Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Idan Mace Ta Tuba Daga Zina, Allah Zai Yafe Mata?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam tambayata anan ita ce Malam Allah yana yafe laifin zina? ko kuwa sai anyi wa mutum bulala ɗari? Ko kuma idan yabari shikenan Allah yana yafewa tunda mutum baiyi aure ba, kuma babu wanda yasani sai Allah? Kuma yanzu wallahi na yi nadama malam yaya zanyi dan Allah?? Kuma dan Allah malam mutum zai iya aurar wanda bai taɓa yin zina ba? kuma idan mukayi aure alhakinsa yana kaina ko kuwa yana kan wancan mutumin da ya yaudareni? kuma idan mutum ya Tuba Allah zai yafe mai kuma yakoma kamar beyiba? malam ina son inji.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Allah Madaukakin Sarki ya faɗa a cikin Alƙur'ani mai girma cewa: "KA GAYA (MUSU) "YAKU BAYINA WAƊANDA SUKA AIKATA ƁARNA a kan KANSU!! KADA KU FIDDA TSAMMANI DAGA SAMUN RAHAMAR ALALH, HAKIKA ALLAH YANA YAFEWA DUKKAN ZUNUBAI. SHI SHI NE MAI GAFARA, MAI JIN ƘAI".

Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) ya ce: Dalilin saukar wannan ayar shi ne akwai wasu mutane ne waɗanda suka aikata kisan kai da yawa, kuma sukayi zinace-zinace da yawa, sai suka zo wajen Manzon Allah suka tambayeshi "Abin da kake kiran mutane zuwa gareshi (wato Musulunci) abu ne mai kyawu. To amma muna so ka bamu labari shin akwai wani abin da zai kankare mana zunuban da muka aikata ne?"

To sai Allah ya saukar da ayar nan ta cikin suratul Furƙan da kuma wannan ayar wacce na kawota asama.

(Aduba Sahihu Muslim hadisi na 122, da sunanul Kubra ta Imamun Nisa'iy hadisi na 11,449).

Hakanan Imamu Ahmad bn Hanbal a cikin Musnadinsa ya kawo cewar bayan saukar wannan ayar sai Annabi ya ce "Wannan ayar tafi mun duniya da abun cikinta".

Sai wani Sahabi ya ce "Ya Rasulallahi har wanda ya yi shirka ma? Sai Annabi ya ce "KU SAURARA! HAR WANDA ya yi SHIRKA (SHIMA IDAN YA TUBA ALLAH ZAI YAFE MASA)".

Hakanan akwai hadisi a cikin Musnadin Imamu Ahmad wanda aka ruwaito ta hanyar Sayyiduna Amru bn 'Abisah (rta) ya ce "Wani mutum tsoho tukuf yazo wajen Manzon Allah yana dogarawa da sanda, ya ce "Ya Rasulallahi ina da wasu manyan laifukan da na aikata irin na yaudara da fajirci. Shin Allah zai yafe mun kuwa?".

Sai Manzon Allah ya tambayeshi "Shin ka shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?"

Sai mutumin ya ce "Kwarai kuwa. Kuma na shaida cewa lallai kai Manzon Allah ne! ".

Sai Manzon Allah ya ce masa "Ai an riga an yafe maka laifukanka".

(Musnadu Ahmad 4/385).

Abu mafi muhimmanci dai ga duk wanda Allah ya jarrabeshi ya afka cikin kurakurai, shi ne gaggauta yin cikakkiyar tuba zuwa ga Allah ɗin.

Allah ya ce: "KU TUBA ZUWA GA ALLAH BAKI ƊAYANKU YAKU MUMINAI, DOMIN KU SAMU RABAUTA".

Sannan Manzon Allah ya ce "WANDA YA TUBA DAGA ZUNIBI, TAMKAR WANDA BASHI DA ZUNUBI NE".

Sai dai ita tuba tana da wasu sharudda waɗanda sai an cikasu sannan tubar take zama karbabbiya. Gasu nan kamar haka:

1. Dena aikata saɓon, nan take ba tare da jinkiri ba.

2. Yin nadama bisa laifukan da mutum ya aikatasu abaya.

3. Ɗaukar niyyar cewa mutum bazai Ƙara aikata wannan laifin ba, har abada.

4. Ɗaukar matakin rabuwa da duk wata hanya ko dalilin da zai iya sanya mutum ya sake komawa kan laifinsa na baya. Misali kamar rabuwa da miyagun samari (Har da blocking ɗin lambobinsu, dena alaƙa dasu ko da a kan facebook ko whatsapp da sauransu) ko miyagun Ƙawayen da ke aikata alfasha, tsayar da mijin aure, etc.

5. Idan laifin ya shafi hakkin wani Bil Adama ne (misali kamar sata, ha'inci, da sauransu) to wajibi ne amayar da hakkoki zuwa ga masu shi, ko kuma anemi yafewarsu.

In Shã Allahu rayuwarki za ta gyaru mutukar dai kin tuba domin Allah. Kuma wannan laifin bai shafi hakkin mijin da za ki aura ba. Don haka ba sai kin gaya masa ba. Kiyi shuru da bakinki don kiyaye mutuncinki.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments