Ticker

6/recent/ticker-posts

Wacce Addu'a Zan Yi Don Kar In Yi Barci Bayan Asubahi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, ina kwana? Tambayata ita ce mutum idan ya tashi da safe ba zai iya addu'a ba akwai wata addu'a dan kar bacci ya dauke shi, kuma shin idan yayi bacci ya yi laifi? Allah ya taimaka Ameen.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, Ba wata addu'a a Sunnah da ake karantawa don ta hana mutum yin barci bayan sallar Asubahi, idan kuma akwai to ni ban san ta ba, babu laifin komai ga wanda ya yi nufin yin azkar sai barci ya ɗauke shi kafin ya kai ga wannan azkar ɗin, Allah shi ke cire ran mutane a lokacin da barci ya ɗauke su, saboda haka ba ki da laifin komai don kin yi nufin yin azkar ɗin Safiya sai barci ya ɗauke ki, ko Bahaushe ma ya ce "barci ɓarawo ne", duk lokacin da kika farka sai ki yi azkar ɗin.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

[11:42 PM, 5/6/2023] Malam Khamis Yusuf Tambayoyi 2: BARCI YA ƊAUKE NI KAFIN SALLAR ISHA'I HAR LOKACINTA YA WUCE, YA ZAN RAMA TA?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam Allah ya saka ma da alkhairi, tambayata ita ce wani lokacin in na zauna sai bacci ya dauke ni kuma ban yi sallar Isha ba, shin meye ne matsayina, shin zan raba sallah ne ko yaya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, wanda barci ya kwashe shi bai sami damar yin sallar Isha'i ba har sai da lokacinta ya wuce, to da zarar ya farka daga barci zai rama wannan sallar ce ta Ishá'i, sannan sai ya yi sallar Asubahi, idan kuma ya ga zai rasa jam'i na sallar Asubahi idan ya tsaya rama ta, ko kuma lokacinta zai fita, to sai ya yi sallar Asubahin, sannan sai ya rama sallar Ishá'i ɗin daga baya.

Idan kuma mace ce da take sallah a gidanta, to ita ma sai ta rama sallar Ishá'i ɗin, daga nan kuma sai ta yi Asubahi, idan kuma ta ga lokacin asubahi zai fita idan ta tsaya rama Ishá'i ɗin, to ita ma za ta fara yin sallar Asubahin ne, daga bisani sai ta rama sallar Ishá'i ɗin.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments