Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ba Ya Gamsar Da Iyalinsa Saboda Azumin Nafila?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam barka da warhaka, wani bawan Allah ne yake azumin Litinin da Alhamis, ga shi yana shiga hakkin matarsa wani lokachin, tayimishi magana amma ya ce shi ba zai daina ba so yake ya saba da azumin, komai zaifaru sai dai ya faru, malam azumin ko sauke hakkin matarsa? Allah ya kara daukaka mlm na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Tabbas yana daga cikin haƙƙoƙi na wajibi na ma'aurata a kan junansu sauke wa juna haƙƙin aure ta ɓangaren saduwa, kuma rashin cika wannan haƙƙin na iya sa ɗaya daga cikin ma'aurata ya kusanci saɓon Allah ta hanyar zina musamman idan aka samu raunin imani, ko kuma hakan ya haifar da mutuwar aure ma baki ɗaya.

Shi kuma yin azumin Litinin da Alhamis sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah , saboda haka ya sauke wajibin iyalinsa a kansa shi ne a gaba a kan yin azumin nafila, saboda katange matarsa ga aikata abin da bai dace ba, kamar yadda yake faɗin komai zai faru ya faru, wannan magana tasa kuskure ne.

Saboda rashin gamsar da juna a tsakanin ma'aurata kaɗai na iya haifar da faruwar fitinar da ba za a iya shawo kanta a tsakaninsu ba in ba ta wannan hanyar gamsarwar ba. Saboda haka sai ya rage yin azumin a kai a kai ko da ba zai daina ba gaba ɗaya tun da yana son koyi da sunnah, kuma ita kanta gamsar da iyali akwai lada a cikinta, kamar yadda azumin taɗawwu'i yake da lada.

Idan kuma ya ƙi ji, to ta yi haƙuri da shi a kan hakan, saboda kada matsawarta a gare shi ya haifar da wata fitina a tsakaninsu, matuƙar dai ba kusantarta ne ba ya yi baki ɗaya ba.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments