𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Mallam musulunci ya haramta asadu da mace tana cikin al'ada. tambaya anan shin ya halatta mace ta yi wasa da mijinta har maniyyi ya futa? Cikin al'ada Ko kuma shi zaice mata ta yi wasa da gabansa har maniyyi yafuta, meye hukuncin yin Hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Dukkan Maluman
Musulunci suna ganin halaccin Mutum ya kwanta shimfida guda da Matarsa alokacin
da take cikin jinin haila, har ma ya halatta su aikata komai irin nasu na
Ma'aurata amma banda Jima'i.
Suna kafa
hujjah ne da hadisin Sayyiduna Anas bn Malik (ra) wanda yake cewa :
"Yahudawa sun kasance idan Mace tana haila ba su cin abinci tare da ita,
kuma ba su zaunawa waje guda da ita. Da Sahabban Manzon Allah ﷺ suka tambayeshi game da
haka sai Allah Mai girma da ɗaukaka
ya saukar da ayar nan ta cikin Suratul Baƙarah :
"KUMA
SUNA TAMBAYARKA GAME DA HAILA, KACE MUSU SHI ƘAZANTA NE. KU NISANCI MATA AYA YIN DA
SUKE CIKIN HAILA, KAR KU KUSANCESU (WATO KAR KUYI JIMA'I DASU) HAR SAI SUN YI
TSARKI (WATO BAYAN DAUKEWAR JININSU KENAN).
Sai Manzon
Allah ﷺ ya ce ma
Sahabbansa "KU AIKATA KOMAI DASU IN BANDA JIMA'I".
(Imamu Ahmad da
Muslim ne suka ruwaitoshi).
Masrouƙ bn
Al-Ajda' ya ce "Na tambayi Nana A'ishah mene ne ya halatta ga Namiji
alokacin da Matarsa take cikin haila? Sai ta ce "KOMAI DA KOMAI, IN BANDA
FARJI". (Wato zai iya Mu'amala da dukkan Jikinta amma banda al'aurarta).
(Imamul
Bukhariy ne ya ruwaitoshi a cikin Tareekh).
Wato za ta
sanya Wani zani ta yi Ƙunzugu dashi, ko kuma ta sanya Gajeren wanda wanda zai rufe
tun daga Ƙasan
cibiyarta har zuwa gwiwarta, Sannan ta kwanta Shimfida guda da Mijinta.
Akwai Hadithi
daga Nana Maimunatu bintul Harith (ra) ta ce "Manzon Allah ﷺ ya kasance idan yana nufin
yin Mubashara da wata Mata daga cikin Matansa wacce take cikin Haila, yakan
umurceta da ta yi Ƙunzugu"
(Bukhariy da
Muslim ne suka ruwaitoshi).
Don Ƙarin bayani
aduba wadannan hadithan :
Sahihul
Bukhariy hadisi na 300-303. Sahihu Muslim hadisi na 293-294. Abu Dawud hadisi
na 211, 269.
Sannan aduba
RISALATUL ƘAIRAWANIY
babin da ke magana a kan haila. Sai kuma AL-FIƘHUL WADHIHU juzu'i na 1, shafi na
104-105.
Sannan dangane
da hukuncin fidda maniyyi ba tare da Jima'i ba, Malamai sun ce ya halatta Mace
ta shafi al'aurar Mijinta har ya fitar da Maniyyi, ko kuma shi ya shafi
al'aurarta har ta biya bukatarta. Amma idan mutum ya shafi tasa al'aurar da
kansa har Maniyyi ya fita, to Wannan shi ne Istimna'i wanda mafiya yawan
Maluman Musulunci suka ce Haramun ne.
Amma idan mace
tana cikin haila bai halatta mijinta ya shafi Farjinta ba, sai dai sauran
sassan jikinta. (Kamar yadda aka fada cikin hadisan da ke sama).
WALLAHU
A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.