𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam, barka da warhaka da fatan an tashi lafiya, Allah ya qara lfy da nisan kwana, amin. Malam tambayata ita ce game da wani labari da na ji cewa wata mata ta mutu gawarta tana kamshi sai aka ce tana karanta suratul mulk ne idan za ta yi bacci. Ina son qarin bayani malam game da wannan magana.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salám. 'yar uwa a iya abin da na sani ban taɓa
jin ko da wannan labari ba daga wurin malamai, kuma ban taɓa ganinsa a karatu ba,
sannan kuma bai yi kama da ingantaccen labari ba. Abin da kawai na san ya
tabbata daga Manzon Allah ﷺ
shi ne abin da Attirmizhiy da Annasá'iy suka ruwaito cewa:
i. Haqiqa
Annabi ﷺ ya ce:
"Lallai akwai wata sura a cikin Alqur'ani mai ayoyi talatin, ta ceto wani
mutum har sai da aka gafarta masa zunubansa ita ce suratu تبارك الذي بيده الملك"
Attirmizhiy (2891).
ii. Daga Jabir
Allah ya qara masa yarda cewa: Lallai Manzon Allah ﷺ ya kasance ba ya yin barci har sai ya karanta
الم تنزيل (suratus Sajada), da تبارك الذي
بيده الملك (suratul Mulk).
Attirmizhiy (2892).
iii. Daga Ibn
Mas'ud Allah ya qara masa yarda ya ce: "Duk wanda ya karanta (تبارك الذي بيده الملك)
a kowane dare, to Allah zai hana masa azabar qabari da ita, mun kasance a
zamanin Manzon Allah ﷺ
muna kiranta da suna ALMÀNI'A (mai hana azaba), lallai tana cikin littafin
Allah, sura ce da wanda duk ya karanta ta a kowane dare, haqiqa ya yawaita lada, kuma ya sami dacewa". Assunanul
Kubra Linnasá'iy (10479).
Don haka, 'yar
uwa wannan shi ne abin da na san ya tabbata daga Manzon Allah ﷺ da Sahabbansa a game da
karanta suratul Mulk a kowane dare. Wancan labarin kuwa na cewa wata mata
gawarta tana qamshi saboda karanta wannan sura da take yi ban san inda masu wannan
labarin suka qwaqulota ba.
Allah Ta'ála
ne mafi sanin dai-dai.
Jamilu Ibrahim,
Zaria.
Ga Masu
Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.