Ticker

6/recent/ticker-posts

Musan Tauhidi 04: Hukuncin Ilimin Taurari A Musulunci

Ilimin taurari akwai wanda yake halal shi ne:

 Gwargwadon yadda mutum zai san ilimin sanin Alƙibla ko juyawar lokuta.

 Amma indai ba wannaan ba, to an saki layi daga umarnin musulunci.

 Duk wani nau'in ilimin taurari daya ƙunshi binciken wata ƙaddarar da za ta faru anan gaba ko kuma ta faru ga wani Ɗan Adam, to wannan malamai sun ce haramun ne.

Akwai hadisi wanda Imam Abu Dawud da Ibnu Majah (R.h) suka karɓo kamar haka:

 Abdullahi Ɗan Abbas (R.A) Ya ce:

 Manzon ALLAH yana cewa:

Duk wanda ya kutsa cikin wani ilimi na taurari, to haƙiƙa ya kutsa wani reshe ne na sihiri, ya ƙara abinda ya ƙara.

Ma'ana:

 Gwargwadon zurfinka a cikin ilimin taurari, shi ne gwargwadon zurfinka a cikin shirka.

 Wannan abinda sukeyi na binciken aure a tsakanin mutane, mace taje a duba mata irin mijin da za ta aura ko kuma ta bada sunansa da nata a duba mata, ko kuma idan an sace wani abu, sai aje wajensu su duba wai suce yana waje kaza, duk ƙarya ne kuma haramun ne.

 Cikakken mumini ya riga yasan cewa dukkan abubuwa suna gudana ne bisa ƙudura da iradar ALLAH, babu wanda ya isa ya canja faruwarsu.

Masu irin wannan binciken, suma wasu nau'i ne na bokaye, mayaudara ne sunfi bokayen hatsari a cikin al'ummah.

 Domin su bokaye yawancinsu ko sallah ma basa yi, amma su waɗannan masu bincike-binciken suna shiga rigar malumta ne, sannan kuma sukanyi amfani da wani wuridi wanda na shaiɗanun aljanu ne, masu sawa ayi yanka domin susha jini ko wanin hakan.

Haka kuma duk wani abu da malaman tsubbu keyi na mallaka ko shanye mace ko namiji wannan ma haramun ne, kuma yana kai mutum ga kafurci, domin sihiri kafurci ne.

 Haka kuma duk wani wanda ya ce maka wai akwai wata mace mai farar ƙafa, wato wata macece wacce idan ka aure ta komai naka zai lalace to ƙarya yake, babu wannan a duniya, domin bawaba ya wuce ƙaddararsa, lallai ALLAH yana rubuta ƙaddarar ko wanne bawa ne tun yana wata huɗu a cikin mahaifiyarsa.

 Haka kuma duk wani wuridin da za a bama mutum a ce sai ya sanya tufafinsa abaibai, ko sai kayi wanka da wani ruwan rubutu ko wanin haka,

 Ko kuma ya zauna kan taburmar da aka saƙa a baibai, ko kuma abawa mutum laya ya yita yawo da ita, duk wannan yana iya kai mutum ga shirka.

 Manzon ALLAH {s.a.w} bai koyar da haka ba, kuma bai aikata haka ba, kuma ba'ayi yagani ko yaji labari baice komai ba.

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya koyar damu addu'o'in da zamuyi a kan kowacce buƙata, ba sai mutum ya yi wasu abubuwa masu kama da camfi ba da zasu rabashi da addininsa ba.

 Mafificiyar shiriya ita ce shiriyar Manzon ALLAH {s.a.w} kuma dukkan alkhairi yana cikin koyi dashi.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments