare ne.
Gaisuwar amaryace
Algaitar ga aure ne.
Waƙar yau fara fat ce,
Nishaɗin amare ne.
Ko wannensu ya dace,
Sai ƙamshi amare ne.
Godiya muke a gurin Allah da baza ta ƙirgu ba,
Da ya ba mu abokanan burmi ba ‘yan ta'adda ba,
Da ya ba mu abokanan hulɗa ba masu cuta ba,
Da ya ba mu abokanan zamni ba wai da gaba ba,
Murmushinka lada ne,
Ci da shanta lada ne,
Tarbiyarta lada ne,
Sutturarta lada ne,
Gaisuwarku lada ne,
Ɗawainiyarta lada ne-
Kai fushi nata da hucewa ƙarshe ibada ne bayin Allah.
Gaisuwar masoyina Annabi baban Nana Faɗimma,
Shugaba na al'umma Annabi gun kowa abin nema,
Kyan siffa da kyan hali Annabi ba shi kini a al'umma,
Kwaikwayonsa ne aure Annabi don tsare martabar umma.
Wanda yarriƙe aure,
Ba batu na terere,
Tsarakinsa ya kere,
Gwargwadon riƙon aure,
Martaba tana aure,
Darraja tana aure,
Aka ce malu banuna duk suna ƙarƙashin aure bayin Allah.
Ai biki uku cif cif ne aka yi wa macce a rayuwa,
Ga bikin zuwa nan dai in aka haihu an sami ƙaruwa,
Sai bikin tsaka tsakki don aure na cikar kamaluwa,
Na ukun kurun kus ne sanda ake rakiyarki kushewa.
Tanadin bikin ƙarshe,
Na mabi bikin ƙarshe,
Ga kira a tattaushe,
Jarrabawa kin lashe,
In ki kay yi harsashe,
A gaɓa gaɓar tashe-
Ki bi Allah da ma'aikinsa a ƙarƙashin aure baiwar Allah.
Ga yabo gurin Malam Alhaji Surajo mai halin girma,
Allah ƙara buɗa ma Rabbu ya yalwata masu koyi ma,
Domin mu dafa ma mut tsare haƙƙoƙi na mai nema,
Masu iggiya daidai suz zama masu biyu da ukku ma,
Domin martabar aure,
Domin fallalar aure,
Don ribar cikin aure,
Don gatan cikin aure
Don daɗin da ke aure-
Don ninkin ladan da kan yiwa masu riƙon aure domin sunna.
Kun zamo madubin duban alumma na ci gabba,
Kun zamo fitilu da ke haske finnasi ba wai ba,
Kun zamo abin sha'awar a gani a ji ba fahar ne ba.
Kar ku fara yin zamba
Kar ku koya yin zamba
Ba batu na tsoro ba
Ku ake duba da alkhairi ba masu sharri ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.