Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Yawan Saɓon Allah, Mene Ne Shawara?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam a cikin zuciya ta ina jin tsoron Allah, kuma ina son bin umarnin Allah, sai dai ina yawan saɓon Allah kuma malam ina so a taimake ni da shawara a kan hakan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 Wa alaikum assalamu.To ɗan'uwa, ina fatan za ka karanta wannan kisar da idon basira, domin za ka samu shawarar da kake bukata:

Wani saurayi ya je wajen Ibrahim ɗan Adhama, (ɗaya daga cikin magabata), sai ya ce masa zuciya ta tana tunkuda ni zuwa saɓo, ka yi min wa'azi, sai ya ce masa: Idan ta kiraka zuwa saɓawa Allah to ka Saɓa masa amma da sharuda guda biyar, sai saurayin ya ce fadi mu ji:

1. Idan zaka saɓawa Allah, to ka ɓoye a wurin da ba zai ganka ba, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za a yi na ɓoye masa, alhalin babu abin da yake ɓuya gare shi, sai ya ce: yanzu ba ka jin kunya ka Saɓa masa alhali kuma yana ganinka.

2. Idan za ka saɓawa Allah to kar ka Saɓa masa a cikin kasarsa, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, ina zan je, alhali duka duniya ta sa ce, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka Saɓa masa alhali kana zaune a saman kasarsa.

3. Idan za ka saɓawa Allah to ka daina cin arzikinsa, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni'imomi daga gare shi su ke, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka Saɓa masa alhali yana ciyar da kai kuma yana shayar da kai, yana ba ka karfi.

4. Idan ka saɓawa Allah, to idan mala'iku suka zo tafiya da kai wuta, ka ce ba za ka tafi ba aljanna za ka, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah ai sun fi karfina, kora ni za su yi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar alkiyama ka ce: ba kai ka aikata su ba, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala'iku masu kiyayewa, sai ya fashe da kuka ya tafi yana maimaita wannan Kalmar ta karshe.

 in har kana tuna ɗaya daga cikin waɗannan idan za ka aikata zunubi, to tabbas za ka ji Kunyar Allah.

Allah ne mafi sani

Amsawa🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments