Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halasta Mutum Ya Yi Burin Mutuwa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Allah ya kara wa malam basira, ya halasta mutum ya ji yana so ya mutu ko ya ringa addu'a ya mutu ya huta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, 'yar uwa bai halasta mutum ya ji yana son ya mutu ya huta ba, saboda hadisi ya tabbata daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda cewa:

Manzon Allah ya ce: "Kada ɗayanku ya yi burin mutuwa, kuma kada ya roƙi mutuwa ɗin tun gabanin ta zo masa, domin idan ɗayanku ya mutu ayyukansa sun yanke, shi kuwa mumini rayuwarsa ba ta ƙara masa komai sai alheri." Muslim (2682).

A riwayar Albukhariy kuwa Manzon Allah cewa ya yi: "Kada ɗayanku ya yi burin mutuwa, ko dai ya kasance mai kyakkyawan aiki ne wata ƙila ya ƙara, ko kuma mai mummunan aiki ne wata ƙila ya tuba". Albukhariy (7235).

Wannan sai ya nuna cewa bai halasta mutum ya yi burin mutuwa ba, kuma bai halasta a roƙi Allah ya kawo mutuwa ba.

Harwayau, hadisi ya tabbata daga Sahabin Manzon Allah Anas ɗan Malik cewa: Annabi ya ce: "Lallai kada ɗayanku ya yi burin mutuwa saboda wani abin cutarwa da ya same shi, idan ya zama dole sai ya aikata hakan, to sai ya ce: Ya Allah ka rayar da ni matuƙar rayuwa ce ta kasance mafi alheri a gare ni, ka karɓi raina idan ta kasance mutuwa ce mafi alheri a gare ni". Albukhariy (5671), Muslim (2680).

Lura da dalilan da suka gabata, bai halasta mutum ya yi burin mutuwa ba, ko ya roƙi Allah mutawa ba, inda ya halasta mutum ya yi burin mutuwa shi ne idan mutum ya ji tsoron fitinuwa a cikin addininsa, to a nan mutuwa nesa da fitunuwa a addini ya fi alheri. Haka nan ya halasta mutum ya yi burin samun mutuwar shahada, akwai hadisai da malamai suka fahimci hakan daga gare su.

Allah Ta'ála ne mafi sanin dai-dai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments