𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, don Allah Mlm ina da tambaya, Mlm na kasance mai son aikin alkairi kuma idan na tashi aikatawa sai na dinga ji zuciyata na raya min don riya nake yi, ko sadaka idan na zo zan yi in dai da mutane a gun sai na fasa saboda zan rika jin ai za su ce ina yi dan a fada, ni kuma sai na fasa, wallahi Mlm ko karatun Alqur'an nake yi wasu suka shigo gidanmu sai na ji muryata ta sauya, in na ji haka sai na daina, saboda ba na son na dinga aiki dan wanin Allah, kuma duk lokacin da zan yi aikin alkairi ln dai da mutum a gurin sai na fasa don Allah Mlm idan da akwai addu'ar da zan dinga yi nadaina a taimaka mini da ita, ban son na dinga aiki dan riya, na gode Allah ya saka da alkairi ya sa mu dinga aiki da abun da za mu ji Mu amfana.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu, Tabbas Allah ba ya karɓar
duk wani aiki da aka yi shi ba tsarkin ninya (ikhlasi), dole ne kowani musulmi
ya yi iya qoqarinsa wajen ganin ya riqa yin duk wani aiki don Allah, ba don
mutane su gani su yaba masa ba, matuqar ba a sami wannan a cikin ayyukan bawa
ba, to waɗannan
ayyukan Allah ba zai karɓe
su ba, kamar yadda ayoyi da hadisai da dama suka yi gargaɗi, daga ciki, Allah S.W.T a
hadisul Qudusiy yana cewa: "Ni na wadatu daga mushirikai game da shirka,
duk wanda ya aikata kowane irin aiki ya haɗa
ni da wani na a cikinsa, to na bar shi da shirkarsa". Sahihu Muslim 2985 .
Wannan na
nufin duk wanda ya aikata wani aikin Allah don mutane su gani su yaba masa, to
Allah ya bar shi da wannan aikin da ya yi, ba zai karɓa masa ba. A wani hadisin da Abuhurairata ya
ruwaito, Annabi ﷺ ya
ce: "Duk wanda ya jiyar da aiki Allah zai jiyar masa da shi, haka duk
wanda ya nunar Allah zai nunar masa da shi".
Bukhariy 6499,
Muslim 2986.
Wannan na
nufin duk wanda ya yi wani aikin lada don mutane su ji su yaba masa Allah zai
sa mutane su ji aikin, haka nan wanda ya yi aiki don mutane su gani su ce ya
iya, to Allah zai nunawa mutane su gani su yaba masa, amma ba shi da sakamako
na lada a lahira, har ma zai sami zunubi na haɗa
Allah da wani a cikin aikinsa, saboda mai yin riya yana yi ne don mutane su
yaba masa, sannan ta wani ɓangaren
kuma yana son Allah ya ba shi lada, don haka wannan shirka ce qarama in ji wasu
malaman. Allah ya tsare mu da yin riya a cikin dukkan ayyukanmu.
Game da addu'a
da kike nema wanda za ki riqa yi don Allah ya raba ki da riya, to ni a gaskiya
ban san wata addu'a keɓantacciya
da ake yi don Allah ya raba mutum da riya ba, amma dai qofar addu'a a buɗe take, matuqar ba ta saɓa wa shari'a ba, wato kenan
za ki iya yin addu'a a kan Allah ya raba ki da aikata riya, ki nace a kan hakan
a duk lokacin da kika yi sujjada, kuma ki riqa tashi cikin dare kina roqon
Allah ya raba ki da riya, in Allah ya so Allah zai taimaka maki a kan hakan.
Kuma za ki iya haɗawa
da wannan addu'ar ta Manzon Allah ﷺ:
يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ
ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ.
Shahru bin
Haushab ya tambayi Ummu Salamata cewa
wace addu'a ce Manzon Allah ﷺ
ya fi yawan yi idan yana wurinki? Sai ta ce: "Addu'ar da ya fi yi ita ce:
يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ
ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ.
Sai ta ci gaba da cewa: "Na tambayi
Manzon Allah ﷺ cewa;
mene ya sa mafi yawan addu'arka ita ce wannan? Sai ya ce: "Lallai babu
wani ɗan'adam face
zuciyarsa tana tsakanin yatsu biyu daga cikin yatsun Allah"".
Sunanut Tirmizhiy
3522.
Allah ne mafi
sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.✍🏻
Ga Masu
Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.