Ticker

6/recent/ticker-posts

Rubutattun Kalmomin Hausa Masu Ma'ana Sama Da Ɗaya

Daga:

Daga Ibrahim Sheme

A harshen Hausa, akwai kalmar da a rubuce ta kan ba da wata ma'ana, to amma a magana za ta iya haifar da wata ma'anar daban, ko ma fiye da ɗaya. Irin waɗannan kalmomin, wajen rubuta su ba a ƙara masu wasali ko wani ɗigo ko wata alama. Sai an saka su cikin jimillar zance ne ake gane inda ake so su dosa. Wani abu da na gano game da irin waɗannan kalmomin shi ne duk guntaye ne, sannan na biyu kuma yawancin duk wata kalma da aka aro ta daga Larabci ko Turanci ba ta bayar da ma'ana sama da ɗaya (misali sadaka, waliyyi, alfijir, malami, table, basukur, fanka, rediyo, janareto, da sauran su).

Ga misalan kalmomin da a rubuce za su iya ba da ma'ana sama da ɗaya, kuma na fassara su da Turanci don a fi saurin ganewa:

baba (father, mother, dye):

1. "Baba ya aike ni"

2. "Baba ce ta dafa abincin"

3. "Sai da baba ake rini"

bori (spirit worship, bad groundnut, go haywire)

1. "Sarki ya hana 'yan bori sakewa"

2. "Ina cin gyaɗa na tauna bori"

3. "Waccan kazar na yin bori"

ciki (stomach, inside, pregnancy)

1. "Cikin dare ciwon ciki ya kamashi"

2. "Sun tashi sun shiga ciki"

3. "Ta na da ciki"

ciwo (wound, a wild fruit)

1. "Ta ji ciwo a hannu"

2. "Mun shiga daji mun samo ciwo nunanne"

dafa (cook, lean on)

1. "Faɗa wa Layla ta dafa mana taliya"

2. "Ya dafa bango ya hau kan doki"

daga (from, struggle)

1. "Kun zo daga ina ne?"

2. "Za a sha daga da ita!"

dama (right side, mix)

3. "Faro daga dama, ba hagu ba"

4. "Kai wa Layla furar ta dama!"

dawa (forest, sorghum)

1. "Sun shiga dawa neman magani

2. "Zan noma dawa da wake a wannan gonar"

dara (world, a game, a cap)

1. "Ta yi fushi ta shiga dara"

2. "Sun zauna a layi su na dara"

3. "Ya sanyo babbar riga da dara"

doka (law, beat, a tree)

1. "Gwamnati ta yi dokar hana barace-barace"

2. "Makaɗi ya doka ganga"

3. "A dajin akwai bishiyoyin doka sosai"

doki (beat, horse)

1. "Ka doki jakin sosai mana"

2. "Talba ya hau doki ya tafi fada"

fafa (cut a calabash, boastful)

1. "A fafa goran kafin ku tafi"

2. "Rabu da shi, ya cika fafa"

fata (skin, hope)

1. "Ki na da kyan fata"

2. "Mu yi fata alƙalin ya yi mana adalci"

fito (whistling, come out, assistance in crossing a river)

1. "An hana yara yin fito"

2. "Ki faɗa masu su fito mu tafi"

3. "Masu fito sun hau gora a gulbi"

gaba (front, enmity, private part)

1. "Shiga gaba ku tafi"

2. "To, gaba dai babu kyau"

3. "Kayan sun rufe gaba kuwa?"

gaɓa (joint, river bank)

1. "Ya ji zogi a gaɓar hannu"

2. "Mun baro su a bakin gaɓar rafi"

gado (inheritance, bed, a bird's name)

1. "An raba gado an sallami kowa"

2. "Ba kullum ake kwana a gado ba"

2. "Yara sun harbo gado za su gasa su ci"

gara (it's better, silly person, termite)

1. "To, gara dai a tafi da wuri"

2. "Wannan yaron ai gara ne"

3. "Duk gara ta cinye rigar"

 gari (flour, town)

1. "Ta je ta niƙo garin tuwo"

2. "Akwai wani gari mai suna Tsanni"

giɓi (space, gap between teeth)

1. "Sun bar giɓi a tsakanin gidajen"

2. "Akwai giɓi a bakin shi"

gora (gourd, heavy stick)

1. "Zuba mini ruwa a gora zan tafi gona"

2. "Ya ɗauki gora zai bugi ɓarawo"

gyaɗa (groundnut, nod head)

1. "An dafa gyaɗa ta dafu sosai"

2. "Sai ya gyaɗa kai ya ce haka ne"

iya (able, mother)

1. "Ka iya mota ne?"

2. "Sannu da ƙoƙari, iya!"

ja (red, pull)

1. "Motar tasa ja ce"

2. "Ku kama ku ja sosai"

kada (don't, crocodile)

1. "Kai, kada ku bari ta faɗi"

2. "Wa zai iya shiga ruwa da kada a ciki?"

kaɗa (drum beating, cotton, push)

1. "Makaɗin ya kaɗa kalangu"

2. "Sun ɗebo kaɗa a gona"

kai (you, head, take it there, exclamation of surprise)

1. "Kai da ita 'yan'uwa ne"

2. "Ya na da farin gashi a kai"

3. "Ɗauki kwanon ki kai mata"

4. "Kai haba! Yaushe hakan ta faru?"

ƙaura (migration, type of sorghum, armed hunter, warrior)

1. "Sun yi ƙaura zuwa Kano saboda 'yan ta'adda"

2. "Wannan dawar ai ƙaura ce ka kawo"

3. "Na ga wani ƙaura ya wuce ta nan za shi farauta"

ƙauye (village, aside)

1. "Ya tafi ƙauye domin ziyara"

2. "Kai koma ƙauye sai mun gama tattaunawa"

mace (female, wife, dead)

1. "Mace aka haifa"

2. "Ya mutu ya bar mace ɗaya"

3. "Karen ya mace"

mai (oil, of)

1. "A sanya wa motar mai"

2. "Wannan shi ne mai sayar da ayabar"

mama (mother, breast, take by surprise)

1. "Idan kin je ki gai da mama"

2. "A ba yaro mama ya sha ya daina kuka

3. "Wa aka mama da aka je?"

mara (food measurement, pubis, slap, lacking in something)

1. "Ta sa mara ta kwashe tuwon"

2. "Ƙurji ya fito masa a mara"

3. "Wa aka mara a cikin ku?"

4. "Ban son hulɗa da mara kunya"

mata (wife, women)

1. "Shi ma ya na da mata"

2. "An tara mata an raba masu kayan tallafi"

matashi (young man, pillow)

1. "Matashi ne ɗan shekara ashirin da uku"

2. "Miƙa masa matashi zai kwanta ya huta"

rana (sun, date)

1. "Rana ta fito sosai"

2. "A wace rana za a ɗaura auren?"

ruga (run, Fulani settlement)

1. "Yaron ya ruga gida"

2. "Bafulatanin ya koma ruga ya ɗauko shi"

sabo (new, familiarity)

1. "Wannan mashin ɗin sabo ne?"

2. "Ta yi masa mugun sabo"

saƙo (message, deep crevice, insert)

1. "Na samu saƙo daga Ajakuta"

2. "Ku duba wani lungu da saƙo"

3. "Sai na ji ya saƙo wata magana a zancen"

saje (whiskers, blend with, sergeant)

1. "Ya yi gemu da saje"

2. "Ta shiga ciki ta saje da su"

3. "Wancan ɗan sandan ai saje ne"

sarki (emir, group head)

1. "Akwai sarki a Jama'are"

2. "'Yan dako sun naɗa sarkin su"

sauna (fool, fear)

1. "Shi ai sauna ne"

2. "Ya ƙi zuwa don ya na sauna"

saura (remains, empty farm in dry season)

1. "An gama cin abinci, har an bar saura"

2. "Wannan saura ce da aka shekara biyu ba a noma ba"

sheƙa (downpour, bird's nest)

1. "A daren jiya an sheƙa ruwa"

2. "Tsuntsu ya yi sheƙa a kan bishiya

suma (fainting, hair on head)

1. "Da jin labarin, sai ta suma"

2. "Ya bar suma a ka duguzum ba kyau"

sura (chapter, image)

1. "A wace sura Allah ya ce haka?"

2. "Mace ce mai kyan sura"

wawa (fool, grab)

1. "Ka san fa shi wawa ne"

2. "Sun ga kuɗi sun saka wawa"

yari (chief prison warden, earrings)

1. "An miƙa su ga yari don ya kulle su"

2. "Ta saka yari mai ƙyalli"

yarinya (small girl, girlfriend)

1. "Ina tsaye sai ga wata 'yar yarinya ta fito daga gidan"

2. "Ya faɗa mani cewa Zainab yarinyar ka ce"

yaro (small boy, son, staff)

1. "Ba za a ɗauke shi ba, don yaro ne ƙwarai"

2. "Ta ce mani yaron ta ne"

3. "Malam Nagona ai yaron Baturen nan ne"

zagi (insult, escort)

1. "Matar ta sha zagi a wajen su"

2. "Zagi na riƙe da akalar dokin sarki"

zana (draw a picture, thatch wall)

1. "Idan za ka zana ni, to ka zana ni da kyau"

2. "Ya yi wa gidan sa sabuwar zana"

zobe (ring, encircle)

1. "Ta cire zobe ta ba shi"

2. "Sojoji sun yi wa dajin zobe"

zuga (instigate, blow fire)

1. "Ku daina zuga ta fa"

2. "Maƙera na ta zuga wutar'

Ko za ku iya tuno da ire-iren waɗannan kalmomin?

Post a Comment

0 Comments