Ticker

6/recent/ticker-posts

Kukan Kurciya Cikin Wakokin Korona Biyu

 Kukan Kurciya Cikin Waƙoƙin Korona Biyu


Kukan Kurciya Cikin Waƙoƙin Korona Biyu

Kukan Kurciya Cikin Waƙoƙin Korona Biyu

Sadaukarwa

Cike da farin ciki da ƙauna muna sadaukar da wannan aiki ga Mukhtar Sani Bindawa Katsina da AbdusSamad Muhammad Babson Bauci. Da bazarku ce manazarta waƙoƙin Hausa suke rawa.

GODIYA

Godiya ta tabbata ga Allah wanda cikin ikonsa komai na duniya ke wanzuwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad (s.a.w). Allah Ka yi gafara da rahama ga iyalansa da zuri’arsa da sahabbansa da mabiyansa har zuwa ranar sakamako amn.

Bayan haka, akwai mutane da dama waɗanda wajibi ne mu bayyana matuƙar godiya gare su saboda rawar da suka taka wajen samun nasarar rubuta wannan littafi, Kukan Kurciya Cikin Waƙoƙin Korona Biyu.

Godiya ta musamman ga mawaƙa biyu waɗanda cikin hikimarsu da fasihancinsu ne muka yi rawa, duk kuwa da cewa watakila masana da manazarta da ma al’umma gaba ɗaya su ga cewa rawar da muka taka ba ta burge su yadda suke so ba. Muna godiya kuma saboda yadda suka yi na’am sosai da manufarmu ta rubuta littafi a kan waƙoƙinsu, suka ba mu dukkan haɗin kai, suka jure buge-bugen wayoyinmu da tambayoyinmu a koyaushe muka ƙage. Waƙoƙinku su ne ƙashin bayan wannan aiki. Da ba ku amince ba, da sai dai mu nemi wasu waƙoƙin na wasu mawaƙan. Murna da farin cikinku su ne suka ba mu ƙwarin gwiwar rubuta wannan littafi. Allah ya ƙara muku fasaha musamman ta tsara waƙoƙi kan abin da zamani ya zo da shi domin faɗakarwa da ilmantarwa bayan nishaɗantarwa. Mukhtar Sani Bindawa da AbdusSamad Muhammad Babson mun gode ƙwarai da gaske. Allah Ya saka muku da mafificin alheri duniya da Lahira, amin.

Godiyarmu mai yawa ga Dakta Murtala Aliyu na Sashen Nazarin Koyar da Ilmin Labarin Ƙasa a Jami’ar Bayero, Kano, wanda shi ne tsani zuwa ga Malam AbduSamad mawallafin waƙar Korona mai ‘uwargida’ da ‘maigida. Haka kuma shi ma Malam AbdurRahaman Aliyu (ɗan jarida, mazauni a Katsina) shi ne ya turo mana waƙa mai ‘dattijo’ da ‘jikokinsa’ da kuma lambar wayar Malam Muktar Bindawi. Dakta Murtala da Malam AbdurRahaman, Allah ya saka muku da alhairansa mafifici, amin. 

Godiya ta musamman ga Dokta Bello S.Y. Al-Hassan na Sashen Harsuna da Al’adun Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello (A.B.U.), Zariya. Duk da yawan hidimomin aiki, kome runtsi Dokta bai ƙin yi muna bukatar da muka zo masa da ita. Mu kuma saboda sanin da muka yi masa na naƙaltar adabi, musamman waƙa, da harshe da al’adun Hausa muka tuntuɓe shi da ya rubuta muƙaddimar wannan littafi, kuma kai tsaye ya amsa cike da murna da farin ciki. Dokta Bello, Allah Ya saka ma da mafificin alherinsa, amin. Mun gode ƙwarai.

Ɗaya daga marubutan tana bayyana godiyarta ga “Malamaina da suka jure halayyar mutuntaka, musamman irin ta ɗalibta, da ‘ya’yana musamman Hauwa’u da Abubakar waɗanda ke bukatar kulawata a kowane lokaci amma  hakan ba ta samu ba.”

A ɗaya gefen, marubuci guda yana bayyana godiyarsa ga ɗansa, Garba Abdulƙadir Malami Yahya da matarsa, Dr. Zainab. Garba shi ne wanda a kullum kuma koyaushe yana tsaye don ganin Babansa ya samu ƙoshin lafiya. Garba, tsakanin ɗa da uba sai addu’a kuma Babanka yana kan yin ta. Allah Ya ƙara ma albarka Ya sa ka gama lafiya duniya da Lahira, amin. Haka ita ma Dr. Zainab, tana biye da umurnin mijinta. Ta kasance tsaye wajen dubin lafiyar baban maigidanta. Dr. Zaimab Allah Ya ba ki ladar aure, Ya ƙara maki albarka, Ya sa ki gama lafiya, amin. Ƙanen Garba kuma taubashinsa, wato Baba Yahya Lamiɗo, shi ke walwale muna duk wata matsalar kwamfuta idan muka rikice wurin sarrafa ta. Baba, Allah Ya saka ma da mafificin alheri, amin.

Ba za mu manta ba da AbdurRahman Ibrahim da Ɗanbaba Tchehe (Doktan masu gadi wanda ya ƙi yarda a yi masa farmoshin zuwa Farfesa) da Bashar Ahmad Ɗankawu saboda taimakon da suka yi da tattaunawa da mu game da waƙoƙin. Muna godiya ƙwarai.

Aliyah Adamu Ahmad
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Jihar Sokoto, Sokoto.

Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,                                                  
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.          

10/9/2020

Muƙaddima

Wannan littafi mai suna Kukan Kurciya Cikin  Waƙoƙin Korona Biyu  aiki ne na masana da za a iya yi wa kirari da ’gidan abin', idan dai ana zancen nazarin waƙa ne. Shi wannan littafi tamkar nagge ne, wato daɗi da yawa, ba ma goma ba. A cikinsa za a mori waƙoƙi biyu masu nishaɗantarwa, waɗanda kuma suke faɗakarwa (wato sanarwa da tunasarwa), tare da kyawawan dabarun adabi da suka haɗa da wa'azi da shawara da addu’a, ga kuma fuskokin rayuwa na gargajiya da zamananci suna takin saƙa duka a ciki.

Kamar yadda mawaƙan ba su tsaurara salo ba wajen wanzar da hikimarsu haka su ma marubutan ba su takura ba a jawabansu. An yi sharhi zuzzurfa tare da amfani da harshe mai jawo hankali domin ƙaruwar makaranci, wato a gamsar ba tare da an gimsar ba. Wannan ya daɗa wa littafin kwarjini a idon duk wanda zai yi ma'amala da shi a ilimance kuma a basirance.

Wannan littafi daidai yake da karin maganar Hausawa da ke cewa, kaɗan mai albarka: ga shi madaidaici, sai tarin alherai. Ba shakka wannan aiki zai amfani manazarta Hausa - malaman da ɗaliban - musamman na adabi, hasali ma waƙa, maƙura kuma ta baka. Bayan haka kuma littafin zai amfani manazarta walwalar ɗan Adam, manazarta fannonin sadarwa, manazarta ko kuma masu la'akari da al'amurran yau da kullum da zamantakewar jiya da yau. Haka kuma littafin zai amfani duk wani mai sha'awar karatu a harshen Hausa ko domin samun abokin hira ko kuma fa'idantuwa da maƙasudin saƙon da ya ƙunsa na nuni cikin nishadi. Wannan littafi zai kasance wani abin la'akari da alfahari, saboda rawar da ya taka wajen nuna muhimmancin adabi,  musamman ma waƙa, a matsayin madubi ko hoton rayuwar al'umma, da yake  ɗauke da manufofi da suka haɗa da abubuwan da al'umma take so ko kwaɗayi da waɗanda take ƙi ko shayi.

Tare da farin ciki da bugun gaba da samuwar wannan aiki nake fatar Allah ya ƙara ma mawaƙan da marubutan wannan littafi basira, ya sa littafin ya zama mai amfani ga al’umma gaba ɗaya, ya sa kuma mu dace, amin.

 Dokta Bello S.Y. Al-Hassan,

Sashen Koyar da Harsuna da Al’adun Afirka,
Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. 14/09/2020.

Ƙumshiya                                                                             

Sadaukarwa

Godiya

Muƙaddima

Babi Na Ɗaya

Shimfiɗa

 Babi Na Biyu.

2.0 Turken Faɗakarwa A Waƙoƙin Hausa

2.1 Faɗakarwa da Ma’anarta

2.2 Tubalan Faɗakarwa

 Babi Uku:

3.0  Nazari a Kan Turke da Tubalan Waƙoƙin

       Korona Biyu

3.1   Waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa

3.1.1 Bin Diddigin Waƙa

3.1.2 Tarihin Mawaƙi

3.2    Sharhi kan Waƙar

3.2.1 Zubi da Tsari

3.2.2 Turke da Tubalansa

3.3     Waƙar Korona ta AbdusSamad Muhammad Babson

3.3.1  Bin Diddigin Waƙar

3.3.2 Tarihin Mawaƙi

3.3.3 Sharhi kan Waƙar

3.3.4 Zubi da Tsari

3.3.5 Turke da Tubalansa

 Babi na Huɗu:

4.0Salo da Dabarun Sarrafa Shi a Waƙoƙin

4.1Gabatarwa

4.2 Ma’anar Salo

4.3Salon Waƙoƙin Miƙaƙƙe ne

4.3.1.Dabarun Sarrafawa

  4.3.1.1. Hira

4.3.1.2. Gangara

4.3.1.3. Karin Magana

4.3.1.4. Tambaya

Babi Na Biyar:

5.0 Ƙyallun Nazarin Salo a Waƙar cikin Bidiyo

5.1 Gabatarwa

5.2 Sajewar Zaren Tunani da Aiwatarwa a Rerawa

5.3 Amfani da Idon Zuci

5.4 Ankarar Zuci

Kammalawa

Manazarta

Ratayen Waƙoƙin Da Aka Yi Nazari

Waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa

Waƙar Korona ta AbdusSamad Muhammad Babson

 

Babi Na ƊAya

1.0      Shimfiɗa

 

Waƙa a ƙasar Hausa ta daɗe tana taka muhimmiyar rawa ta fuskoki da dama, kamar ilmantarwa (Muhammad 1977, 1981 da Ɗangambo 1980, 2007 da Yahya 1997, 2001, 2004, 2006, 2016 da Dunfawa 2002) da faɗakarwa (Ɗangambo 1980 da Usman 2006 da Safana 2015 da Halima 2002 da Auta 2017) da nishaɗantarwa (Yahya 2013 a&b da Usman 2006), da siyasa (Birniwa 1987 da Aliyah 2003) da tarihin adabin Hausa (Hisket 1975 da Aliyah 2009, 2017), kai har  ma da gyaran hali (Usman 2006 da Tsoho 2013) da ginin ƙasa (Yahya 2016 da Idris 2016) da ci gaban al’ummar Hausawa (Yakasai 2014), da makamantansu da yawa.

Waƙa a ƙasar Hausa sunanta waƙa sai dai akwai ire-irenta, da waƙar gargajiya/waƙar baka da waƙa rubutacciya, amma dai duka sunansu guda ne, waƙa.Wannan suna ne magabata kamar Shehu ɗan Fodioyo a waƙarsa, Ma’ama’are,suka kira duka waɗannan waƙoƙin (Yahya 1987, sh. 149, bt. 79).Hausawa waɗanda su ne masu waƙoƙin Hausa na baka da rubutattu, sun daɗe tun zamani mai tsawo suna ƙirƙirar waƙoƙinsu.Malaman da suka gabaci Shehu Usmanu su ma kalmar waƙa suka yi amfani da ita don bayyana waƙoƙin. Waƙoƙin Hausa su ne suka riga rubutattu kasancewa a kan takarda. Wannan kuwa ya auku ne saboda sai bayan da Hausawa suka iya karatu da rubutu a dalilin shiga Musulunci da suka yi sannan suka fara yin rubutattu. A kan sadar da waƙoƙin baka, waɗanda akan kira waƙoƙin gargajiya, da baki ne kamar yadda ake sadar da sauran ɓangarorin adabin Hausa na baka,kamar tatsuniya da kirari da karin magana da sauransu. Kamar yadda Ɗalhatu Muhammad ya bayyana a wurin Hausawa waƙa duk waƙa ce, ta baka da rubutatta, sai dai su kasance da kammanni da bambance-bambance (1977, sh. 9-10 ). Saboda waɗannan dalilai na suna da kamanni da bambance-bambance ne za a lura da cewa waƙoƙin sun fi yin tarayya ga jigogi da salailansu. Wurin aiwatar da sadarwa ce za a fi ganin bambanci.

Idan mawaƙi ya ga wani muhimmin abu cikin al’umma da yake son ya faɗakar da al’umma game da shi ko kuma wani sabon al’amari ya zo ga al’umma, musamman a ƙasar Hausa, har dai idan ya shafi kusan dukan jama’a ko wasu mutane masu ruwa da tsaki cikin al’ummar, kamar ‘yan siyasa, ko kuma idan hukuma ce take son al’ummar ta mayar da hankali ga shi al’amarin, to lalle adabin Hausa kan taka muhimmiyar rawa don yaɗa shi. Idan kuwa haka ya samu to ɓangaren waƙa da na wasan kwaikwayo ne suke da babban kaso cikin rawar. Shi kuwa al’amarin kan iya kasancewa mai daɗi ko akasin haka ga jama’a. Misali a shekarun 1967-1970 da aka yi yaƙin basasar Nijeriya lokacin da yankin gabashin ƙasar inda ƙabilar Igbo take ya yi yunƙurin ɓallewa, an samu waƙoƙin faɗakarwa da yawa. A 1968 ne hukumar gidan Rediyon Tarayya na Kaduna ta sa gasar yin waƙoƙi domin ba sojojin tarayyar ƙwarin gwiwa. Sakamakon haka ne aka samu waƙoƙin Hausa fiye da ɗari biyar (500). Abdu Yahaya Bici na CibiyarHarsunan Nijeriya da ke Jami’ar Bayero, Kano ya tattara waɗannan waƙoƙin a 1988. Wani abin sha’awa shi ne a irin wannan yanayi ba akan rasa wasu ɗaiɗaikun mutane ba waɗanda kan ci gaba da ƙirƙirar waƙoƙin da suka shafi irin lalurar da al’umma ta fuskanta. Akwai ire-iren wannan ƙungiya musamman a Kano da mawaƙa kan haɗa kansu domin su faɗakar da jama’a. Misali akwai ƙungiyar da Aƙilu Aliyu ya jagoranta wadda aka kira Ƙungiyar Marubutan Waƙoƙin Hausa. Mawaƙa da yawa ba ma na birnin Kano ba kurum kan shiga irin wannan ƙungiya. Misali, da Alƙali Shehu Alƙanci Sokoto ya ji labarin kafa Ƙungiyar Marubutan Waƙoƙin Hausa, ya ga kuma ba a tuntuɓe shi ba, da shi da sauran mawaƙan da ke yankinsa na Sakkwato, sai ya rubuta wa wannan ƙungiya wasiƙa cikin waƙa, yana mai bayyana mamakinsa na rashin tuntuɓar su da ta yi. A cikin wannan waƙa da ya kira Wasiƙa ta Sha’irci, Shehu Alƙanci ya faɗakar da ƙungiyar su Aƙilu Aliyu da cewa sun fa bar babban kason mawaƙa da ba na watsi da shi ba ne. Ƙungiyar ita kuwa nan da nan ta ba shi amsa cikin waƙa, wadda ta yi amfani da irin karin da Alƙali Shehu Alƙanci ya tsara tasa.  Ƙungiyar ta ba shi haƙuri cikin harshe mai taushi tare da amsa kuskuren da ta yi. Wannan kuwa yana daga cikin tasirran faɗakarwa. Za a iya samun wannan waƙa da ƙungiyar ta rubuta masa mai suna ‘Amsa ga “Wasiƙa ta Sha’irci”’ cikin Aliyu, A.A., Fasaha Aƙiliya (sh.29-33). Ita kuma ta Shehu Alƙanci, wato ‘Wasiƙa ta Sha’irci’, a kundin digirin B.A. na Aminu Galadima­ Batagarawa(sh.185).

Haka nan kuma a shekarar 1982 ma sakamakon gangamin bunƙasa noma da Gwamnatin Tarayya lokacin mulkin shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari ta yi, sai Ƙungiyar Marubuta da Manazarta Waƙoƙin Hausa a ƙarƙashin inuwar Hukumar Al’adu da Yaɗa Labarai ta Jihar Sokoto, ta gudanar da gasa a kan sana’ar noma. Hasili ita wannan ƙungiya ta ci gaba da gudanar da gasar rubuta waƙoƙin faɗakarwa a kan abubuwa da dama. A ƙarƙashin jagorancin Ɗangaladiman Wazirin Sakkwato Alhaji Muhammadu Bello Giɗaɗawa an gudanar da ire-iren wannan gasa kamar a kan aure da Tarbiyya da sauransu. Haka kuma saboda rungumar manyan malamai manazarta harshen Hausa da adabi da al’adunsa da ƙungiyar ta yi sai ta fito da Mujallar da ta shafi ƙudurinta na bunƙasa waƙoƙin Hausa. Sunan wannan mujalla shi ne Dandalin Hikima.

A wannan littafi an yi yunƙurin yin nazari a kan waƙoƙi biyu da al’amarin cutar korona a Najeriya ya haifar. Korona cuta ce wadda ta addabi duniya gaba ɗaya. A nan cikin gida Najeriya, kamar sauran ƙasashen duniya, hukuma ta ɗauki al’amarin cutar da muhimmanci ƙwarai har ma wasu na ganin ta giɗaɗa ta fiye da sauran curotoci waɗanda suke ganin cewa sun fi ta lahani ga rayuwar mutane. Duk da haka hukuma ba ta yi sanyi a ƙafa ba wurin nuna wa jama’a haɗarin wannan cuta. A kan haka sai ta fito da matakan kariya daga korona, saboda ita wannan cuta ba a san ta ba lokacin da ta ɓulla balle a san maganinta. Matakan kuwa sun taɓa lamurran rayuwa masu ɗimbin muhimmanci ga jama’a, domin manya  manyan ɓangarorin al’ada da addini ba su bar su ba. Da sana’a da walwala da ibada, duk matakan sun shige gabansu, abin da ko shakka babu mai tayar da hankalin mutane ne. Tattare da wannan ita kanta hukuma ba ta tsira ba, saboda ya zama tilas ta ba da tallafi ga al’ummarta da matakan suka hana musu fita su nemi na sakawa a baka da kuma sauran abubuwan moriya. Haka kuma ya zama wajibi gare ta ta ɗauki nauyin sha’anin kiyon lafiya, kama daga samar da jami’an lafiya da kayan aikin likita da wuraren keɓe waɗanda cutar ta harba har zuwa ga samar da magani.

Waɗannan matsaloli da hukuma da mutane suka fuskanta sun haifar da kyawawan yanayi da haliyyar da kan zaƙulo basira da fasahar mawaƙa da sauean maƙirƙira adabi gaba ɗaya. Dangane da wannan basira ta waƙa ce wannan littafi zai dubi yadda waƙoƙi guda biyu suka kalli cutar korona da matakan hukuma da kuma matsayin jama’a musamman Hausawa. An kira wannan littafi da sunan Kukan Kurciya cikin Waƙoƙin Korona Biyu saboda irin koken da mawaƙan suke ganin al’umma na yi game da cutar da kuma matakan da aka sa don kariya, da ma zagon ƙasa da ita al’ammar ke ganin wasu macuta suna yi.

 

Babi Na Biyu

 

2.0      Turken Faɗakarwa A Waƙoƙin Hausa

 

2.1 Faɗakarwa da Ma’anarta

Faɗakarwa muhimmiyar hanya ce ta tarbiyya a rayuwar al’ummar Hausawa.A ƙamusun da G. P. Bargery (Bargery 1934) ya tsara wa Gwamnatin Najeriya an shigar da kalmar faɗakarwa wadda asalinta shi ne, “faɗakad da”, aka kuma fassara ta kamar haka:

Awaken; warn; cause p. (wato, person) to understand; cause p. to recall, e.g. a forgotten fact. …

Ana iya fassara wannan kamar haka:

Tayar (da mutum) daga (kwana ko mantuwa); horo; a sa mutum ya fahimta; a sa mutum ya tuno, kamar abin da aka manta. ..

 

Shi kuwa Ƙamusun Hausa (2006) wanda Jami’ar Bayero, Kano ta wallafa, kalmar “faɗaka” ya fassara ta kamar haka: faɗaka (faɗaka, fi.,) farka ko lura ko kula.

Halima (2002) cewa ta yi,

Faɗakarwa na nufin yi wa mutum tuni a kan abin da ya rigaya ya sani wato yana da masaniya a kan abin. Sai dai a daɗa nusarshe shi ta yadda abin zai daɗa ratsa shi.

(‘Nazari A Kan Jigon Faɗakarwa Na Adabin Baka’:sh. 75)

 

Yayin da aikin Halima ya shafi faɗakarwa a kan adabin baka, shi kuwa na Auta (2017) aiki ne wanda ya shafi faɗakarwa cikin rubutattun waƙoƙin Hausa. Marubucin cewa ya yi:

…faɗakarwa, ana tunatar da mutum ne a kan waɗansu al’amuran rayuwa domin ko dai ya aikata abubuwan nan saboda muhimmancinsu kuma ya amfana da su, ko kuma a lurar da mutum ga waɗansu al’amura munana domin ya guje su saboda illarsu. Duk waɗannan abubuwan kuwa akan gabatar da su ne a matsayin jawo hankali da nasiha ga mutum.                                     

(Faɗakarwa A Rubutattun Waƙoƙin Hausa: sh. 26)

 

A fahimtar marubutan wannan littafi, ta la’akari da abin da manazarta suka ce, ana iya cewa faɗakarwa na nufin farkarwa daga bacci ko kwana na jiki ko kuma daga bacci ko kwana (wato shagalta, ko-in-kula, sha’afa) na hankali; horo don mutum ya bi; gargaɗi don ya hankalta; ilmantarwa domin mutum ya yi aiki da sanin da ya samu daga ilmantarwar; tunatarwa domin ya yi abin da yake daidai wanda ya sha’afa ko ya yi watsi da abin da yake yi da ba daidai ba; da kuma jan hankali ko nuni ko ishara, duk kuma domin wanda aka yi wa ita faɗakarwar ya yi aiki da ita, aiki mai amfanin kansa ta gefensa, ko kuma da shi da al’ummarsa gaba ɗaya. A taƙaice ana iya a bayyana faɗakarwa kamar haka:

Faɗakarwa tunatarwa ce ko nasiha; tunatarwa kan abin da aka riga aka sani amma aka sha’afa da shi ko aka yi watsi da shi; nasiha  ce kan abin da aka sani ko ba a sani ba, ko ake yi ko ba a yi. Manufar duka biyu ɗin ita ce a dawo ma hanya madaidaiciya wadda al’umma ta yarda da ita.

 

Faɗakarwa a ƙasar Hausa, kamar sauran al’ummomi, ɗabi’a ce kuma al’ada ce da ake bi domin yin tarbiyya ga yara da manya, maza da mata, talakka da shugaba, ba a bar kowa ba. Faɗakarwa jan kunne ce musamman ga manya ko shugabanni. A kan haka ne Hausawa suke gina adabinsu na baka da rubutacce, ko bayan nishaɗi da suke gina shi a kai.

 

2.2 Tubalan Faɗakarwa

Halima (2002) ta bayyana tubalan ginin turken faɗakarwa cikin adabin baka na Hausa kamar haka:

Tubalan gina jigon (turken) faɗakarwa sun haɗa da matsayi da amfanin abu da muhimmancinsa, da nuna daraja tare da ƙima da fito da martaba da illa da shiryarwa da kyautatawa da kulawa da fito da munanan halaye da ingancinsu da yin gyara, kai har ma da sakamako  (‘Nazari A Kan Jigon Faɗakarwa Na Adabin Baka’:sh. 75)

Ta ƙara bayani da cewa in ban da turken ilmi “wanda shi ma yake da ressa da yawa”,  na faɗakarwa shi ne “ya fi ɗaukar babban kaso fiye da sauran takwarorinsa a cikin adabin Hausa”.

 

Shi ma Auta (2017), kamar Halima, duk da yake ya tattauna sosai a kan wasu ƙananan jigogin (tubalan) babban jigon (turken) faɗakarwa, bai furta iyakar adadinsu ba. Aikin nasa ya duƙufa ne a kan kishin ilmi da muhimmancinsa da illar jahilci da gyaran hali da muni ko illolin shan giya da karuwanci da ɗan daudu da caca da  kuma yi da mutane. Haka kuma ya kawo tubalin kishin ƙasa da kishin harshe da na al’adu da na sana’o’i da makamantan haka.

 

Idan aka zurfafa tunani da nazari za a fahimci cewa lalle nuni da faɗar da Halima da Auta suka yi gaskiya ne cewa ilmi ne kaɗai faɗakarwa ba za ta ja da shi ba. A wata fahimta ana iya cewa ai da ilmi da faɗakarwa tamkar Buzu da raƙumi ne a faɗar Bahaushe da ya ce, ‘kowa ya ga raƙumi ya ga raƙumi’. Abin nufi a nan shi ne yadda babban jigon ko turken ilmi yake da tarin ƙananan jigogi ko tubalai haka na faɗakarwa yake da su. Haka kuma ana iya a ce da ilmi da faɗakarwa duka suna karakaina ne a kan rayuwa. Idan ɗan Adam ya samu ilmi to kuwa saboda zamansa ɗan tara bai kai goma ba, to lalle sai ya samu faɗakarwa. Kasancewarsa ɗan tara ta yiwu idan ya sani ya manta ko ya yi watsi da sanin da gangan. Hakan zai sa ya zamo wanda za a yi wa faɗakarwa. Idan ma ya samu ilmin bai manta da shi ba kuma bai yi watsi da shi ba, akan jaddada mai ilmin domin kada ya manta ko ya yi watsi da shi. Wannan ma turken faɗakarwa ne.

A ɓangaren waƙoƙin faɗakarwa akwai na baka da rubutattu da kuma waɗanda Bello Bala Usman ya kira, ‘Ruwa Biyu’, waɗanda suka ƙunshi sigogin duka biyu da aka fi sani a nazarin waƙoƙin Hausa (Usman 2018). Waƙoƙin Wazirin Gwandu da na Sambo Wali Giɗaɗawa da na Alhaji Garba Gwandu G.G. tarshe suke da jigon na faɗakarwa, kamar yadda waƙoƙin Alhaji (Dokta) Mamman Shata da na Alhaji Musa Ɗanƙwairo da na  Alhaji Aminu Aliyu ALAN Waƙa suka ƙunshi wasu da ke ɗauke da wannan turke na faɗakarwa.

Babi Uku

3.0 Nazari A Kan Turke Da Tubalan WaƙoƙinKorona Biyu

A ƙarƙashin wannan babi za a yi tsokaci a kan wasu waƙoƙi guda biyu da aka yi kan cutar korona (corona virus/covid-19 a Turance). Waɗannan waƙoƙin kuwa su ne ‘Waƙar Korona’ wadda wani  maigida kuma dattijo da jikokinsa mata biyu ke rerawa, da kuma ‘Waƙar Korona’ wadda wani maigida da matarsa ke rerawa. Waƙa ta farko ita ce wadda Mukhtar Sani Bindawa ya yi, ta biyu kuwa wadda AbdusSamad Muhammad Babson ya yi.Sai dai wani hanzari ba gudu ba, waɗannan waƙoƙi ba su kaɗai ne aka yi kan cutar korona ba, kuma ba tubalan da suka ƙunsa su kaɗai ne ke cikin waƙoƙin cutar korona ba, har dai idan aka yi la’akari da yadda Auta (2017) ko Halima (2004) suka bayyana su. Haka kuma a yanzu ne mawaƙa ke kan ƙirƙiro waƙoƙin Korona saboda a bana ne cutar ta ɓulla a wannan ƙasa cikin watan Fabrairu. Hasali, ko masana kimiyya da likitoci ba su gama sanin cutar ba a faɗin duniya.

Tsokacin da zai zo zai yi ƙoƙarin nuna cewa duk da yake faɗakarwa ce, to amma mai saurare a farkon saurarensa zai ɗauka cewa muhimmin turken da suka ƙunsa shi ne faɗakarwa da ya ginu da tubalan illolin cutar korona ga ɗan Adam da kuma tubalan shawarwari na likitoci daga hukuma. To sai dai a zahirin gaskiya faɗakarwa ce ga shugabanni da talakkawa ta fuskoki biyu. Ta fuskar shugabanni waƙoƙin suna faɗakar da hukuma kan  matakan da take ɗauka don daƙile cutar korona, a haƙiƙanin gaskiya illa ce suke yi wa talakkawan. Ta fuskar su kuwa talakkawan faɗakarwar ta danganci ƙuncin da suka shiga da kuma ayyukan saɓon da suke yi. Waɗannan ƙananan jigogi ko tubalai su suka fi jan hankalin mai saurare fiye da matakan kariya da hukuma ke son talakkawan su ɗauka.Su ne tubalan da waƙoƙin suka fi jaddadawa.

3.1Waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa

3.1.1   Bin Diddigin Waƙa

Mun samu wannan waƙa ta Mukhtar Sani Bindawa daga shafin zumunta na whatsApp a watan Mayu na shekarar 2020. Lokacin da muka yi niyyar yin nazari a kanta sai muka yi ƙoƙarin saduwa da mawaƙin da ya yi ta ta neman samun lambar wayarsa muka tuntuɓe shi. Mun kuwa dace muka sami lambar daga Malam AbdurRahman wanda muka samu tuntuɓa ta amfani da shafin zumunta na Gidan Manazarta Hausa. Shi ya ba mu lambar Malam Mukhtar Sani Bindawa da ma na wasu mawaƙa. Nan take kuwa muka tuntuɓi Mukhtar Sani Bindawa ran 27 ga watan Mayu, 2020, kuma ya yi muna maraba ƙwarai da gaske.

An fara da kiran wannan waƙa mai dattijo da jikokinsa biyu mata domin a gane wadda ake nufi, saboda dalilai biyu. Dalili na farko shi ne waƙar ta fito cikin hoto mai motsi, wato bidiyo. Dalili na biyu kuwa shi ne domin a sanar da mai kallo ko saurare cewa wanda yake kallo ko saurare a matsayin jagoran waƙar ba shi ne mawallafin waƙar ba. A hirar da marubutan wannan littafi suka yi da mawallafinta ya sanar da su cewa saboda fatar jama’ar da ake son su ji waƙar su kuma ɗauki saƙon da ta ƙunsa da ƙima da muhimmanci a matsayinsu na zama Hausawa kuma al’ummar Musulmi, sai ya zaɓi ya sanya dattijo ya rera waƙar tare da ‘yan mata matasa ‘yan makaranta. ‘Yan matan kuwa ‘ya’yansa ne. Shi kuwa ainihin mawallafin da yake matashi ne sai ya janye shiga cikin hoton bidiyon rera waƙar. A ganinsa al’ummar Hausawa za su ƙara ɗaukar saƙon waƙar da muhimmanci. Dattijo ne da ‘yan mata a matsayin jikokinsa ke rera waƙar, ba matashi da budare ba, tsarin da zai iya sa masu kallo da saurare shagala. Wannan kuwa ba ƙaramar tsinkaya ce mawaƙin ya yi ba. Yin irin haka wata dabara ce ta salon tsara finafinai, kamar yadda Hagen (1991) ta nuna lokacin da take kafa hujjar muhimmancin yin kwatanci ga mai aiwatar da wasan kwaikwayo:

When Laurette Taylor insisted that all that was needed to be a fine actor was imagination, I thought:How wonderful, I have a lot of that. (Uta Hagen, A Challenge for the Actor: p. 69).

Fassara:

Da na fahimci Laurette Taylor ta nace da cewa idon zuci kaɗai ne ɗan wasan kwaikwayo ke bukatar ya mallaka, sai tunani ya zo min:Ya yi daidai! Ai kuwa ina da wannan birjit.      (Uta Hagen, A Challenge for the Actor: sh..69). 

Marubucin wannan waƙa ya ce tunanin ya rubuta ta ya zo masa ne lokacin da cutar korona (corona virus/covid-19) ta bayyana musamman a Najeriya. Ya ce ganin cewa baƙuwar cuta ce wadda ta game duniya, kuma mai saurin yaɗuwa, ya kuma lura da yadda hukumar Najeriya ke ɗaukar matakan ganin ta daƙile ta ta hanyar yekuwa ga jama’a, tana son mutane su dage da ɗauka kamar sa takunkumi da sauransu, sai mawaƙin ya ga shi ma ya kamata ya ba da tasa gudunmawa kamar kowa. A kan wannan dalilin ne ya yi wannan waƙa a makon farko na watan Afrilu na wannan shekara ta 2020. Ya yi ta ya saka ta cikin bidiyo a Ƙofar Sauri. A taƙaice ganin dama ta sa mawaƙin ya yi ta, ba sa shi aka yi ya yi ta ba kamar wata wadda ya ce Gwamnatin jihar Katsina ta sa shi da ya yi. Ya kuma saka ta cikin bidiyo a ɗakin ɗaukar waƙoƙi, wato sitidiyo, nasa da ke a Ƙofar Sauri, wata unguwa a garin Katsina.

3.1.2 Tarihin Mawaƙi

Sunan wanda ya rubuta wannan waƙa da aka kira Korona shi ne Mukhtar Sani Bindawa wanda aka fi kira da Mukhtar Bindawa kai tsaye. Shi ne ya rubuta ta, ba wani ko waɗanda suka fito cikin bidiyo ba. Mukhtar Bindawa ya dai saka su ne su rera waƙar da nufin a kalli namijin a matsayin wani dattijo tare da wasu ‘yan mata biyu suna rerawa a matsayin kaka da jikokinsa.

Mukhtar Bindawa mutumin garin Katsina ne. A nan aka haife shi shekaru arba’in (40) da suka wuce a ƙofar Durɓi, ranar Talata 22/04/1980. Sunan mahaifinsa shi ne Malam Sani Lawal. Sunan mahaifiyarsa kuma Hajiya Rammanatu Muhammad, dalilin da ya sa ake kiran wata ‘yarsa da laƙabin Ummi don ita ma sunan da aka sa mata ke nan.

Mukhtar ya fara karatun Addinin Musulunci ne a nan Katsina daga mahaifinsa kuma kamar kowane yaro ko yarinya, ya fara ne da karatun babbaƙu. Haka kuma daga baya ya koma ga mahaifiyarsa, lokacin da aka sa shi makarantar Addini ta wani mallami mai suna Malam Sani Musa Bindawa. A gun wannan mallami ne ya ci gaba da karatun Alƙur’ani sannan kuma ya fara karatun sani. Akwai daga cikin abin da ya karanta littattafan Hadisi da na Fiƙhu da na Sira har da ma na koyon tajwidi. Waɗannan littattafai irin waɗanda aka saba karantarwa ne a ƙasar Hausa, kamar Arba’una Hadisi da Ashmawi da Risala da makamantansu.

Haka nan kuma a lokacin da ya kama aikin ɗan sanda aka kai shi garin Maiduguri, Malam Mukhtari ya ci gaba da neman ilmin Addini. A farko buɗa makarantar Allo ya yi da kansa a gidan wani ɗan uwansa. A nan ya karantar da yaran da suka haɗa da ‘ya’yan ɗan uwansa da na maƙwabta. ‘Yan Makarantar Malam Mukhtar da kaɗan kaɗan har suka kai su hamsin da ‘yan kai. To amma saboda yanayin aikin da yake yi wannan makaranta ba ta ɗore ba. Sai dai kuma a wurinsa shi kansa neman ilmi bai kuɓuce masa ba, saboda ya jiɓinci limamin masallacin da yake yin hamsa salawatu yana sa littattafan sani a wurinsa.

Malam Mukhtar ya bayyana cewa an sa shi makarantar furamare da ake kira Makarantar Filin Samji amma yanzu Makarantar Sandabale ake kiran ta, a nan cikin garin Katsina, har ya kai aji ukku sannan aka mayar da shi Bindawa inda ya shiga aji huɗu ya ci gaba har ya shiga makarantar Sakandare wadda ya kammala a shekarar 1999.

Tun Mukhtar yana ɗan shekaru goma sha takwas (wato a 1998) ya fara rubuta waƙa, a makarantar Islamiyya. Waƙarsa ta farko ita ce wadda ya yi wa ‘yan makarantar waɗanda suke ajin kafin wanda shi yake. Ya yi ta ne a kan yadda ya kamata ‘yan makaranta su kasance a gida lokacin hutu. A taƙaice waƙa ce ta nasiha da faɗakarwa, kamar dai sananniyar waƙar nan ta Wazirin Gwandu Alhaji Dokta Ummaru Nasarawa mai suna,‘Waƙar Gargaɗi Ga ‘Yan Makaranta’ (Usman: 2006).

Lokacin da Mukhtar ya kammala karatun sakandare sai ya sami shiga aikin ɗan sanda a shekara ta dubu biyu 2000 Miladiyya, ya yi koyon aikin a garin Kaduna. Yana kammalawa sai aka tura shi zuwa garin Maiduguri. Yana can tun daga lokacin mulkin Gwamna Mala Kachalla har zuwa na Ali Modu Sherif wanda ya yi mulkinsa daga 2003 zuwa 2011. To tun zamanin Gwamna Mala Kachalla zuwa na Gwamna Sherif ne shi Mukhtar Bindawa yake yin waƙoƙi galibi na finafinai sannan na siyasa. A shekarar 2010 ya nemi a mai da shi jihar Katsina kuma ya dace ya samu, inda yake har zuwa yau 2020. A halin yanzu dai Mukhtar sufeto ne na ‘yan sanda (Police Inspector), kuma har yau yana rubuta waƙoƙinsa ya kuma sa su a bidiyonsa da ke Ƙofar Sauri a nan cikin garin Katsina. A nan ne ma ya saka waƙar da ake nazari nan, Waƙar Korona, cikin bidiyo.

Mukhtar Bindawa ya rubuta waƙoƙin finafinai da na siyasa da kuma na faɗakarwa kamar wannan waƙa ta Korona. Ya bayyana wa marubutan wannan littafi cewa a farkon lokacin da yake a Maiduguri ya fi mai da hankali ga rubuta waƙoƙin finafinai amma ba su da yawa. A cewarsa waɗanda yake iya tunawa guda huɗu ne har da wasu guda biyu da aka sa cikin wani bidiyo da aka kira, Zafin So. Su waɗannan waƙoƙI wata da ake kira Hauwa Katanga ta hau su cikin fim ɗin. Akwai kuma wata da ya yi da shi da wata mai suna Sadiyya Gele. Ya ci gaba  da yin waƙoƙin finafinai sannan daga baya ya koma ga yin waƙoƙin siyasa lokacin Gwamna Mala Kachalla har zuwa na mulkin Ali Modu Sherif. Ya ce waƙoƙinsa na siyasa galibi yakan yi su ne a kan turken faɗakarwa, saɓanin yadda wasu mawaƙa takwarorinsa kan yi suna yabon gwarzonsu da magoya bayansa, kuma su yi wa abokan hamayyarsa zambo. Shi kuwa Mukhtar ya fi mai da hankali ga yi wa nasa gwarzo gyara-kayanka da kuma hannunka-mai-sanda. A taƙaice Mukhtar ya fi mai da hankali ga gargaɗi da jan hankali da faɗakarwa. Babban misali a nan ita ce waƙar da ya yi wa Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari wadda ya kira, “Buɗe Idonka Buhari Ka Lura Waɗansu na yi maka Zamba”. Shi a ganinsa waƙoƙin nan nasa na siyasa ta wannan fuskar ce suka banbamta da na sauran mawaƙa.

Bayan waƙoƙin siyasa Mukhtar Bindawa yakan kuma rubuta waƙoƙi kan aikinsa na ‘yan sanda. Daga cikin waɗannan akwai waƙar da ya kira, ‘Ɗan sanda Abokin Kowa’. Su ma waɗannan waƙoƙi turkensu na faɗakarwa ne.

Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin mawaƙinmu, Malam Mukhtari Sani Bindawa, haifaffen birnin Katsina wanda a halin yanzu yake nan a Katsina a matsayin Sufeton ‘Yan Sanda. Allah Ya ja zamaninsa Ya ƙara ɗaukaka shi tare da kariya, Ya sa ya gama lafiya, amin summa amin.

Mukhtar Sani Bindawa

Mukhtar Sani Bindawa
Mawaƙin da ya yi Waƙar Korona mai dattijo  da ‘yan mata biyu
(An samo hoton daga mawaƙin.)

Rammanatu Mukhtar (Ummi)

Rammanatu Mukhtar (Ummi)            

 

Fatima Mukhtar

Fatima Mukhtar

(Hotunan ‘yan matan da ke cikin bidiyon waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa. An samo su daga mawaƙin wanda kuma shi ne mahaifinsu.)

Umaru Ibrahim Rimi (Sarkin Fawa.)

Umaru Ibrahim Rimi (Sarkin Fawa.)

(Hoton dattijon da ke cikin bidiyon waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa)

3.2      Sharhi kan Waƙar

3.2.1   Zubi da Tsari

Wannan waƙa ta ƙunshi zubin ɗiya ashirin (20). Mafi yawa daga cikinsu sun ƙunshi layuka 4 (ɗ.17) zuwa 6(ɗ. 1, 18), amma akwai ɗa mai layi guda kamar ɗ.3, 4,13. Haka kuma akwai mai layuka 12 kamar ɗ.15 da mai ɗiya har 14 kamar ɗ.14. Haka kuma akwai ɗiya biyu waɗanda aka saka ayar Al-Ƙur’ani tsakaninsu. Ita ayar ita ce aka sanya cikin ɗa na goma sha ɗaya, ɗ.11, ma’anar fassararta kuwa a ɗa na 12. Wannan irin zubi ne na waƙar baka, wato na rashin daidaton layuka a ɗiyan waƙa.

 

Abin da za a fahimta ta fuskar tsarin waƙar shi ne cewa an tsara ta cikin tsarin da Bello Bala Usman (2018) ya kira ‘tsarin ruwa-biyu’. Abin nufi shi ne waƙar da ake samun tana bin wasu sigogi na rubutattar waƙa a gefe guda, yayin da a ɗaya gefen ta ƙunshi wasu sigogin waƙar baka. Tattare da waɗannan sigogi ‘Waƙar Korona’ take. A mafi yawan ɗiyanta ta ƙunshi abin da ake kira ƙafiya, wato amsa-amo, a rubutattar waƙa. To kuma amsa-amon waje ne, ko babban amsa-amo, mai gaɓar /ba/ shi ne ya mamaye kusan ƙarshen kowane ɗan waƙar. Ga misalin da ya ƙunshi rashin daidaiton layuka cikin ɗiyan waƙa a waƙar baka da kuma samun amsa-amo musamman na waje, babban amsa-amo, a rubutattar waƙa:


 18. Matakan da gwamnati ke ɗauka

 Mu yi haƙuri da su

 Kar mu yi kuka da su

 Umurnin ma’aikatan lafiya

 To mu yi riƙo da su

 Kar mu yi wasa da su

 In an ce mu zauna gida mu zauna

 Don kariyarmune

 Da ka ji alama ka taɓa kanka

 Kar ka shiga mutane

 In ka ji inda cutar take

 To kar da ka shiga

 Idan kana garin da cutar take

 To kar da ka fita

 Mu daina zargin ba gaskiya ba ce ba

 Kar da mu ƙaryata

 Mu daina zargin cewa waɗansu

 Ne sunka ƙirƙira ta

 Mu roƙi Allah Ubangiji

 Mu sunkuya ƙasa mu tuba

Wata sigar rubutattar waƙa ta wannan waƙa ita ce samun ayoyin Ƙur’ani ko wani hadisi cikin waƙa. A ɗa na 11 mawaƙin ya fara shi da, / Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un/, wanda wani sashe ne na aya ta 156 cikin Suratul Baƙara (wato, 2:156). Ayar tana karantar da Musulmi cewa idan wata musiba ta same su to su furta wannan sashe wanda mawaƙin ya kawo cikin wannan ɗan waƙarsa. Daga nan kuma sai aka sake kawo wata aya bayan faɗar, /Ƙalallahu Ta’ala.../. Ayar ita ce ta 30 cikin Surat -ash Shura (wato,42:30). To amma fa a lura da cewa amfani da wannan siga cikin waƙa wani salo ne wanda za mu tattatauna a gaba cikin ɓangaren salo. Haka nan kuma akwai kalmomin harshen Larabci a farkon ɗan na 11 inda ya ce /Ƙalallahu Ta’ala fi Ƙur’anil Karimi…/, wato, ‘Allah Maɗaukaki Ya ce a cikin Ƙur’ani mai girma’. A nan kai tsaye sai mawaƙin ya kawo fassarar ma’anar abin da Allah ya ce cikin al-Ƙur’ani. Wannan magana ita ce ke cikin Surat al- Shura, aya ta 30 (42:30). Ita ma wannan aya mawaƙin ya kawo ma’anar fassararta kai tsaye da kammala ta. Wannan siga ta sake bayyana a ɗa mai bi ma wannan na yanzu. A nan ma sigar harshen Larabci ce. Haka kuma ta wani ɓangare siga ce ta marubutan waƙoƙin Hausa inda sukan kawo ma’anar baƙuwar kalma da ba Hausa ba, kuma kusa da inda suka kawo kalmar ko jimlar. A taƙaice saka kalmomin Larabci cikin wannan waƙa fitacciyar sigar rubutattar waƙar Hausa ce mawaƙin ya yi.

Akwai daga cikin sigogin waƙoƙin Hausa na baka rashin daidaiton yawan layukan ɗiyan waƙa. Akan samu ɗa mai layi guda sannan mai bi masa ya kasance da layuka uku ko huɗu ko goma ko ma fiye da haka. Duk da shike mun kawo misali tun farko tattare da wata magana kan waƙar baka da rubutatta a dunƙule, ya kamata a jaddada cewa wannan sigar a bayyane take cikin wannan waƙa ta Mukhtar Bindawa. Ɗa na 3 da na 4 da na 6 da na 8 misalai ne na masu layi guda guda, alhali ɗiya na 1 da na 5 misalai ne na ɗiya masu layuka 5 da 3. Ga kaɗan daga misalan waƙar:

 

Ɗiya masu layi ɗaya ɗaya:

 3. Dattijo!

 …

 4. Na’am ya aka yi jikanlena?

 …

 6. Miye maganinta jikokina?

 …

 8. Wayyooo

Ɗiya masu layuka fiye da ɗaya ɗaya:

1. Ta zo gare mu annoba

Wayyo Korona wayyooo

Cutar Korona ta sa ba za mu je kasuwa mu je gona ba

Masallatan Jumu’a an kulle

Da wayona ni ban taɓa gani ba

 (layuka5).

 5. Takunkumi da wanke hannu

 Su kaɗai ba za su sa komai ba

Ba za su raba ka da annoba ba

 (layuka 3).

 

Wata sigar waƙar baka ita ce rashin daidaiton tsawon layuka cikin ɗa guda. A ɗa na farko mun samu layuka biyu na farin sun bambanta da na uku wanda ya fi duk sauran huɗu ɗin tsawo ta fuskar yawan kalmomi. Layi na ɗaya yana da kalmomi biyar, layi na biyu yana da kalmomi uku, shi kuwa layi na uku yana da kalmomi tara a yayin da layi na huɗu yake da kalmomi huɗu rak yayin da layi na biyar ya ƙunshi kalmomi guda bakwai. To da irin wannan siga sauran ɗiyan wannan waƙa suka kasance.

 

Haka kuma daga cikin sigogin waƙoƙin baka na Hausa akwai kiɗa da amshi da kuma amsa-amon murya. To duk waɗannan akwai su cikin waƙar Bindawa ta Korona. Ƙari da haka shi ne shi kiɗan da ke cikinta irin na sitidiyo ne, sannan kuma akwai abin da ake kira hawan waƙar da dattijo da ‘yan mata biyu ke yi. Waɗannan sigogi biyu duk na zamani ne da aka aro daga kiɗa irin na zamani mai asali daga Turai da Indiya da ma ƙasashen Larabawa kamar Masar da Sudan, ko kuma mu hutar da kawunammu mu ce daga tsari irin na finafinai. A nan sai mu ce yin hawan waƙa bai yiwuwa sai masu yin sa sun kasance a natse saboda mai hawan waƙa tamkar ɗan wasan kwaikwayo ne wanda samuwar natsuwar zuciyarsa dimun ce kuma tilas (Hagen: 106)

3.2.2 Turke da Tubalansa

Mawaƙin ya buɗe waƙarsa da ambaton turken waƙarsa, wato Cutar Korona, wanda kuma ya gina da tubalin firgita wanda shi ne kukan cutar da ta sami al’ummarsa, wadda kuma ya nuna cewa ta jima tana yaɗuwa cikin duniya kafin ta kawo ga al’ummar tasa:

 1.Ta zo gare mu annoba

 Wayyo Korona wayyoo

 

Kalmomin waɗannan layuka cike suke da kaifin ma’ana. Cewar da ya yi /ta zo/ nuni ne cewa abin nan fa tuni ya kai wasu wurare. Sannan da ya ce / gare mu annoba/, magana ce kai tsaye ba tare da wani tsaiko ba, cewa abin nan fa da ta riga ta je wasu wurare, annoba ce wadda sunanta ya game duniya, wadda ake kira Korona, cuta ce da kowa ke gudu, ita ce ta shigo ba tare da kowa ya shirya zuwanta ba cikin al’ummar mawaƙin. A taƙaice ta zo babu duk wani shiri. A kan haka ne mawaƙin ya yi kururuwa ta amfani da kalmar ‘wayyo’ wadda kowane Bahaushe da ya ji ta ya san wani abu ne mummuna aka gani kuma abin gudu da tsoro. Ga al’adar Hausawa, da zarar aka furta wannan kalma to duk wanda ya ji ta ya san da cewa ba abin alheri ne mai furta ta ya ji ko ya gani ba.

 

Mawaƙin ya ci gaba da ginin wannan ɗan waƙar da bayyana matsalolin da shi da al’ummarsa suka shiga, ciki kuwa har da matsalar da take ba abin da za a taɓa nasartawa ne ba ga rai. Ga abin da ya ce:

Cutar Korona ta sa ba za mu je kasuwa mu je gona ba

Masallatan Jumu’a an kulle

Da wayona ni ban taɓa gani ba

Noma da kasuwanci manyan sana’o’in ƙasar Hausa ne. A nemi Bahaushe ya bar su babban al’amari ne. Barin su sai mutuwa ko tsananin ciyyo. Hasali da waɗannan sana’o’in ne Bahaushe ke kare kansa daga yunwa da ciyyo da kuma mutuwa. Idan kuwa kana son ya daina yin su to kuwa tilas ka samar masa madadinsu. To amma abin da ya fi waɗannan ciyyo ga a bari ko ma wanda bai saɓuwa ga Bahaushe shi ne ka ce masa ya daina bauta wa Mahaliccinsa Allah. Wannan kuwa shi ne aka nemi Bahaushe ya yi. Wato aka ce ya daina zuwa masallaci inda yake yin wannan bauta. A nemi ya daina zuwa masallaci ba ma babban al’amari ba ne, a’a, abin da bai taɓa gani ba ne kuma ba zai yiwu ba. Lokacin rubuta wannan littafi kafafen labarai sun sha kawo labarin cewa jami’an tsaro suna fama da mutane a masallatai da coci-coci da kuma a kan hanya, waɗanda ke bijire ma matakan kariya don su yi ibada ko su je neman abinci ta hanyar kasuwanci.

Waɗannan al’amurra guda uku, noma da kasuwanci da kuma ibada, tubalai uku ke nan da mawaƙin ya fara ginin turken waƙarsa, wato faɗakarwa kan cuta ko annobar Korona. Yana faɗakar da al’ummarsa cewa wannan annoba tana tilasta jama’a ga su yafe zuwa gona don su nemo abin da za su ci, su yafe zuwa kasuwa inda za su yi saye da sayarwa don biyan bukatunsu na yau da kullum, waɗanda suka ƙunshi sayar da albarkatun noman da suka yi, don su sayi abinci ko sutura da makamantan haka. Faɗakarwar ta kuma ginu da tubalin da ke nufin Hausawa su daina zuwa masallaci da coci saboda gudun su harbu da cutar korona.

Bayan waɗannan tubalai uku sai mawaƙin ya shigo da tubalin tsafta da na daina yin mu’amala inda yake cewa:

2. Zan riƙa yawaita wanke hannu

Sannan na sanya takumkumi

Na koma gida ba za ni fito ba

A nan mawaƙin yana faɗakar da jama’arsa kan su lura da cewa guje wa cutar korona na bukatar mutum ya rinƙa wanke hannuwansa a kai a kai, kuma ya riƙa saka ƙyalle mai rufe baki da hanci saboda kar wannan cuta ta samu kafar shiga cikin jikinsa. Haka nan kuma cutar ba ta jure ganin mutane suna kai-komo. A taƙaice makarin kamuwa da wannan cuta shi ne a zauna cikin gida a daina yin mu’amala. Haƙiƙa duk waɗannan tsauraran matakai ne na kariya daga cutar korona. Tsaurara ne musamman ga Hausawa waɗanda a manyan sana’o’insu, noma da kasuwanci, tilas ne su fita waje domin aiwatar da su. Wanke hannuwa da rufe baki da hanci bai yi tsauri kamar zama cikin gida koyaushe ba, wato kulle kamar matan aure.

Abin jaddadawa shi ne duk waɗannan tsauraran matakai a ƙarƙashin tubalin farko suke na turken faɗakarwa kan cutar korona. Tubalin kuwa shi ne tubalin matakan kariya. Muna iya cewa mawaƙin ya yi wa wannan tubali rassa na tsafta da kulle.

To amma fa duk waɗannan matakai masu tsauri ba su ne abin damuwa ba a ra’ayin mawaƙin, ta bakin da ya ara na ‘yan mata ya ci musu albasa. A cewarsa duk waɗannan matakai ba za su hana kamuwa da cutar korona ba. Kariya kam ita ce komawa ga Allah da jama’a za su yi su tuba gare shi, su daina saɓa wa umurninsa:

3. Dattijo!

4. Na’am ya aka yi jikanlena

5. Takunkumi da wanke hannu

Su kaɗai ba za su sa komai ba

Ba za su raba ka da annoba ba

6. Miye maganinta jikokina?

7. Saɓon Ubangiji zunuban da muke

Sunka ja mana

8. Wayyoo!

9. Cutar korona mashaƙo

Rashin kumya muka wa Allah

Kuma ba za ta kau ba

Sai mun tuba

Abin da ya bayyana a nan shi ne mawaƙin ya ci gaba da gina turken waƙarsa da tubalai guda biyu. Tubali na farko shi ne abin da ya kasance dalilin ɓullar annobar korona, wato saɓon da mutane ke yi wa Allah. Wani tubali shi ne abin da zai kasance kariya da maganin annobar, wato komawa ga Allah.

Jin wannan bayani kan dalilin aukuwar annobar korona da kuma kariya daga kamuwa da ita da maganinta, wato aikata zunubbai da yin tuba ga Allah, shi ya sa nan take mawaƙin ya kawo mana yadda ake aiwatar da tuba. Ya kuwa yi haka a layin farko na ɗa na goma, /Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un/. Haka kuwa ci gaba ne na ƙoƙarin gina turken faɗakarwa da tubalin komawa ga Allah, wato tuba.

 

Mawaƙin ya ci gaba cikin wannan ɗa na goma da amfani da waɗannan tubalai na saɓon Allah Ubangiji da yin tuba gare shi, yana mai jaddada su har zuwa ɗa na goma sha biyar (ɗy na.10 -15). Ga dai abin da yake cewa cikin ɗa na goma gaba ɗayansa:

10. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un

Saɓon Ubangiji zunuban da muke

Sunka ja mana

Cutar korona mashaƙo

Su suka ja muna, hangenmu

Ba mafita gare mu

Sai mun tuba

Allah Ubangiji mun tuba

A ɗa na goma sha ɗaya (ɗ. 11) ma mawaƙin jaddada tubalin tuba ya yi kuma ya yi hakan ne ta kawo matuƙar hujjar kiran da yake yi na mutane su tuba. Matuƙar hujja ita ce aya ta talatin ta Surat Ash- Shura cikin Alƙur’ani mai girma (42:30). Bayan ya kawo ayar nan kamar yadda take cikin Alƙur’ani da harshen Larabci sai mawaƙin ya kawo fassarar ma’anarta cikin Hausa a ɗa na goma sha biyu (ɗ.12) yana cewa:

12. Allah Ubangiji Ya ce

Da mun ga masifa annoba

Da hannunmu mu muka jawo ta

Amma kuma Allah na afuwa

Da mun koma gare shi mun tuba

Haka nan kuma kamar yadda mawaƙin ya bayyana misalin yin tuba a ɗa na goma layin farko, ya kawo wani misali a ɗa na goma sha uku inda yake cewa cikin kalmomi na ƙanƙan da kai:

 13. Allah Ubangiji mun tuba

 Ka yi muna lamuni

 Albarkacin ƙananan yara

 Albarkar managartan bayi

Bindawa a nan ya ƙanƙan da kansa ya yi roƙo ga Allah yana mai yin tawassuli da masu daraja ga Allah, wato ƙananan yara da kuma mutane masu nagarta masu yin ɗa’a gare Shi. Ya ambaci ƙananan yara saboda a shari’ar Musulunci yara ba su da zunubi ko ɗaya a wurin Allah, shekarunsu ba su kai yawan da za a rubuta musu zunubi ba, ko me kuwa laifin da suka aikata muddin dai ba su balaga ba. A shari’ar Musulunci hukumci bai hawa kansu sai sun balaga kuma suna da hankali. Su kuma manyan da ya yi tawassuli da su su ne waɗanda suka kasance masu ɗa’a ga bin umurnin Allah, suna yin abin da ya umurce su da su yi, suna kuma barin abin da ya ce su bari, baligai ne masu hankali. Waɗannan su ne shari’ar Musulunci ta hau kansu amma suka kasance ‘managartan bayi’ na Allah, masu bin umurninSa. Wannan kuwa ya zo daidai da hukumcin da usulid addini wanda ke karantar da cewa tauhidi ya shafi Musulmi baligi mai hankali, tamkar dai yadda huɗubar Shehu Usmanu ɗan Fodiyo ta yi nuni (Bello:Infaƙul Maisuri:sh.74-5).

A ɗa na goma sha bakwai (ɗ.17) ne mawaƙin ya ƙara yin amfani da tubalin tuba ya yi kira ga rukunonin al’ummarsa cewa duk su yi gyara ga rayuwarsu. Hasali mutum na iya cewa Bindawa bai cire kowa ba ga wannan kira na a yi gyara ga rayuwa:

 17. Shuwagabanni talakawa

 Da malamanmu da ‘yan kasuwa

 Masu hukumci alƙalai

 Ma’aikatan tsaronmu jami’ai

 Da sauran masu madafan iko

 Talakawan birni ko saƙo

 Jama’a maza da mata

 Kowa ya san abin da yake yi wa Allah

 Wanda ba daidai ba

 Mu daina kawai mu tuba

 Astagfirullah astagfirullah

 Astagfirullah Allah astagfirullah

 

Mawaƙin bai cire kowa ba a wannan kira da ya yi. Ya kira shugabanni da talakawa, kuma domin mai saurare ya tabbatar da haka sai ya rattabo manya manyan shugabannin. Sun haɗa da malamai da ‘yan kasuwa da jami’an tsaro da duk wani mai riƙe da wani muƙami cikin al’umma. Daga nan sai kuma ya ƙara jaddada cewa har da talakawa kuma mazansu da matansu. Kiran nan nasa bai bar kowa ba. Yana son kowa ya binciki kansa ya ga ina ne yake aikata saɓo domin ya gyara ko ta gyara. A nan mawaƙin ya rufe ginin turken waƙarsa da tubalin tuba wanda ya faro tun a ɗa na bakwai bayan da ya yi tambayar maganin korona a ɗa na shidda.

 A ɗa na goma sha takwas (ɗ. 18) ne Bindawa ya sake fitowa da tubalin matakan kariya wanda ya fara fitowa da shi a ɗan waƙar na biyu (ɗ. 2). A wannan ɗa na sha takwas mawaƙin ya faɗaɗa bayani kan matakan kariyar da suka haɗa da a yi haƙuri da su kome tsaurinsu domin suna cikin hanyoyin kawo lafiya. A yi haƙuri da malaman assibiti a cewar da suka yi a yi kulle kuma idan mutum ya ji wata alamar cutar korona kamar ciwon kai to kada a shiga cikin mutane don gudun a yaɗa cutar. Haka kuma a guji zuwa wuraren da aka san cutar ta ɓulla, sannan idan mutum ya sami kansa cikin wurin da cutar take to kada ya fita zuwa wurin da babu ta. Akwai bayanin cewa jama’a su sani fa wannan cuta ta korona gaskiya ce. A taƙaice dai a guji ɗaukar jita-jita cewa wai cutar ba gaskiya ba ce. Duka waɗannan bayanai suna cikin tubalin matakan kariya a layuka goma sha takwas daga layuka ashirin na wannan ɗa na 18. Sai a layuka biyu na ƙarshen wannan ɗan waƙa ne mawaƙin ya sake kawo tubalin tuba yana cewa:

 …

 Mu roƙi Allah Ubangiji

 Mu sunkuya ƙasa mu tuba

A ɗa na goma sha tara (ɗ. 19) da na ashirin (ɗ. 20) ma da waƙar ta kai ƙarshe tubalin ne na tuba mawaƙin ya saƙa ya kuma aje da shi:

 Astagfirullah astagfirullah

Astagfirullah Allah astagfirullah.

Taƙaitawa

Wannan ɓangare ne ƙarshen nazarin Waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa ta fuskokin bin diddigin zubi da tsari da kuma turke da tubalansa. Kamar sunansa ɓangaren taƙaitawa ce kan Waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa. Taƙaitawar kuwa ta ƙunshi sassa kamar haka:

Ø Bin diddigin waƙa ta Mukhtar Sani Bindawa

Ø Tarihin mawaƙi

Ø Zubi da tsari.

Ø Turken waƙa - Faɗakarwa kan Cutar Korora

Ø Tubalan Turken Faɗakarwa a waƙar:

 i. Matsalar barin noma

 ii. Matsalar barin kasuwanci

 iii. Matsalar kulle masallatai

 iv. Yin tsafta

 v. Taƙaita yin mu’amala - Kulle

 vi. Saɓon Ubangiji Allah - Zunubbai

 vii. Komawa ga Ubangiji Allah - Tuba

3.3 Waƙar Korona ta AbdusSamad Muhammad Babson

3.3.1 Bin Diddigin Waƙar

Ita ma wannan waƙa mun samo ta ne daga shafin zumunta kuma har yau Malam AbdurRahman ne ya ba mu lambar mawaƙin da ya yi wannan waƙa. Wato Malam AbdusSamad Muhammad Babson. Mun kuma buga masa waya nan take kuma ya yi maraba da mu. Ya shaida muna cewa shi ne ya ƙirƙiri waƙar. Hirar da muka sha yi da shi, kamar yadda muka sha yi da mawaƙin waƙar farko, ta tabbatar muna da shi ne ya yi waƙar.

Ita wannan waƙa ta bayyana ne cikin bidiyo. Mawaƙin ne tare da wata mai suna Zainab Hasan suke rera ta. An yi waƙar kusan watan azumin Ramadan amma ba ta fito ba sai a cikin watan, kafin hukuma ta kafa dokar kullen shiga masallaci don salla saboda kariya daga kamuwa da cutar. Layin ƙarshe na waƙar ma ya yi nuni da haka nan. Wato ana iya cewa an yi waƙar a cikin watan Maris na shekarar 2020, aka fito da ita cikin watan Afrilu ko Mayu na shekarar, bayan kimanin wata ɗaya da yin ta ke nan. Waƙar ita ce kaɗai wadda mawaƙin ya rubuta a kan cutar korona har zuwa lokacin da ake rubuta wannan littafi. AbdusSamad ya ce ya samu tunanin yin wannan waƙa lokacin da ya ji a gidajen rediyo ana rera, “Korona bairos Allah Ka tsare bayinKa”, sai nan take baiwar da Allah Ya yi masa ta yin waƙa ta zaburo, ta zaƙulo masa ya mai da wannan zuwa abin da waƙarsa ta fara da shi.

 

Ana samun wannan waƙa cikin bidiyo (hoto mai motsi da sauti) da kuma odiyo (faifan sauti), duk kuma daga ɗakin naɗiyar hoto da waƙa, sutidiyo, na mawaƙin wanda ya ba suna ‘White House’. Haka kuma akan same ta a wuraren sayar da fayafayen waƙoƙi da kuma shafukan sada zumunta da masu talla a wurare kamar gidajen sayar da man mota da makamantansu.

3.3.2Tarihin Mawaƙi

Sunan mawaƙin da ya yi wannan waƙa shi ne Malam AbdusSamad Muhammad Bauci. Ana yi masa laƙabi da Babson. Marubutan wannan littafi sun samu tuntuɓar mawaƙin ne ta waya da taimakon Malam AbdurRahman wanda kuma shi ne ya taimaka muna har muka sadu da mai waƙa ta farko, wato Malam Mukhtar Sani Bindawa na Katsina. Lokacin da muka kira AbdusSamad ta waya ya yi mana kyakkyawar maraba da bayyana jin daɗinsa da jin manufarmu kan waƙoƙinsa, musamman “Waƙar Korona”. Shi mutumin garin Bauci ne. An haife shi ranar 11 ga watan biyu na shekarar 1993 (11/2/1993). A wannan shekara ta 2020 ke nan yana da shekaru ishirin da bakwai (sk.27) na haihuwa.

AbdusSamad ya tashi a garinsa na haifuwa, Bauci a jihar Bauci. Ya yi karatun Alƙur’ani a nan garin Bauci a ƙarƙashin kulawar mahaifinsa da malaman makarantar Allo. Wannan karatu ya fara shi tun yana ɗan shekara uku da haihuwa kamar dai yadda mafi yawan ‘ya’yan Hausawa kan fara karatu. Haka kuma ya yi makarantar Islamiyya inda a nan ne ya samu yin karatun sani kamar na fiƙihu cikin littattafai irin al- Ishmawi da Risala da makamantansu.

Ta fannin makarantar Boko AbdusSamad ya fara ne daga ajin yara, wato Nursary inda ya yi aji na ɗaya har zuwa na uku a makarantar da ake ce ma Ibrahim Baƙo Primary School, Bauci. Daga nan ya shiga furamare duk a makarantar. Lokacin da ya kammala wannan makaranta sai ya shiga ƙaramar makarantar gaba da furamare, wato JSS, sannan babba ta gaba da JSS, wato SSS. Wannan karatu ya yi shi ne a JIBWIS Science Day Secondary School duk dai a garin Bauci. Bayan ya kammala wannan sai ya yi karatun Difloma (Diploma) a Kwalejin Ilmi (College of Education) ta Kandere.

AbdusSamad mawaƙi ne wanda ke yin waƙoƙin da suka shafi rayuwa musamman na faɗakarwa. Waƙarsa ta korona ita ce ta farko a kan annobar wadda ya yi kuma har zuwa lokacin rubuta wannan littafi bai yi wata ba saboda kuwa aikin ba guda ba ne, basirar ba a kan korona ɗai ta tsaya ba.

A halin yanzu Malam AbdusSamad bai wada yin aure ba amma yana kan gwagwarmayar neman na kansa, har ma ya buɗa ɗakin naɗiyar finafinai da waƙoƙi. Kamar yadda aka ambata ɗazu sunan wannan sutidiyo shi ne White House.

 

Abdussamad Muhammad (Babson)

Abdussamad Muhammad (Babson)

(Mawaƙin da ya yi waƙar Korona mai mata da miji, kuma shi ne ke cikin bidiyon waƙar. An samo hoton daga wurinsa.)

 

Zainab Hasan

Zainab Hasan

(Hoton wadda ke cikin bidiyon waƙar Korona ta AbdusSamad Muhammad. An samo hoton daga mawaƙin)

3.3.3 Sharhi kan Waƙar

3.3.4 Zubi da Tsari

Mawaƙinmu Malam AbdusSamad ya tsara wannan waƙa ta Korona Bairos cikin ɗiya goma sha ɗaya (ɗy. 11). Waɗannan ɗiya suna da layuka waɗanda yawansu da tsawonsu kan banbamta daga wani ɗa zuwa wani. Misali, ɗa na farko yana da layuka biyu a yayin da ɗa na biyu ya ƙunshi layuka huɗu. Ta fuskar tsawon layi kuwa, layin farko a ɗa na farko ya ƙunshi kalmomi biyu a yayin da layinsa na biyu yake da kalmomi huɗu. Shi kuwa ɗan da ke bin na farko, wato ɗa na biyu, ya ƙunshi layin farko mai kalmomi biyu, da layi na biyu mai kalmomi uku, su kuwa layuka na uku da na huɗu kowanensu yake da kalma ɗaya ɗaya:

1. Korona Bairos

Allah Ka tsare bayinKa

2. Korona Bairos

Aiko dafa’i lillahi

Hhhh!

Toh!

 

Kamar yadda waɗannan ɗiya suka banbamta ta fuskar tsawo da yawan kalmomi, haka suka banbamta ga yawa da tsawon gaɓoɓin kalmominsu. Waɗannan ɗiya kyawawan misalai ne na yadda zubin waƙar yake.

Tsarin da wannan waƙa ta zo da shi shi ne na ruwa-biyu wanda a wasu ɗiyansa kai tsaye kan kasance da sigar waƙar baka, sannan a wasu ɗiya kuma sai a same su sun ɗauko sigar rubutattar waƙa. Wannan zubi kuwa shi ne wanda da yawa daga cikin mawaƙan zamani masu amfani da kayan kiɗa na zamani suke tsara waƙoƙinsu da shi. A cikin wannan waƙa za a iya lura da tasirin ƙafiya na rubutattar waƙa cikin ɗiyanta. Misali, akwai amsa-amo na /na/ a ɗa na 3 da na 4 har zuwa layinsa na uku daga ƙarshensa:

3. Wai Maigida ya za a yi ke nan?

Al’amarin nan na damu na

4. Kar ki ishe ni da zancen banza

Ni kan na tushe hancina

To tashi ka ba ni abin girkawa

Ni kam yunwa na damu na

Ai in yunwa na damun ki

Ni ma yunwar na damu na

To ka je ka saya mini garin kwaki

Kai ko da zai ƙulle cikina

Wai ni kan tafiyarku ta ran nan

In ce dai ba ku je Legas ba

Lura da cewa amsa-amon /ba/ shi ne za a iya kira babban amsa-amo ko amsa-amon waje, saura kuwa su kasance na amsa-amon ciki ko ƙaramin amsa-amo.

A ɗa na 5 da na 6 kuwa amsa-amon /wa/ ne suka zo da shi, a yayin da amsa-amon /ba/ ya yi fice a ɗa na 7 zuwa na 9. A ɗa na 10 da na 11 kuwa amsa-amon /mu/ ya taka rawa.

3.3.5 Turke da Tubalansa

AbdusSamad mawaƙin da ya yi wannan waƙa ta cutar korona ya buɗa ta ne da kururuwar ambaton turkenta ne, wato ‘korona bairos’, sannan kai tsaye ya roƙi Allah da ya tsare su. To kuma ko tantama babu kan cewa tsarin nan da yake roƙon Allah Ya yi, daga wannan ‘korona bairos’ yake nufi. Saboda haka mawaƙin a tattare cikin ɗan farko ya fara gina turken waƙarsa da tubalin neman tsari. A kaikaice mawaƙin yana faɗakar da jama’a masu sauraren sa cewa ga fa wani abu nan wanda tilas a nemi magani da kariya game da shi, kuma waɗannan ga Allah Maɗaukakin Sarki kuma Mabuwayi za a roƙe su:

1. Korona Bairos

Allah Ka tsare bayinKa

Mawaƙin ya ci gaba da gina tubalin neman tsari a ɗan waƙar na biyu inda ya maimaita faɗar turkenta da cewa:

2. Korona Bairos

Aiko dafa’i lillahi

Hhhh!

Toh!

Abin nufi shi ne ‘Ya Allah Ka aiko da maganin wannan abu, wato cutar korona bairos. Layuka na uku da na huɗu a Hausance suna bayyana halin ƙaƙa-nika-yi, halin da Bindawa mai waƙar da muka gani ta farko yake cewa ‘wayyo!’. A yayin da shi mawaƙin farko ya sami bakin yin magana, shi AbdusSamad mai wannan waƙa kusan ajiyar zuciya kurum ya sami yi. Sai dai abin lura kuma game da wannan ɗan waƙar shi ne addu’ar da mawaƙin ya yi tare da ajiyar zuciyar ta yi kusa da wadda mawaƙinmu na farko ya yi, domin shi na farko cewa ya yi sun tuba shi kuma AbdusSamad roƙon magani ya yi.

‘Matar’ mawaƙin ta shigo da wani tubalin ginin turken waƙar a ɗa na uku (ɗ.3) da na huɗu (ɗ.4). Tubalin kuwa shi ne matsalar yunwa da annobar korona ta haifar:

3. Wai Maigida ya za a yi ke nan?

Al’amarin nan na damu na

 

4. Kar ki ishe ni da zancen banza

Ni kan na tushe hancina

To tashi ka ba ni abin girkawa

Ni kam yunwa na damu na

Ai in yunwa na damun ki

Ni ma yunwar na damu na

To ka je ka saya mini garin kwaki

Kai ko da zai ƙulle cikina

Wannan tubali na matsalar yunwa kamar juyi ɗaya ne na waina mai juyi biyu; a juyi ɗaya tubalin matakin kulle ne da a bayansa tubalin matsalar yunwar ne. Abin da mawaƙin ke cewa, ta ‘bakin matarsa’, shi ne annobar korona ta sa hukuma ɗaukar matakin tilasta al’umma yin kulle, su shige gida ba fitowa, abin da ya haifar da rashin abinci a gidajensu, ɗan wanda suka samo kafin shiga kullen ya ƙare. Saboda haka ‘matar’ ta koka ma ‘maigida’ tana tambayar sa mafita saboda ita dai ba wai tana ƙin son dafa abinci take yi ba. Ita ba ta ga abin da za ta dafa ba saboda ‘maigida’ ya darɓe cikin gida, ba batun yau bale na gobe bai fita ba don ya nemo abin da ‘uwargida’ za ta dafa su ci. Shi kuma ‘maigida’ ya mayar mata da faɗa da cewa kar ta dame shi da ‘batun banza’ saboda shi umurnin hukuma yake biya, ya toshe hancinsa kuma ba zai fita ba domin gudun ya kamu da cutar korona. Ita da ta ce yunwa na damun ta ai shi ma yunwar ba ta bar shi ba.

A taƙaice dai wannan mataki na kulle da hukuma ta tilasta mutane ɗauka ya saka su cikin halin ƙaƙa-nika-yi. Idan suka fita zuwa neman abinci mai yiwuwa su harbu da cutar korona. Idan kuma suka zauna cikin gida suka bi umurnin hukuma na yin kulle, to lalle yunwa za ta addabe su domin ba su fita ba balle su biɗo abinci. Gaba kura baya sayaki ke nan, ko kuma ta bakin mata Hausawa, sakin tukunya ridar murhu ke nan!

A layuka biyu na ƙarshen wannan ɗa na huɗu (ɗ.4) sai mawaƙin ya shigo da tubalin zargi wanda amma bai ci gaba da shi ba sai can a ɗa na bakwai da na tara. A ƙarshen na huɗu ɗin yake zargin ‘matarsa’ cikin tambaya da ko shin ta je birnin Legas. A kaikaice yana nuna mata cewa yana zargin kila ta ɗauko cutar korona domin a can ne cutar ta yi ƙamari fiye da ko ina a ƙasarsu:

 …

Wai ni kan tafiyarku ta ran nan

In ce dai ba ku je Legas ba

Wani abin lura game da wannan zargi shi ne tabbas mawaƙin ya yi wannan waƙa yayin da ta bayyana cewa cutar korona ta riga ta yaɗu sosai a birnin Legas. Wannan kuwa manazarcin waƙar zai gano haka ko da bai yi hira da mawaƙin ko wani da ya san lokacin da aka yi ta ba. Haka kuma waɗannan layuka kan sa mai nazari ya yi hasashen cewa wannan annoba ba ta wada ɓulla a garin da mawaƙin yake ba.

Mawaƙin ya ci gaba da gina tagwayen tubalan kulle da na matsalar yunwa ta bakin ‘Matar maigida’ inda take zayyana masa abubuwan cefane da babu su a cikin gidansu bale abincin da za su ci tare da miyar da za ta yi da cefane. Duk kuma tattare da cewa ga shi yunwa na cin su. Ita ba ta koma kan zargin da yake yi mata ba:

5. Ni da nake magana ta abinci

Kai fuskarka kake ɓoyewa

Ba mu da manja

Ba mu da magi

Ba mu da ko garin tuƙawa

A ɗa na shidda (ɗ.6) layi na ɗaya da na biyu (ɗ.6, ly.1-2) ne mawaƙinmu ya sake shigowa da tubalin roƙon Allah Maɗaukakin Sarki, watakila domin ya sanyaya zuciyar ‘matar’ a kan zargin ta da ya yi, sai dai bai yi nasara ba domin ita dai ta kafe da lalle sai dai ya fita ya nemo ko da gari ne wanda za ta yi abinci.Wato ɗa na 6 ya ƙunshi tubalai biyu ke nan: tubalin addini na roƙon Allah da kuma ci gaba da tubalin yunwa:

6. Ɗauko carbinki mu kama salati

Dug ga Ilahi ake komawa

Haba ka tashi daga kwance ka nemo gari

Ni in samu abin tuƙawa

Kamar wada ɗa na 6 ya ƙunshi tubalai biyu haka shi ma ɗa na 7 yake da tubalai biyu, tubalin fushi wanda ya mamaye ɗan gaba ɗaya da kuma sake saka tubalin zargi a layuka biyu na ƙarshen ɗan. A layuka biyu na farko mawaƙin ya yi tambaya cikin fushi wanda kuma yake yin bayyanin ci gaban tubalin kulle saboda cutar korona. A nan kuma wata ishara ce mawaƙin ya yi ta cewa wannan cuta fa ba a Legas kurum ta shiga ba, a’a ta fara yaɗuwa, kuma yayin da mawaƙin ya yi wannan waƙa.

Bayan da ya kawo wannan tubali na fushi tattare da na kulle sai kuma mawaƙin a layuka biyu na ƙarshen wannan ɗa ya kawo tubalin yin barazanar da za ta iya sa ta, ita ‘matar’, yin yaji ko ma watakila ya sake ta ɗungum:

7. Wai shin wane ne zai fita

Ni kam Anti Korona tana zagawa

Mamar Kaltume bi ni a sannu

Kin fa daɗe ba ki yo yaji ba

To amma kamar yadda muka san zaman aure na mata da miji, a ciza ne a dawo a busa, sai mawaƙin ya zo da lallashi bayan barazanar da ‘miji’ ya yi, sai ya sake shigowa da tubalin lallashi a ɗa na takwas (ɗ. 8):

8. Ba ni da ko sisi in faɗa miki

Ke ba ki san haƙurin yunwa ba

Mawaƙin ya riƙa shigowa da wannan tubali na lallashi domin mai saurare ko nazari ya fahimci yawan matsalolin da cutar korona, da matakin kulle wanda hukuma ta gindaya da jama’a suke fuskanta. Ga dai cutar, ga yunwa, ga zargin juna, sannan kuma uwa-uba, ga rashin kwanciyar hankali a gida inda aka sa su yin kulle, matsalar da ka iya raba mata da mijinta! A ra’ayin mawaƙin abin da ya dace ga magidanci shi ne ya riƙa cizawa yana kuma busawa, wato idan ya fusata a kan damuwarsa da matarsa ke yi masa na ya motsa ya nemo abinci, abin da farar gaskiya ce take faɗa masa, to ko ya yi fushin ya dawo wa gaskiyar, ya lallashe ta. Saboda haka ne mawaƙin ya fara lallashin da saka mijin cewa, /Ba ni da ko sisi in faɗa miki/, sannan ya kawo tunasarwa na a riƙa yin haƙuri kome wuya, /Ke ba ki san haƙurin yunwa ba/. Sai dai duk da wannan lallashi ta yiwu miji ya kasa shawo kan matarsa kamar yadda mawaƙin ya ci gaba da tubalin matsalar yunwa da na lallashi da ma tubalin cacar baki, hayaniya, da kuma na kulle. Waɗannan kuwa duk ɗa na 9 ne ke ɗauke da su:

9. To ko a abokanka sai ka nema

Ai na san ba za ka rasa ba

Allah na kula wannan matar

Ba ƙaunar in rayu take ba

Don Allah ka fusata ka tashi

An ce cuta ba mutuwa ba

Na san cuta ba mutuwa ba

Kuma cuta ba inwa ba

In ba gwamnati ce ta sake ba

Ko wundo ba zan leƙa ba

A wannan ɗa ‘matar’ ce mawaƙin ya ari bakinta ya sake shigowa da tubalin matsalar yunwa inda ta ba ‘mijin’ shawarar da ya tashi ya roƙo abinci daga abokansa. To sakamakon wannan shawara ce mawaƙin ya sake shigowa da tubalin fushi har ‘mijin’ ya yi zargin ta da cewa son take ya mutu. Wato a ganin mawaƙin wannan cuta da matakin kulle suna iya kai ba ga kashe aure kurum ba har ma da zargin bukatar miji ya mutu da matarsa ke iya yi.

10. Sarkin rahama kawo mana ɗauki

Kar Ka bari yunwa ta kashe mu

Dut tallafin da ake bayarwa

Mu har yau ya kasa ishe mu

11. An ɗaure akuya ba dusa

Wai sai dai mu ci ‘yar ajiyarmu

In ko ta ƙare dole a fantsama

Na rantse sai dai ta rutsa mu

Amma don Allah kowa ya bi doka

In dai ba ta hanin salla ba

Da waɗannan ɗiya na goma da na goma sha ɗaya ne mawaƙin ya rufe waƙarsa ta amfani da tubalai biyu. Na farko shi ne sake kawo tubalin addini na roƙon Allah da Ya kawo sauƙin wannan cuta da matakan da aka gindaya musu, waɗanda suka kuma jawo yunwa ga al’umma. Tubali na biyu shi ne na jan kunnen hukuma cewa fa ta sani taimakon da take bayarwa domin rage raɗaɗin yunwar da matakan da ta gindaya musu, ba fa kai gare su yake yi ba. Akwai inda yake zuwa amma dai ba gare su ba. Hasali ma waɗanda hukuma ta aza wa alhakin raba wannan tallafi zagon ƙasa suke yi mata, suna cewa mutane wai su lallaɓa da ɗan abin da suke da shi kafin a kawo tallafin! Bayan wannan jan hankali da mawaƙin ya yi wa hukuma sai ya gargaɗe ta da cewa idan fa ba ta gyara ba to lalle ƙarshen lamari shi ne mutane za su bore su taka doka kome kuwa za ta yi musu ta daɗe amma ba za su zauna cikin kulle da yunwa ba. Dalilin yin boren shi ne kome suka ajiye na ci zai ƙare ne.

A ƙarshe sai mawaƙin ya dasa aya ga waƙarsa da tubalin yin kira ga jama’a kowa da kowa ya bi dokokin da hukuma ta kafa. Amma fa ya yi togiya da cewa doka duk doka ce amma fa dokar da Allah ya kafa duk ta fi, kamar ta yin salla. Ita kam ba za su ƙin bin ta ba kome kuwa hukuma za ta yi sai ta yi! Wannan kalami kuwa ishara ce mawaƙin ke yi wa hukuma cewa duk tsananin cutar korona kuma duk dokokin da hukuma za ta kafa, to ahir! Kada ta kuskura ta taɓa dokar da Allah Ya yi umurni a bi. A nan mai nazari na iya ya goyi bayan mawaƙin saboda a fahimtar da jama’a, ai da cutar korona da su kansu jama’ar duk Allah ne ya yi su. To ina dalilin cewa a daina bauta masa? Wannan babbar matsala ce ga hukuma, musamman yadda talakkawa ke ganin hukuma ba ta hana shiga kasuwanni ba amma ta ce ta hana zuwa masallaci. Talakka ba zai fahimci wannan matsayi ba saboda da masallaci da kasuwa duk mutane suna taruwa cikinsu, kuma ma ta ɓangaren yaɗuwar cutar ai hankali ya fi yarda da cewa a kasuwa ne za a fi ganin ta.

A nan ne Babi na Uku game da sharhi kan turke da tubalai da zubi da tsari na waƙoƙin korona biyun da wannan littafi yake yin nazari ya kammala. Babi na gaba zai yi nazari ne kan salo da dabarun sarrafa salo na waƙoƙin.

Babi Na Huɗu 

4.0 Salo Da Dabarun Sarrafa Shi A Waƙoƙin

4.1 Gabatarwa

Wannan babi zai yi nazarin salon da waƙoƙin da babin da ya gabata ya nazarci turke da tubalansu. To sai dai ba kamar babin na uku ba, shi wannan zai kalli salon waƙoƙin biyu a tare ba daban dabam ba. Abin nufi shi ne ba zai dubi salon waƙa guda a ɓangare ɗaya ba sannan a ɓangare ɗaya ya dubi salon ɗaya waƙar. Zai ɗauki wani nau’i na salo ne ya zaƙulo shi cikin duka waƙoƙin biyu. Dalilin yin haka kuwa shi ne sanin cewa shi salo fage ne ɗaya tal da dukkan mawaƙa ke yin rawarsu ta isar da saƙonninsu ga masu saurare ko karanta waƙoƙinsu. A yayin da mawaƙa kan banbamta a ire-iren saƙonnin da suke tsara waƙoƙinsu a kai, ba su banbamta a salo sai dai a nau’o’in salo. Dukansu da salo ne suke amfani su isar da saƙo domin shi ne ke bayyana saƙo a fahimce shi sosai, kamar dai yadda Yahya (2001; 2016) ya kira shi da cewa shi ne asirin da ke fitowa da abin da waƙa ke nufi sosai.

4.2 Ma’anar Salo

Kafin Abdulƙadir Ɗangambo ya kawo yalwataccen bayani dangane da abin da ake kira salo sai da ya bayyana a jumlace cewa,salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo (2007: sh. 37).

Sau da ƙafa ne Abdullahi Bayero Yahya ya bi wannan ma’ana ta karantarwar malaminsa. Ga yadda tabi’in ya ce:

Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin ya isar da saƙon da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa.

 (Salo Asirin Waƙa (2016), sh.30).

 

A nazarin da marubutan wannan littafi suka yi dangane da salon da ya rinjaya cikin waƙoƙin korona na Bindawa da AbdusSamad, suna da ra’ayin cewa shi ne wanda Ɗangambo ya kira miƙaƙƙen salo (Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa: sh. 42). Haka kuma ya zo daidai da fahimtar Aminu Lawal Auta a kan waƙoƙin faɗakarwa da yake da’awar cewa:

Idan muka yi nazarin waƙoƙin faɗakarwa a jumlace za mu iya cewa mafi yawansu suna da miƙaƙƙen salo ne, wato na kai tsaye mai sauƙin ganewa. Hakan kuwa ta kasance ne saboda yanayin jigon waƙoƙin, tun da idan har mawaƙi na so ya isar da wani saƙo da yake fatan mutane su gane kuma su fa’idantu da shi, … dole ne su kasance masu sauƙin ganewa kai tsaye, wato a guji yin amfani da kalmomi masu tsauri ko wahalar fahimta da ka iya sanya fahimtar manufar ta yi wahala.

(Faɗakarwa A Rubutattun Waƙoƙin Hausa (2017): sh.153).

 

4.3 Salon Waƙoƙin Miƙaƙƙe ne

Waƙoƙin annobar korona na Bindawa da AbdusSamad duka biyu an tsara su ne cikin miƙaƙƙen salo. Saƙon da suke ƙoƙarin isarwa ga jama’a bai da wuyar fahimta saboda ba a saka tsauraran kalmomi masu wuyar fahimta ko masu ɗauke da salon dibilwa ba. Jumloli da ɗiya da layukan da waƙoƙin suka ƙunsa ba dogaye ko masu goyen jumloli ba ne.Dubi waɗannan misalai:

Bindawa:

A.

 1.Ta zo gare mu annoba

 Wayyo Korona wayyoo

Cutar Korona ta sa ba za mu je kasuwa mu je gona ba

 Masallatan Jumu’a an kulle

 Da wayona ni ban taɓa gani ba

 

 2.Zan riƙa yawaita wanke hannu

 Sannan na sanya takumkumi

 Na koma gida ba za ni fito ba

A waɗannan ɗiya, saboda babu wata sarƙaƙiya ta goyen jumloli, ma’anarsu ta fito a sarari ba tare da ka-ce-na-ce ba. Babu wasu lunge-lunge ko susar kai wanda dibilwa kan haifar kafin a fahimci saƙon da suka ƙunsa. Kururuwa ce mawaƙin ya yi wadda ta bayyana tsoron shigowar cutar korona a ƙasarsa, kuma har ta fara tilasta al’umma yin abubuwan ba su taɓa zata su yi ba a rayuwarsu.

Kamar haka waƙar AbdusSamad ta ƙunshi miƙaƙƙen salon inda ya ce,

AbdusSamad:

 A.

 1. Korona Bairos

 Allah Ka tsare bayinKa

 2. Korona Bairos

 Aiko dafa’i lillahi

 Hhhh!

 Toh!

 3. Wai Maigida ya za a yi ke nan?

 Al’amarin nan na damu na

A nan shi ma AbdusSamad tamkar kururuwa ce ya yi wadda yanke ta bayyana tsoro da tashin hankali kamar yadda Bindawa ya ji. Tsoro kan bayyanar cutar korona. Tsoron ya ƙara bayyana da mawaƙin ya haɗa da yin addu’a ga Allah da ya tsare al’ummarsa. Ya kuma haɗa tare da ajiyar zuciya, amma sai ‘uwargida’ ta zo ta ƙara dame firgitar, inda ta bayyana cewa babu ma abinci a gida kuma ga shi ‘maigida’ ya nuna ba zai fita ba saboda dokar hana fita duk da shike mawaƙin bai wada faɗi ba a waɗannan ɗiya. Saboda kaifin ma’anar waɗannan ɗiyan waƙar sai zuciyar mai saurare kai tsaye ta fahimci saƙon da mawaƙin ke son ya isar: annobar korona ta auko cikin ƙasa kuma babu mafita sai roƙon Allah Mai kowa Mai kome Mai magani don Ya kawo tsari ga al’umma.Duk wannan fahimta a dalilin kasancewar salon waƙar miƙaƙƙe ne kamar na waƙar Bindawa.

A wani misali daga waƙoƙin biyu ga abin da suke cewa:

Bindawa:

B.

 3. Dattijo!

4. Na’am ya aka yi jikanlena

5. Takunkumi da wanke hannu

 Su kaɗai ba za su sa komai ba

 Ba za su raba ka da annoba ba

6. Miye maganinta jikokina?

7. Saɓon Ubangiji zunuban da muke

Sunka ja mana

8. Wayyoo!

9. Cutar korona mashaƙo

 Rashin kumya muka wa Allah

Kuma ba za ta kau ba

Sai mun tuba

 

AbdusSamad:

B.

 3. Wai Maigida ya za a yi ke nan?

 Al’amarin nan na damu na

 4. Kar ki ishe ni da zancen banza

 Ni kan na tushe hancina

 To tashi ka ba ni abin girkawa

 Ni kam yunwa na damu na

 Ai in yunwa na damun ki

 Ni ma yunwar na damu na

 To ka je ka saya mini garin kwaki

 Kai ko da zai ƙulle cikina

 Wai ni kan tafiyarku ta ran nan

 In ce dai ba ku je Legas ba

A haka cikin miƙaƙƙen salo ne waƙoƙin biyu suka kasance har zuwa ƙarshensu.

4.3.1. Dabarun Sarrafawa

4.3.1.1. Hira

Fitacciyar dabarar sarrafawa da waɗannan waƙoƙi suka ƙunsa ita ce hira. Wannan salo ne da mawaƙi ke kawo maganganun mutane biyu ko fiye cikin sigar tattaunawa ko canza yawu. Yahya (2016) ya bayyana wannan salo kamar haka:

Idan baitocin waƙa suka ƙunshi muryar mai magana fiye da ɗaya, wato, mawaƙi ya ƙaddarta da shi da wani ne ke magana, ko kuwa wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna magana, to a fagen nazarin waƙa sai a ce mawaƙi ya yi amfani da salon hira a cikin waƙarsa.

(Salo Asirin Waƙa: sh. 137).

 

To a waɗannan waƙoƙi biyu na korona na Bindawa da AbdusSamad salon hira ne ya mamaye kusan dukan ɗiyan da suka ƙunsa. Da farko dai abin lura shi ne a kowace waƙa masu furta ta biyu ne ko fiye. A Waƙar Korona ta Bindawa ‘yan mata (jikoki) biyu ne da wani dattijo (kaka) ke furta ɗiyan waƙar, ko dai su ‘yan matan su fara yin magana sai dattijon ya mayar musu da jawabi, ko kuma shi ya yi su mayar masa da martani. Ta haka ne salon hira ya wanzu. Kazalika, a Waƙar Korona ta AbdusSamad salon ya ƙullu ne tsakanin mutane biyu, ‘miji’ da ‘mata’. ‘Mata’ ta yi magana sai ‘miji’ ya mai da martani ko kuma shi ya fara ita ta mai da martani.

 

Tun daga ɗa na uku har zuwa ɗa na sha takwas a waƙar Bindawa salon ne na hira, sannan a ɗiya biyu na ƙarshe, ɗy. 19-20, dukan masu muryoyin ne suka furta su. A waƙar AbdusSamad kuwa nan ma wannan salo ya fara daga ɗa na uku sai a ɗa na tara ne ya tuƙe, a yayin da ɗa na goma da na goma sha ɗaya dukan masu muryoyin biyu ne suka furta su, duk da yake ɗaya (miji) ya fi ɗayar (mata) magana da yawa.

 

4.3.1.2. Gangara

Gangara, in ji Ɗangambo (2007), a matsayin salo, ana bayyana shi kamar haka:

Ita gangara tana aukuwa ne cikin baiti inda za a faro wata magana a cikin wani ɗango, ba za a ƙare ta ba sai a ɗango na gaba.

(Ɗaurayar Gadon…:sh. 51)

 

Za a fahimci cewa ɗaya daga cikin amfanin gangara cikin waƙa shi ne riƙe zaren tunanin mai saurare ko karatun waƙar domin ya fahimci saƙon da mawaƙi yake son ya isar masa. Wato mawaƙin yana sane da cewa saƙonsa mai tsawo ne kuma mai muhimmanci, layi guda ba zai wadatar da shi ba saboda sauran bukatu ko ƙa’idojin saƙa waƙa. A taƙaice muna iya cewa gangara wata lalurar waƙa ce a lulluɓe cikin saƙar ɗa ko baitin waƙa.

 

Mawaƙanmu sun ci moriyar wannan salo a ɗiyan waƙoƙinsu. Alal misali, Bindawa ya yi haka a ɗa na biyar na waƙarsa:

5. Takunkumi da wanke hannu

Su kaɗai ba za su sa komai ba

Ba za su raba ka da annoba ba

 

Ma’anar wannan ɗa ba ta bayyana a layi na farko sai an haɗa layin da na biyu. Wato yana cewa,“ka sani fa don ka sa takunkumi, ka kuma wanke hannuwanka babu wata fa’ida da za ta zo maka”. Mawaƙin ya ma goya wata jumla a wannan ɗa wadda ke iya zama cikon gangarar ko da an cire cikonta na fari, /Su kaɗai ba za su sa komai ba/. Wato sai ɗan ya kasance a haka:

6. Takunkumi da wanke hannu

Ba za su raba ka da annoba ba

 

ba tare da wani targaɗe ba.

Mawaƙin ya sake amfani da gangara a gaba ɗayan ɗa na tara da layi na biyu zuwa na uku, da layi na huɗu zuwa rabin layi na biyar, da kuma rabi na ƙarshen layin zuwa layi na bakwai, duk a ɗa na 10. Haka kuma akwai wani dogon salon na gangara a ɗa na 17 tun daga layinsa na farko har zuwa layi na takwas. Shi ma ɗa na 18 wanda ya soma da /Matakan da gwamnati ke ɗauka/ yana ƙunshe da gangara har guda biyar. Haka kuwa bai rasa nasaba da jeranta abubuwan da mawaƙin ke bukatar mai saurare ya naƙalta. Waɗannan abubuwa kuwa sune, da yin haƙuri da matakan da hukuma ke gindaya wa jama’a, da tsare bin umurnin ma’aikatan lafiya, da rashin shiga wuraren da cutar korona ta ɓulla, da ma rashin fita daga garin da cutar take idan mutum yana cikin garin da kuma nisantar yin zargin cewa wani ya ƙirƙiro cutar. Ɗa na 20 ma yana da gangara biyu a layuka biyu na farko da kuma layi na huɗu zuwa na biyar.

 

A waƙar AbdusSamad ma mawaƙin ya yi amfani da wannan salo na gangara. A ɗa na 4 inda ‘mata’ ta faɗa wa ‘miji’ cewa ita fa yunwa na damunta sai mijin ya mayar mata da martani:

4. …

 Ai in yunwa na damun ki

 Ni ma yunwar na damu na

 …

A ƙarshen ɗan ya ƙara amfani da gangara inda ‘miji’ ya tuhumi ‘mata’ da kila ta harbu da cutar a wata tafiya da ta yi da ƙawayenta da kila ta je birnin Legas inda cutar ta ɓulla:

 …

 Wai ni kan tafiyarku ta ran nan

 In ce dai ba ku je Legas ba

 

Haka nan kuma mawaƙin ya sake yin amfani da gangara a ɗa na 5 har sau biyu: a layi na ɗaya zuwa na biyu, da kuma layi na huɗu zuwa na biyar:

 5.Ni da nake magana ta abinci

Kai fuskarka kake ɓoyewa

Ba mu da manja

Ba mu da magi

Ba mu da ko garin tuƙawa

Ya kamata a lura da cewa salon gangara da ke a nan ya shafi na zaren tunani ko ma’ana ba wai ta jumla ba.

Haka kuma a lura da cewa shi ma wannan ɗa kamar ɗa na 5 ne na waƙar Bindawa ta fuskar ana iya a cire wani layi a maye gurbinsa da wani na kusa da shi amma duk da haka a samu salon gangara. Abin nufi shi ne a nan ana iya a cire, /Ba mu da magi/ a maye gurbinsa da layi na uku /Ba mu da manja/ kamar haka:

 

 Ba mu da manja

 Ba mu da ko garin tuƙawa

 

Sauran wuraren da wannan salo yake sun haɗa da layi na uku zuwa na huɗu, da layi na tara zuwa na goma duk a ɗa na 9, da kuma ɗa na 10 a layi na uku zuwa na huɗu.

 

4.3.1.3. Karin Magana

Ɗangambo (2007) ya ja hankalin manazarta waƙoƙin Hausa ga yadda mawaƙa kan yi “amfani da al’adu da tatsuniyoyi, da karin magana” cikin waƙoƙinsu. Ya ce manufa ita ce don “a ga muhimmancinsu, da tasirinsu a cikin waƙar”(Ɗaurayar Gadon…: sh. 53).

 

Ta la’akari da wannan ne Yahya (2016) yake cewa:

 

Mawaƙi kan kawo karin magana cikin waƙarsa saboda wasu dalilai da suka haɗa da:

a) yin ishara

b) ƙarin bayani

c) nuna ƙwarewa ga harshen Hausa

d) adana karin Magana da sauransu.

(Salo Asirin Waƙa: sh.120).

To saboda ire-iren waɗannan manufofi ne Bindawa da AbdusSamad suka yi amfani da karin magana cikin waƙoƙinsu. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, a lokacin da AbdusSamad ya yi amfani da karin magana kai tsaye, shi Bindawa amfani ya yi da maganar magabata masu daraja ga Hausawa Musulmi. A nan muna nufin maganar hikimar nan ta Larabci a ɗa na 14:

14. Maa nazzalul balaa’u illaa bi ma’asiyaa

 Wa maa rufi’a illaa bi taubaa

Wannan maganar hikima ce wadda halifa na huɗu a Daular Musulunci, wato Ali ibn Abi Ɗalibi (Allah Shi y arda da shi, amin), ya yi. Shi kuwa Ali ɗan uwan Manzon Allah (S.A.W.) ne kuma surukinsa, domin ya auri Nana Fatima (Allah Shi yarda da ita, amin), ‘yar Manzon Allah (S.A.W.),. Ɗa na 16 ne ya fassara ma’anar wannan magana ta Larabci cikin Hausa:

16. Saɓo ke saukar da bala’i

 Bai tafiya sai da istigifari

 Astagfirullah astagfirullah

 Astagfirullah Allah astagfirullah.

Da za a fassara Larabcin cikin Hausa kalma da kalma sai a ce:

 Bala’i ba ya sauka face sai da saɓo

Kuma ba za a ɗauke (kau da) shi ba face sai da tuba

To amma shi mawaƙinmu na biyu, AbdusSamad ya yi amfani da maganar Hausawa ta gargajiya, wato karin magana a ɗa na 9:

9.To ko a abokanka sai ka nema

 Ai na san ba za ka rasa ba

 Allah na kula wannan matar

 Ba ƙaunar in rayu take ba

 Don Allah ka fusata ka tashi

 An ce cuta ba mutuwa ba

 Na san cuta ba mutuwa ba

 Kuma cuta ba inwa ba

 In ba gwamnati ce ta sake ba

 Ko wundo ba zan leƙa ba

Abin da mawaƙin ke nufi /cuta ba mutuwa ba/, ta bakin uwargida, shi ne tun da dai sanin kowane Musulmi ne cewa ba lalle ne sai cuta ce ke kawo mutuwa ba, saboda haka maigida ya tashi ya je ya samo abin da za su ci. Haka kuma a ta bakin maigida sai mawaƙin ya ce /cuta ba inwa ba/, wato duk da shike ba lalle ne cuta ta haifar da mutuwa ba amma kuma ai kowa ya san da cewa cuta ba ta haifar da lafiya da hutu.

Haka nan kuma mawaƙin ya sake kawo karin magana a ɗa na11, wato na ƙarshe:

 11.An ɗaure akuya ba dusa

Wai sai dai mu ci ‘yar ajiyarmu

In ko ta ƙare dole a fantsama

Na rantse sai dai ta rutsa mu

Amma don Allah kowa ya bi doka

In dai ba ta hanin salla ba

A wannan wuri mawaƙin yana nufin muddin aka tsare mutum a wuri ɗaya, kamar yadda hukuma ta gindaya dokar kulle, ba tare da abincin da zai ci ko ya fita ya nemo abincin ba, to kuwa ko shakka babu cewa an jawo masa mutuwa ne, kul ba daɗe kul ba jima!

4.3.1.4. Tambaya

A mafi yawam lokuta Bahaushe a maganarsa ta yau da kullum yakan yi amfani da tambaya don neman bayani ko don ya ƙarfafa zancen da yake yi. Wato wani lokaci don ya samu amsa daga abokin maganarsa, ko kuma wani lokaci ba ya bukatar amsar domin da shi da abokin nasa duk sun san amsar, illa kurum ya yi tambayar ne domin ya jaddada saƙon da yake son ya isar. Tambaya akan yi ta don neman amsa ko don a ƙarfafa saƙo.

Su ma mawaƙa da sauran wasu maƙirƙira adabi a Hausa kamar na gatana, tatsuniya, da na zube da na wasan kwaikwayo, sukan yi amfani da salon tambaya cikin ƙirƙirensu. Su mawaƙa ko bayan tambaya wadda yake ba da amsarta cikin waƙarsa, da wadda ba sai ya kawo amsarta ba don ya san mai sauraren ta ya sani, akwai kuma wadda yakan sa mala, wato bai ba da amsarta ba kuma yana sane da cewa ba lalle mai saurare ya san amsar ba. Wato dai manufarsa masu saurare su yi ta laluben amsar tambayarsa.

Irin wannan tambaya ta uku da mawaƙi kan sa a mala domin masu saurare su wasa ƙwaƙwalwarsu, ba ita ce ke cikin waƙoƙinmu biyu da ake nazari ba. Mai karatu yana iya ya dubi waƙar Wazirin Sakkwato Muhammadu Buhari (h.1838; r. 1910) wadda ake kira, ‘INA DA GARIBI’ wadda Yahya (2016: 8-10) ya yi magana a game da ita.

Bindawa a waƙarsa ya yi amfani da salon tambaya har sau uku kuma ya kawo amsoshinsu. A ɗa na 4 ya ce, /Na’am ya aka yi jikanlena/ lokacin da a ta bakin ‘jikanya’ ta kira ‘kaka(nta)’. Haka kuma mawaƙin a ta bakin ‘kaka’ ya sake amfanin da salon a ɗa na 6 inda ya ce, /Meye maganinta jikokina/. Wannan kuwa tambaya ce ‘kaka’ ya yi wa ‘jikoki’ lokacin da suka faɗa masa cewa takunkumin da zai sa da wanke hannuwa da zai riƙa yi, duk ba za su hana mutum ya kamu da cutar korona ba. Salon tambaya na uku da mawaƙin ya kawo, shi ma a ta bakin ‘kaka’, ya zo a ɗa na 15 bayan ‘jikanya’ ta buga Larabci alhali shi kuwa ‘kaka’ bai fahimta ba. Saboda haka sai ya tambayi ‘jikanya’ guda, /Me ta ce cikin Larabci/ kuma amsar ta zo a ɗa mai bi ma tambayar, wato ɗa na16.

Shi ma AbdusSamad a waƙarsa ya yi amfani da salon tambaya a wurare uku. A wuri na farko, ɗa na 3, ‘mata’ ce take tambayar ‘miji’ na wace mafita ce za su bi, /Wai Maigida ya za a yi ke nan/ saboda matsalar da suke ciki, ‘al’amarin nan’ ya dame ta har ba ta san yadda za su yi ba. Amsar tambayarta kuwa ba daɗi ne da ita ba don ‘miji’da fushi ya taso mata a ɗa na 4, /Kar ki ishe ni da zancen banza…./. Wuri na biyu kuwa shi ne a layi na ƙarshen wannan ɗa na 4, har yanzu dai aron bakin ‘miji’ ne mawaƙin ya yi. Ya ce, /In ce dai ba ku je Legas ba/. A nan salon ƙunshe yake a nasarce da amsar da mai tambaya yake bukatar ya samu, wato, “A’a ba mu je Legas ba”. Sai dai ita uwargida da zargi ne ta ba maigida amsar tambayarsa ta yi. A ɗa na 7 ne wurin da salon na tambaya ya bayyana a sakamakon zargin da uwargida ta yi a can baya. Maigida ne mawaƙin ya ari bakinsa ya kawo salon da, /Wai shin wane ne zai fita/ A nan ma mawaƙin bai kawo amsar tambayar ba sai dai a dunƙule nasarce. Wato, “Babu mai fita”, don cutar korona akwai ta a kowane wuri mutum zai je.

Sauran wasu nau’o’in salo da ake samu cikin waɗannan waƙoƙi biyu na Bindawa da AbdusSamad sun haɗa da salon kawo nassin Alƙur’ani (waƙar Bindawa: ɗa na 11), ƙullin jimla, (wƙ. Bindawa: ɗa na17, ly.10; wƙ. AbdusSamad: ɗa na 5, ly. 4, 5), da kuma salon togiya (wƙ. AbdusSamad: ɗa na 11, ly.6.).

  

Babi Na Biyar

 

5.0 Ƙyallun Nazarin Salo A Waƙar Cikin Bidiyo

 

5.1 Gabatarwa

A babi na uku da na huɗu an yi nazarin waƙoƙin biyu musamman ta fuskar manyan gimshiƙan nazarin waƙa, jigo da salo, da Ɗangambo (2007) ya shimfiɗa. Tattare da wannan an kuma yi amfani da tsattsafin da ɗaliban Ɗangambo (Gusau: 2003, 2014; da Yahya: 2001,2016) suka yi a kan waɗannan gimshiƙai. Manufar wannan babi na biyar ita ce yin tsokaci a kan wani nau’in salo da muke ganin ya kunno kai a dalilin saka waƙoƙin Hausa musamman na baka da ruwa-biyu cikin na’urar zamani, wato bidiyo na sitidiyo. A kan haka ne muka kira wannan tsokaci da “Ƙyallun Nazarin Salo A Waƙar Cikin Bidiyo”. Wato dai nazarin kamar ƙwaron nan ne mai nuna kansa ta ƙyallaro haske, da Hausawa kan kira ‘ƙyallun belun’. A tunanin marubutan wannan littafi, yadda wannan ƙwaro ke ƙyallaro haske haka wannan salo yake yi yana bukatar manazarta salon waƙa su fito da shi sosai a riƙa yin nazari a kansa.Wannan nazari ya tuzgo ne a sakamakon ganin yanzu mawaƙan Hausa musamman matasa sukan tsara waƙoƙinsu da niyyar saka su cikin bidiyo. Haka kuma manazarta waƙoƙin Hausa kamar Sa’idu Muhammad Gusau (Waƙar Baka Bahaushiya: 2014) sun saka waɗannan waƙoƙi cikin jerin waƙoƙin Hausa. Wannan nau’in salo hasko kansa ne yake yi ga manazarta waƙoƙin Hausa domin ya samu wurin zama.

Abin la’akari a nan shi ne ya kamata mai nazari ya san da cewa akwai ayyukan da suka danganci wasan kwaikwayo da ake aiwatarwa a dandamali da kuma ayyuka a kan fina-finai. Waɗannan masu taimakawa ne a wannan fage. Sai dai kuma wajibi ne a koyaushe ɗabi’u da al’adun Hausawa su kasance jagora ga mai nazarin salon waƙaoƙin Hausa na cikin bidiyo.

5.2 Sajewar Zaren Tunani da Aiwatarwa a Rerawa

A wannan salo ana nufin yadda tunanin masu rera waƙar da yadda suka aiwatar da hakan cikin bidiyon suka saje da juna. Wato mu da muke kallon bidiyon sai mu haƙiƙance cewa tunani guda ne ke isar da saƙon da ke cikin waƙar, yadda muka kalli bidiyon ya kasance ko da mawaƙin ne ke rera waƙar haka nan ne zai yi. Idan muka kalli waƙar Bindawa za mu ga dattijo yana mitar matsalolin da ya shiga da shi da al’ummarsa, kwatsam sai ya ji an kira shi, ya kuma gane muryar jikanyarsa ce sai ya karɓa da sauri ya tambaye ta me ke faruwa. Abin da mai kallo da sauraren waƙar zai nasarta a rai shi ne ‘dattijo’ zai ɗauka cewa wata ƙarin matsala ce jikanyarsa ta kawo a kan matsalolin da ya damu da su kuma yake yin mita a kansu.Daga jawabin da yarinya da ita da ‘yar uwarta suka yi wa dattijo sai ran mai kallo da saurare ya ji kamar zaren tunanin masu rerawar ya ɗinke ya zama zare guda. Haka kuwa zai kasance ne saboda ƙura ido da dubin da dattijo ya yi ga yarinya da kuma girgiza hannuwa da ‘yan matan suka yi yayin da suke jaddada rashin amfanin matakan da dattijo ya ce zai ɗauka don kariya daga cutar korona.

Haka nan kuma lokacin da dattijo ya ji abin da ‘yan matan suka ce game da rashin amfanin matakan da ya zana zai ɗauka,sai ya sunkuyar da kansa ya tambaye su mene ne mafita, su kuma nan take suka cira hannuwa sama suka ba shi amsa. Shi kuma ya ce, /wayyo/, amma wannan kalma ya ja furta ta sosai. To da sunkuya kai, da jan furucin kalmar ‘wayyo’ da cira hannuwa duk suna ƙara saje zaren tunani da rerawar waƙar da masu rerawa ke yi.

 

Duk wannan motsin gaɓoɓin jiki na ido da harshe ko baki da hannuwa, suna cikin ɗabi’u da al’adun Bahaushe wajen sadar da saƙo ko musayar magana.

 2. Zan riƙa yawaita wanke hannu

 Sannan na sanya takumkumi

 Na koma gida ba za ni fito ba

3. Dattijo!

4. Na’am ya aka yi jikanlena

 5.Takunkumi da wanke hannu

 Su kaɗai ba za su sa komai ba

 Ba za su raba ka da annoba ba

 6.Miye maganinta jikokina?

 7.Saɓon Ubangiji zunuban da muke

 Sunka ja mana

 8.Wayyoo!

Kamar haka ne ke faruwa a waƙar AbdusSamad a sa-in-sar da ta gudana tsakanin ‘mata’ da ‘miji’ a ɗa na 8 zuwa na 9:

8.Ba ni da ko sisi in faɗa miki
Ke ba ki san haƙurin yunwa ba

 9.To ko a abokanka sai ka nema
  Ai na san ba za ka rasa ba

 Allah na kula wannan matar

 Ba ƙaunar in rayu take ba

 Don Allah ka fusata ka tashi

 An ce cuta ba mutuwa ba

 Na san cuta ba mutuwa ba

 Kuma cuta ba inwa ba

 In ba gwamnati ce ta sake ba

 Ko wundo ba zan leƙa ba

Za a lura da sa-in-sar da uwargida da maigida suke yi tare da yadda uwargida ke motsa hannuwanta.Haka nan kuma akwai nunin da maigida yake yi mata, da kuma yarɓe hannuwansu da suke yi domin jaddada abin da suke faɗa. Duk wannan amfani da gaɓoɓin jiki ne da ke taimakawa ga sajewar rerawar da mutanen biyu ke yi.

5.3 Amfani da Idon Zuci

Amfani da idon zuci na nufin mutum ya nasarta kasancewa wani mutum daban ko wani abu da ba shi ne ba, ko kuma mutum ya nasarta abin da kalma ko furuci ke nufi cikin aiwatarwarsa. Wato dai mutum ya kasance wani mutum na daban, ya sa ba rigar wani ba kurum, a’a har ma da zuciyar wanin, da tunanin wanin, da aiwatarwar wanin. Wannan shi ne cikakken kwaikwayo kuma hakan ne ake son mai rera waƙar da ba shi ne ya ƙirƙire ta ba ya yi, ko kuma ko da shi ne ya ƙirƙire ta, to ba shi ne wanda ya ƙirƙira ta ba sai dai wanda saƙon waƙar ke magana a kai.

AbdusSamad a waƙarsa ta korona ya yi amfani da wannan nau’in salon amfani da idon zuci a kusan dukan waƙar. Misali, a farkonta ana iya ganin matar da take a matsayin matar maigida, yadda ta yi tsaye tana saurare da dubin ‘maigida’ a hankaɗe, wato cikin takaici kafin ta buɗa bakinta. Irin wannan tsayi da ma kalamin da ta furta duk yanayi ne na matar maigida a al’adun Hausawa. Duk Bahaushen da ya kalli wannan sashe na bidiyo zai yarda da cewa haka ne matar Bahaushe kan yi, ba wai don wani ɓacin rai da kan zama na rabuwar mata da miji ba, a’a, sai don ta isar da wani muhimmin saƙo da ke bukatar ɗaukar matakin gaggawa. Ɗan waƙar da matar ta yi amfani da idon zucin shi ne:

 3. Wai Maigida ya za a yi ke nan?

 Al’amarin nan na damu na

 

Shi ma ‘maigida’, wanda kuma a haƙiƙani mawaƙin da ya yi waƙar ne, ta amfani da salon idon zuci ne ya mayar wa ‘uwargida’ da martani. Mai kallo da sauraren bidiyon, in dai Bahaushe ne, zai haƙiƙance cewa haka ne magidanci Bahaushe, a irin yanayin da ake ciki, zai mai da martani ga uwargidan da ta yi masa irin maganar can. A matsayin ne mawaƙin/maigida ya taso da fushi, ya nuni ‘uwargida’, ya furta kalamin da yake zaton za ta bar damuwar sa. A madadin ‘uwargida’ ta yi shiru kamar yadda Hausawa ke zato a wata fuska, sai ta ci gaba da irin maganar da ta yi da farko kuma tare da motsa hannuwa don nuna damuwa kamar kuma yadda Hausawa kan yi zato a ɗaya fuskar. Haka nan kuma ‘maigida’ ya yarɓe hannuwansa domin ya jaddada wa ‘uwargida’ matsayinsa, kamar yadda ita ma ta taɓa cikinta don ta jaddada bayyana saƙon jin abin da cikinta zai samu sanadin cin garin rogo. Ta kuma yi amfani da hannuwanta domin ta lissafa abubuwan da gidansu ya rasa. Duk wannan motsi da gaɓoɓi na ‘maigida’ da ‘uwargida’ suna cikin abin da amfani da idon zuci ke haifarwa. Ga dai ɗiyan da amfani da idon zuci ɗin yake tattare da su:

 4. Kar ki ishe ni da zancen banza

Ni kan na tushe hancina

To tashi ka ba ni abin girkawa

Ni kam yunwa na damu na

Ai in yunwa na damun ki

Ni ma yunwar na damu na

To ka je ka saya mini garin kwaki

Kai ko da zai ƙulle cikina

Wai ni kan tafiyarku ta ran nan

In ce dai ba ku je Legas ba

 5.Ni da nake magana ta abinci

Kai fuskarka kake ɓoyewa

Ba mu da manja

Ba mu da magi

Ba mu da ko garin tuƙawa

A ɗiya na 10 da na 11 wanda shi ne na ƙarshen waƙar, mawaƙin ya sa salon amfani da idon zuci daban da na maigida da uwargida. A wannan karo mawaƙin shi ne Bahaushe na gidi, ɗaya daga cikin al’umarsa ta Hausa. Ya yi tsaye ya miƙe hannuwansa sama yana rera ɗan waƙar wanda addu’a yake ɗauke da ita. Wannan amfani da idon zuci ya bayyana ne ta irin tsayi da miƙe hannuwa da tayar da kai sama da yin addu’a tamkar yadda Bahaushe Musulmi kan yi idan yana cikin matsala. Ganin mawaƙin cikin wannan yanayi zai gamsar da mai kallo da sauraren waƙar cewa lalle mawaƙin ya matsu.

 

Daga wannan yanayi sai kuma mawaƙin ya sake amfani da idon zuci na daban, wanda ya fice daga na addu’a ya shiga na yin kira ga al’ummarsa na su bi dokokin da hukuma ta kafa na matakan kariya. Haka kuma sai ya liƙa wani amfani da idon zuci mai nuna bijirewa. Abubuwan da ke bayyana duk wannan amfani da idon zuci har kashi biyu su ne, yin nuni zuwa ga mutane amma da hannuwa ƙasa-ƙasa kuma a jicce don nuna lalama. Haka ma buɗe ido da taɓa goshi yayin furta kalamin bijirewa ga hukuma muddin ta yi yunƙurin saka dokar hana yin salla suna tattare da amfani da idon zuci. Amfani da waɗannan nau’o’in idon zuci sukan sa Bahaushe kuma Musulmi, a farko ya ji ya yarda da kiran da mawaƙi ke yi, sannan kuma ya aminta da bijire wa hukuma wadda mawaƙin ya sha alwashin yi.Ga ɗiyan waƙar da suka ƙunshi amfani da idon zucin:

10.Sarkin rahama kawo mana ɗauki

Kar Ka bari yunwa ta kashe mu

Dut tallafin da ake bayarwa

Mu har yau ya kasa ishe mu

11.An ɗaure akuya ba dusa

 Wai sai dai mu ci ‘yar ajiyarmu

In ko ta ƙare dole a fantsama

Na rantse sai dai ta rutsa mu

Amma don Allah kowa ya bi doka

In dai ba ta hanin salla ba

A waƙar Bindawa yayin da jikokin ‘Dattijo’ suke kawo ayar Alƙur’ani don su kafa masa hujjar cewa saɓon da mutane ke yi shi ne musabbabin cutar korona, dattijon ya yi amfani da idon zuci. Wannan kuwa ya bayyana a dalilin yin shiru da ƙura ido da ya yi ga jikokin, da girgiza kansa da ya yi yayin da jikanyar ta take karanto ayar, girgiza don yarda da abin da ayar ke cewa. Duk waɗannan ayyuka na gaɓoɓin jikinsa kan tabbatar wa mai saurare da kallo wanda ya san ɗabi’o’i da al’adun Bahaushe cewa hakan ne Bahaushe Musulmi kan yi idan aka karanta masa ayar Alƙur’ani, musamman domin kafa hujja.

Su ma ‘jikokin’ ‘Dattijo’ sun yi amfani da idon zuci ta hanyar girgiza hannuwansu, da ɗaga su sama da kuma karanta ayar Alƙur’ani a yadda take cikin Larabci, da kuma yanayin da mai karatun take riƙe da Alƙur’ani. Yin duk wannan motsa gaɓoɓin jiki da natsuwa suna cikin yanayin da Bahaushe kan shiga idan yana kafa hujja da Alƙur’ani ga abokin maganarsa. Kalli sashen bidiyon da ya nuna abubuwan da aka ambata:

10. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un

 Saɓon Ubangiji zunuban da muke

 Sunka ja mana

 Cutar korona mashaƙo

 Su suka ja muna, hangenmu

 Ba mafita gare mu

 Sai mun tuba

 Allah Ubangiji mun tuba

11.Ƙalallahu Ta’ala fi Ƙuranil Karimi Mai girma

(Surat Ash-Shura 42, aya ta 30)

 12. Allah Ubangiji Ya ce

 Da mun ga masifa annoba

 Da hannunmu mu muka jawo ta

 Amma kuma Allah na afuwa

 Da mun koma gare shi mun tuba

An kaurara rubutun aka kuma yi shi gicceye don nuna farkon inda mai kallo zai mai da hankali.

Wannan natsuwa da ƙanƙan da kai da mai kallo da saurare ya kalla sun saɓa da yadda mawaƙin ya faro waƙar. Ya faro ta ne da ‘Dattijo’ yana cikin tsoro da jin mamaki. Idon zucin da ‘Dattijo’ ya yi amfani da shi ke nan. Tsoro da mamaki, a yayin da ‘jikokinsa’ su ko suka yi amfani da idon zuci na mai amanna da abin da yake faɗi. Shi ya noce kai, ya yi ‘wayyo’, sannan ya girgiza hannu bayan ya yi nuni da jihar da masallaci yake, su kuwa ‘jikoki’ sun girgiza hannuwawan ‘faufau’, da kuma buɗa tafukan hannuwansu don nuni zuwa ga mafitar da ke zamewa madadin mitar da ‘Dattijo’ yake yi. Duk wannan motsin gaɓoɓi na ‘Dattijo’ da ‘jikoki’ suna cikin abubuwan da kan sa mai kallo Bahaushe kuma Musulmi ya ƙara kasancewa tare da mawaƙin cikin idon zuci iri ɗaya.Kalli ɗiyan waƙar:

1. Ta zo gare mu annoba

 Wayyo Korona wayyoo

Cutar Korona ta sa ba za mu je kasuwa mu je gona ba

 Masallatan Jumu’a an kulle

 Da wayona ni ban taɓa gani ba

 2.Zan riƙa yawaita wanke hannu

 Sannan na sanya takumkumi

 Na koma gida ba za ni fito ba

3.Dattijo!

4. Na’am ya aka yi jikanlena

5. Takunkumi da wanke hannu

 Su kaɗai ba za su sa komai ba

 Ba za su raba ka da annoba ba

 6. Miye maganinta jikokina?

 7. Saɓon Ubangiji zunuban da muke

 Sunka ja mana

 8. Wayyoo!

9. Cutar korona mashaƙo

 Rashin kumya muka wa Allah

 Kuma ba za ta kau ba

 Sai mun tuba

5.4 Ankarar Zuci

Abin da ake nufi da “ankarar zuci” a nan shi ne zuciya da hankalin mutum su kasance a falke da abubuwan da ke a kewaye da shi ta yadda zai iya mai da martani farat ɗaya nan take. Misali, mutum biyu ne taurari cikin wasan kwaikwayo, magana da aiwatarwar ɗaya su kasance sun daidaita da na mutum na farko. Wato martanin ɗaya ya zo kamar sakamakon tasirin furuci ko aikin ɗaya ne a haƙiƙani ba shiri ba, babu gargada ko inda-inda. Wannan shi ne Uta Hagen ke nuni a littafinta wurin da ta ce:

An alert mind is an actor’s prerequisite. It must be exercised as continuosly and with the same discipline as the body. …According to the dictionary, to be intelligent means “to reveal good judgement and sound thought, to be alert, to be quick-witted.” It also means to comprehend information, to be successful in dealing with new situations, and to apply knowledge so as to cope with one’s surroundings. On the other hand, to be intellectual is to be “chiefly guided by the intellect rather than by emotion or experience.” …, it is important that the artist leave intellectual concepts, theories, and conclusions to scholars, scientists, critics, or to discussions about other matters than the work on his roles. Treaties should be confined to libraries, lecture halls and parlors, not brought to the theatre.(bold emphasis is ours).

 (Hagen, U, A Challenge for the Actor, p.106 ).

Fassara:

Bukatar tilas ce ga ɗan wasan kwaikwayo zuciyarsa ta kasance ankare. Wato dole ne a koyaushe tana a faɗake kuma jere da juna da jiki suna aiki tare. …A cikin Ƙamus an bayyana zamowa fasihi (mai basira/kai) da “ iya nuna yanke kyakkyawan hukumci da yin ingantaccen tunani, a kasance a ankare, a kasance mai kaifin basira.” Haka nan kuma ana nufin fahimtar bayani, ko a yi nasara ga tunkarar sabon yanayi, da kuma iya amfani da sanin da mutum yake da domin iyawa da yanayin da ke kewaye da shi. To amma a waje ɗaya, zama masani na nufin “ a kasance wanda galibi basira ke yi wa jagora maimakon sosuwar zuciyarsa ko ɗanɗanonsa.”…, abu ne da yake da muhimmanci mutum fasihi ya rabu da dukan ƙumshiyoyin tunanin masana, da hasashe-hasashensu, da kuma jituwa game da ra’ayoyi, duk ya bar su can wurin malamai, da masana kimiyya, da masharhanta, da ma tattaunawar da akan yi ta wasu abubuwa daban da rawarsa ta zama fasihi. Dole ne a kai muƙalu ko kundayen nazari can cikin maɗali’u, da azuzuwan koyarwa da ɗakunan taro, amma ba a kai su a dandalin wasan kwaikwayo ba. (rubutu cikin baka biyu da damɓara taddawa duka namu ne).(Hagen, U, A Challenge for the Actor, p.106 ).

A jumlace abin da Hagen take son bayyanawa shi ne, tsakanin masani ko manazarci ko na masanin kimiyya da ɗan wasan kwaikwayo (mai rera waƙa cikin sitidiyo a wannan littafi) tamkar a cewar Bahaushe ‘hanyar mota daban ta jirgi daban, ko kuma ‘babu abin da ya haɗa kifi da kaska’.Shi ɗan wasan kwaikwayo aiwatarwarsa ta karkata ne ga biyar ankarar zuci da ɗanɗanonsa, saɓanin waɗancan masana da muka ambata farko. Da ankarar zuci da ɗanɗano ne ‘dattijo’ da ‘jikokinsa’ na waƙar Bindawa da kuma ‘maigida’ da ‘uwargida’ na cikin waƙar AbdusSamad suka rera waƙoƙin biyu. Haka na tabbata ga mai kallon bidiyoyin waƙoƙin, da kuma zai iya samun damar yin hirar gaba da gaba da waɗanda suka rera su, ko da kuwa da AbdusSamad ne shi da ya rera waƙar a matsayin ‘maigida’.

A nan ne za mu dasa aya ga Babi na Biyar da ke bayani a kan abin da muka kira Ƙyallun Nazarin Salo a Waƙar Cikin Bidiyo. Fatarmu da kawo wannan bayani ita ce mu yi nuni don manazarta waƙoƙin Hausa su duba su gani ko wannan abu ya cancanci kulawarsu musamman ta fuskar salo. Haka kuma abu ne mai muhimmanci ta wannan fuska manazarcin waƙa ya ƙulla abota da ayyukan nazari kan wasannin kwaikwayo da na finafinai. Dalili kuwa shi ne ganin yadda mawaƙan Hausa na baka da na rubutattu, musamman matasa, suka rungumi na’urorin zamani don isar da saƙonninsu ga al’umma. Haƙiƙa ba manufar marubutan wannan littafi ba ce wai abin da aka bayyana a wannan babi ya kasance dil a nazarin salon da ake samu cikin waƙar da aka sa cikin bidiyo. Kamar yadda aka kira babin da sunan ‘ƙyallun’, to haka nan ya kamata a ɗauke shi. Tsinkaye ne na abin da ke can da nisa, bushi-bushi muke ganin sa. Manazarta salon waƙoƙi ne da ke iya sadaukar da bincike sukutum za su iya kakkaɓe ƙurar da ta yi shamaki a halin yanzu, domin salon ya fito kwas kamar wata ɗan sha huɗu.

Kammalawa

A cikin wannan ɗan ƙaramin littafi da aka kira Kukan Kurciya Cikin Waƙoƙin Korona Biyu an yi ƙoƙarin a yi nazarin wasu waƙoƙi biyu na mawaƙan Hausa biyu da ke zaune a birane biyu na cikin ƙasar Hausa, Katsina da Bauci. Mawaƙan su ne Mukhtar Sani Bindawa a Katsina da AbdusSamda Muhammad Babson a Bauci. Bayan ɗan tsokaci kan ma’anar faɗakarwa an kalli waƙoƙin a matsayin na faɗakarwa ga al’umma da kuma hukumomin Najeriya dangane da cutar Korona. A ɓangaren da ya shafi al’umma mawaƙan, duk da shike sun faɗakar dangane da matakan kariya daga cutar, sun kuma faɗakar dangane da watsi da mutane suka yi da Addini da al’adunsu. Suka nuna cewa wannan watsi da al’umma ta yi yana daga musabbabin wannan cutar ta Korona. Ta ɓangaren hukuma kuwa faɗakarwar ta shafi illolin wasu daga cikin matakan kariya da hukuma ta fito da su, da kuma nuni ga haɗarin da ke cikin taɓa addinin al’umma da hujjar yin kariya daga cutar. Kai har ma da barazanar bijirewa ga hukuma muddin aka taɓa addinin al’umma. Wannan sharhi ke nan na dangane da turke da tubalan waƙoƙin.

Ta ɓangaren salo kuwa an duba nau’o’in salo da aka sani musamman ta hanyar Ɗangambo da kuma tattaki ko rufa bayan da ɗalibansa suka yi ga hanyar. Haka nan kuma littafin ya yi ɗan tsokaci kan salon masu rera waƙa cikin sitidiyo domin sakawa cikin bidiyo. Wannan kuwa an yi ne domin a yi nuni ga manazarta waƙoƙin Hausa musamman na wannan ƙarni na ishirin da ɗaya da fatar su zurfafa nazari musamman a kan salo su share mana hanyar da ɗalibai irinmu za su bi totar. Alhamdulillahi.

Manazarta

1.     Ainu, H. A. (2006), ‘Rubutattun Waƙoƙin Addu’a na Hausa: Nazarin Jigoginsu da Salonsu’, kundin digirin Ph.D., Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

2.     Aliyah, A. A. (2003), ‘Nazarin Zambo-Zagi a Adabin Hausa:Tsokaci kan Siyasar Arewacin Nijeriya (1950 -1966)’, Sokoto: kundin digirin M.A. a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

3.     Aliyah, A. A. (2012), “Sharhi kan Waƙar ‘Azancin Waƙa na Hausa”,cikinAhmad Haliru Amfani da wasu,Champion of Hausa cikin Hausa: a Festshrift in Honour of Professor Ɗalhatu Muhammad, Zaria: Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University. sh.356- 367.

4.     Aliyah, A. A. da Hadiza, S. A. (2012), “Gudummuwar Mawaƙan Baka na Hausa a kan Dogaro da Kai da Haɗin Kan Ƙasa”, cikin Farfaru Journal of Multi-Disciplinary Studies 7.Sokoto: Shehu Shagari College of Education. sh. 126-34.

5.     Aliyah, A. A. (2013), “Mata a Idon Marubuta Waƙoƙin Hausa: Nazari daga Waƙar Ƙwazon Mata ta Sulaiman Ibrahim Katsina”, cikin Abdullahi Bayero Yahya da wasu, da wasu (editoci)ZAUREN WAƘA Mujallar Nazarin Waƙoƙin Hausa I, Sokoto: GUARANTY PRINTERS. sh. 224-240.

6.     Aliyah, A. A. (2014), “Ra’ayin Rashin Taƙalidi a Nazarin Adabin Hausa dangane da Mazhabobin Tarke”,cikin Sa’idu Muhammad Gusau da wasu (editoci) Garkuwan Adabin Hausa: a Festshrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo, Kano: Bayero University. pp. 351-358.

7.     Aliyah, A. A. (2016), “Haɓaka Hausa da Yayata Hausa a Duniyar Yau: Waiwaye Dangane da Ra’ayoyin Malaman Hausa”, cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studieas, Kano: Bayero University. sh. 13-21.

8.     Aliyah, A. A. (2017), “They Shout and Cry Out in Vain: The Hausa Poets’ Ignored Panacea for the Problems of Sustained Peace and Progress in Nigeria”,cikinKADA Journal of Liberal Arts 10,Kaduna: Faculty of Arts Kaduna State University, sh. 101- 117.

9.     Aliyah, A. A. (2017),Rupert Moultie East 1898-1975: Tarihinsa da Sharhi a kan Gudummawarsa ga Adabin Hausa 1, Kaduna: Whales Adverts Limited.

10. Auta, A.L. (2008), ‘Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Faɗakarwa a Ƙarni na 20’, kundin digirin Ph.D. Kano: Bayero University.

11. Auta, A.L. (2017), Faɗakarwa a Rubutattun Waƙoƙin Hausa, Kano: Bayero University Press

12. Bargery, G. P. (1957), A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary Compiled for the Government of Nigeria, London: Oxford University Press.

13. Bargery, G. P. (2016), A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary Compiled for G. P. Bargery, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

14. Batagarawa, A. G. (1983), ‘Waƙoƙin Shehu Alƙanci’, kundin B.A. Zaria: A.B.U.

15. Bello, S/M. M.(1974), Taƙaitaccen Tarihin Ƙas ashen Tukururu (fassara zuwa Hausa daga Larabci Sidi Muhammadu Sayuɗi da Jean Boyd; sannan Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya ɗauki nauyin bugawa, da yin taharirinsa da Abu Maimuna Ahmad Bello ya yi).Akwai kuma na asili da Larabci wanda Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Najeriya ta Arewa, Ahmadu Bello ya buga a 1964 a Masar.

16. Birniwa, A. H. (1987), ‘Conservatism and Dissent: a Comparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from circa 1946-1983’, kundin digirin Ph.D. Sokoto:University of Sokoto.

17. Bunguɗu, A. I. (2017), ‘Tarken Rubutattun Waƙoƙin Siyasa na Kabiru Yahaya Kilasik’, kundin digirin M.A. Kano: Bayero University.

18. Dunfawa, A.A. (2002), ‘Waƙa a Tunanin Yara’, kundin digirin Ph.D., Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

19. Ɗangambo, A. (1980), ‘Hausa Wa’azi Verse from circa 1800 to 1970: a Critical Study of Form, Content, Language and Style’, kundin digirin Ph.D. London: School of Oriental and African Studies (SOAS).

20. Ɗangambo, A. (1982), ‘Rikiɗar Azanci:Siddabarun Salo da Harshe cikin “Tabarƙoƙo Tahamisin Aliyu Ɗan Sidi”’,cikin Yahaya, I. Y. da wasu (editoci)Studies in Hausa Language, Literature and Culture 2, Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages.

21. Ɗangambo, A. (2007), Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Tsari ), Zaria: amana publishers ltd.

22. Gusau, S. M. (1983), ‘Waƙoƙin Noma na Baka: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu Musamman a Sakkwato’, kundin digirin M.A. Kano: Bayero University.

23. Gusau, S. M. (1988), ‘Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye-Yanayensu’ kundin digirin Ph.D. Kano: Bayero University.

24. Gusau, S. M. (2003), Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Kano: Benchmark Publishers Limited.

25. Gusau, S. M. (1996), Makaɗa da Mawaƙan Hausa, Kaduna: Fisba M edia Services.

26. Gusau, S. M. (2016), Makaɗa da Mawaƙan Hausa 2, Kano:Century Research and Publishing Limited.

27. Gusau, S. M. (2014), Waƙar Baka Bahaushiya (Laccar Ƙaddamarwar Farfesa ta 14), Kano: Bayero University.

28. Gusau, S. M. (2014), ‘Makaɗan Hausa Jiya da Yau’, cikin Sa’idu Muhammad Gusau da wasu (editoci), Garkuwan Adabin Hausa: A Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo, Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited, sh.117-124.

29. Hagen, U. (1991),A Challenge for the Actor, New York: Macmillan Publishing Company.

30. Halima, A. Ɗ. (2002), ‘Nazari a kan Jigon Faɗakarwa na Adabin Baka’ kundin digirin M.A. Kano: Bayero University.

31. Halima, A. Ɗ. (2012), ‘Kwatanta Tubalan Gina Jigo tsakanin Rubutattun Waƙoƙi da Ƙagaggun Labarai na Hausa’ kundin digirin Ph.D. Kano: Bayero University.

32. Hiskett, M. (1975), A History of Hausa Islamic Verse, London: School of Oriental and African Studies.

33. Idris, Y. (2016), ‘Bijirewa a Waƙoƙin Siyasa: Bincike kan Waƙƙin 1903-2015’ kundin digirin Ph.D., Zaria: Ahmadu Bello University.

34. Muhammad, Ɗ. (1976) edita, Fasaha Aƙiliya, Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Ltd.

35. Muhammad, Ɗ. (1977), ‘Individual Talent in the Hausa poetic tradition: a study of Aƙilu Aliyu and his art’, kundin Ph.D., London: University of London.

36. Muhammad, Ɗ. (1990), edita, Hausa Metalanguage (Ƙamus na Keɓaɓɓun Kalmomi), Ibadan: University Press Limited.

37. Muhammad, Ɗ. (1980), ‘Zumunta tsakanin marubutan Waƙoƙin Hausa da Makaɗa’ cikin Harsunan Nijeriya 10. sh. 85-102.

38. Safana, Y. B. (2015), ‘Nazarin Waƙoƙin Auwalu Isa Bunguɗu na Faɗakarwa kan Itatuwa’ kundin digirin M.A. Kano: Bayero University.

39. Usman, B. B. (2006), ‘Hikimar Magabata: Nazarin Ƙwaƙƙwafi a kan Rayuwar Malam (Dr.) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000)’, kundin digirin Ph.D.,Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

40. Usman, B. B. (2013), ‘Magana Zarar Bunu: Salon Waskiya a Waƙoƙin Baka’, cikin Zauren Waƙa Journal of Hausa Poetry Studies 1, Sokoto: Guaranty Printers, sh. 20-28.

41. Usman, B. B. (2018), ‘Ruwa-Biyu: Sabon Zubin Waƙoƙin Ƙarni na Ashirin da Ɗaya’, cikin Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJALLAC),Damaturu: Yobe State Universitysh. 218-230.

42. Yahaya, I. Y. (1988), Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce cikin Hausa, Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

43. Yahya, A. B. (1987), ‘The Hausa Verse Category of Madahu with Special Reference to Theme, Style and the Background of Islamic Sources and Belief’, kundin Ph.D., Sokoto: University of Sokoto.

44. Yahya, A. B. (1997),Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas Media Services.

45. Yahya, A. B. (2001), Salo Asirin Waƙa, Kaduna: Fisbas Media Services.

46. Yahya, A. B. (2002), ‘Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani Shaƙo cikin Nazarin Waƙa’, cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture 5,Kano:Bayero University, sh. 220-240.

47. Yahya, A. B. (2014), ‘Gudale Waƙar Soyayya: Misalin Gazal (Ghazal) cikin Rubutattun WaƙoƙinHausa’, cikin Sa’idu Muhammad Gusau da wasu (editoci),GarkuwanAdabin Hausa: A Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo, Zaria:AhmaduBello University Press Limited, sh. 125-138.

48. Yahya, A. B. (2016), Salo Asirin Waƙa (sabon bugu), Sokoto: Guaranty Printers.

49. Yakawada, M. T. (1987), ‘Tarkakken Matanin Waƙar Kanzil Azim ta Aliyu Namangi’, kundin digirin M.A. Zariya: Ahmadu Bello University.

Ratayen Waƙoƙin Da Aka Yi Nazari

Waƙar Korona ta Mukhtar Sani Bindawa

1.Ta zo gare mu annoba

 Wayyo Korona wayyoo

Cutar Korona ta sa ba za mu je kasuwa mu je gona ba

 Masallatan Jumu’a an kulle

 Da wayona ni ban taɓa gani ba

 

 2 .Zan riƙa yawaita wanke hannu

 Sannan na sanya takumkumi

 Na koma gida ba za ni fito ba

 

3.Dattijo!

 

4. Na’am ya aka yi jikanlena

 

5. Takunkumi da wanke hannu

 Su kaɗai ba za su sa komai ba

 Ba za su raba ka da annoba ba

 

 6.Miye maganinta jikokina?

 

7.Saɓon Ubangiji zunuban da muke

 Sunka ja mana

 

 8.Wayyoo!

 

9.Cutar korona mashaƙo

 Rashin kumya muka wa Allah

 Kuma ba za ta kau ba

 Sai mun tuba

 

 10. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un

 Saɓon Ubangiji zunuban da muke

 Sunka ja mana

 Cutar korona mashaƙo

 Su suka ja muna, hangenmu

 Ba mafita gare mu

 Sai mun tuba

 Allah Ubangiji mun tuba

 

11.Ƙalallahu Ta’ala fi Ƙur’anil Karimi Mai girma

(Surat Ash-Shura 42, aya ta 30)

 

12.Allah Ubangiji Ya ce

 Da mun ga masifa annoba

 Da hannunmu mu muka jawo ta

 Amma kuma Allah na afuwa

 Da mun koma gare shi mun tuba

 

13.Allah Ubangiji mun tuba

 Ka yi muna lamuni

Albarkacin ƙananan yara

 Albarkar managartan bayi

 

14. Maa nazzalul balaa’u illaa bi ma’asiyaa

Wa maa rufi’a illaa bi taubaa

 

15. Me ta ce cikin Larabci?

 

16. Saɓo ke saukar da bala’i

 Bai tafiya sai da istigifari

 Astagfirullah astagfirullah

 Astagfirullah Allah astagfirullah.

 

17. Shuwagabanni talakawa

 Da malamanmu da ‘yan kasuwa

 Masu hukumci alƙalai

 Ma’aikatan tsaronmu jami’ai

 Da sauran masu madafan iko

 Talakawan birni ko saƙo

 Jama’a maza da mata

 Kowa ya san abin da yake yi wa Allah

 Wanda ba daidai ba

 Mu daina kawai mu tuba

 Astagfirullah astagfirullah

 Astagfirullah Allah astagfirullah

 

18. Matakan da gwamnati ke ɗauka

 Mu yi haƙuri da su

 Kar mu yi kuka da su

 Umurnin ma’aikatan lafiya

 To mu yi riƙo da su

 Kar mu yi wasa da su

 In an ce mu zauna gida mu zauna

 Don kariyarmu ne

 Da ka ji alama ka taɓa kanka

 Kar ka shiga mutane

 In ka ji inda cutar take

 To kar da ka shiga

 Idan kana garin da cutar take

 To kar da ka fita

 Mu daina zargin ba gaskiya ba ce ba

 Kar da mu ƙaryata

 Mu daina zargin cewa waɗansu

 Ne sunka ƙirƙira ta

 Mu roƙi Allah Ubangiji

 Mu sunkuya ƙasa mu tuba

 

19. Ni Ummi Mukhtar Bindawa

 Astagfirullah Allah Astagfirullah

 Ni Fatima Mukhtar Bindawa

 Astagfirullah Allah Astagfirullah

 

20. Saɓon Ubangiji zunuban da muke

 Sunka ja mana

 Cutar Korona mashaƙo

 Rashin kunya muka wa Allah

 Kuma ba za ta kau ba

 Sai mun tuba

 Astagfirullah astagfirullah

 Astagfirullah Allah astagfirullah

Waƙar Korona ta AbdusSamad Muhammad Babson

 

1. Korona Bairos

Allah Ka tsare bayinKa

 

 2. Korona Bairos

 Aiko dafa’i lillahi

 Hhhh!

 Toh!

 

 3.Wai Maigida ya za a yi ke nan?

 Al’amarin nan na damu na

 

 4. Kar ki ishe ni da zancen banza

Ni kan na tushe hancina

To tashi ka ba ni abin girkawa

Ni kam yunwa na damu na

Ai in yunwa na damun ki

Ni ma yunwar na damu na

To ka je ka saya mini garin kwaki

Kai ko da zai ƙulle cikina

Wai ni kan tafiyarku ta ran nan

In ce dai ba ku je Legas ba

 

 5.Ni da nake magana ta abinci

Kai fuskarka kake ɓoyewa

Ba mu da manja

Ba mu da magi

Ba mu da ko garin tuƙawa

 

6. Ɗauko carbinki mu kama salati

Dug ga Ilahi ake komawa

Haba ka tashi daga kwance ka nemo gari

Ni in samu abin tuƙawa

 

7.Wai shin wane ne zai fita

 Ni kam Anti Korona tana zagawa

 Mamar Kaltume bi ni a sannu

 Kin fa daɗe ba ki yo yaji ba

 

8.Ba ni da ko sisi in faɗa miki

 Ke ba ki san haƙurin yunwa ba

 

9.To ko a abokanka sai ka nema

 Ai na san ba za ka rasa ba

 Allah na kula wannan matar

 Ba ƙaunar in rayu take ba

 Don Allah ka fusata ka tashi

 An ce cuta ba mutuwa ba

 Na san cuta ba mutuwa ba

 Kuma cuta ba inwa ba

 In ba gwamnati ce ta sake ba

 Ko wundo ba zan leƙa ba

 

10.Sarkin rahama kawo mana ɗauki

Kar Ka bari yunwa ta kasha mu

Dut tallafin da ake bayarwa

Mu har yau ya kasa ishe mu

 

11.An ɗaure akuya ba dusa

Wai sai dai mu ci ‘yar ajiyarmu

In ko ta ƙare dole a fantsama

Na rantse sai dai ta rutsa mu

Amma don Allah kowa ya bi doka

In dai ba ta hanin salla ba

Post a Comment

0 Comments