Ticker

6/recent/ticker-posts

Mun Ci Bashin Kuɗin Biki, Ni Da Mijina, Wa Ya Dace Ya Biya?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya; wani ne ya nemi budurwa aka sa masu ranar aure, da auren ya zo sai ya kasance sun yi rigima da wani a kan kasuwancinsa, har aka rufe shi a gidan yari, iyayensa ba su bari an daga bikin ba, suka ce a fara za a yi belin din sa kafin ranar daurin aure, to sai ya yi wa amaryarsa waya a kan cewar tun da ya kama za a yi biki ba shi nan to ta ranci kuɗi ko ma a ina ne dubu N150,000 ta yi duk abin da suke bukata na walima kunshi da sauransu, da niyyar zai biya bayan bikin, to malam har ya fito aka yi biki, sai Allah ya sa kafin ya biya mutanen sai suka rabu da matar, kuma ba a biya kuɗin nan ba, malam mene ne hukuncin wannan bashin, shin ita ce za ta biya ko mijin nata? Saboda bayan mutuwar auren mijin nata ya ce shi wallahi ba zai biya ba, ita za ta nema ta biya tun da sun rabu.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, ‘yar uwa a zahirin abin da ya bayyana a gare mu in dai wannna maganar haka suka yi ta, to mijin nata shi ne ya kamata ya ɗauki nauyin biyan wannan kuɗi, saboda shi ne ya ba da umurnin a ciwo wannan bashi, kuma ya ɗauki nauyin cewa zai biya idan ya fito gidan kurkuku, sai dai mu a nan ba mu isa mu ce lallai-lallai hakan za a yi ba, wannan matsalar magabatansu ne ya kamata su zauna don a warware matsalar, idan kuma duk ya gagara sai a garzaya kotu, shi Alƙali zai bayyana wanda ya wajaba a kansa ya biya wannan kuɗi a tsakanin su biyun, wannan ita ce magana ta gaskiya.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments