Ticker

6/recent/ticker-posts

Cali Cajinge - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

 Jagora: Siyasa ta dawo

 Gwamna Alu zai tuta yam.

Yara: Cali siyasa ta dawo,

 Gwamna Alu zai tuta yam.

 

Jagora: Siyasa ta dawo

 Gwamna Alu zai tuta yam.

Yara: Cali siyasa ta dawo,

 Gwamna Alu zai tuta yam.

 

Jagora: Ya Allah Sarki Allah,

 Ya Allah kama ma Alu,

Yara: Shehu kaso ba musu ba.

 

Jagora: Ya Allah Sarki Allah,

 Ya Allah kama ma Alu,

Yara: Shehu kaso ba musu ba.

 

Jagora: Ina yin kiran jama’ar birni,

 Ina yin kiran jama’arƙ ƙauye,

 Gwamna Alu zai tuta yam.

 

Jagora: Ina yin kiran jama’ar birni,

 Ina yin kiran jama’arƙ ƙauye,

 Gwamna Alu zai tuta yam.

Yara: Shehu ka zakka ko yaushe.

 

Jagora: Idam Buzu bai gwamna

Yara: Sai ya tsaya kallosh shayi.

 

Jagora: Idam Buzu bai gwamna

Yara: Sai ya tsaya kallosh shayi.

 

Jagora: Alu bai gasar kyan aiki,

 Ɗan Barade na jikan Umar,

 Ya ɗamara Baban,

Yara: Baban Bello.

 

Jagora: Alu bai gasar kyan aiki,

 Ɗan Barade na jikan Umaru.

Yara: Yo ɗamara baban Bello.

 

Jagora: ‘Yan ta ɓare sun yo kunya,

 Wai an ce sun ɗau boka,

 Dun gurinsu a ka da Alu,

Yara: Ba su iyawa wa su nan.

 

Jagora: ‘Yan ta ɓare sun yo kunya,

 Wai an ce sun ɗau boka,

 Dun gurinsu a ka da Alu,

Yara: Ba su iyawa wa su nan.

 

Jagora: Boka da ɗan bori,

 Wannan bai iya ka da Alu.

Yara: Sai da nufin yardar Allah.

 

Jagora: Boka da ɗan bori,

 Wannan bai iya ka da Alu.

Yara: Sai da nufin yardar Allah.

 

Jagora: Ummaru Ɗan Ama na Alu,

 Ya ba ni gida ya bani kuɗɗi,

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Ummaru Ɗan Ama na Alu,

 Ya ba ni gida ya bani kuɗɗi,

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Ummaru Ɗan Ama na Alu,

 Ya ba ni gida ya bani kuɗɗi,

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Salihu Barade babban sarki na,

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Salihu Barade babban sarki na,

 Sannu masoyin gwamna Alu.

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Salihu Barade babban sarki na,

 Sannu masoyin gwamna Alu.

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Ahamed Barade ubana na,

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Ahamed Barade ubana na,

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Ina kai kai,

Yara: Cali siyasa ta dawo gwamna Alu zai tuta yam.

 

Jagora: Ahamed Barade ubana na,

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Mamman ɗan Cadi sadauki na.

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Shi ko ciyaman ne Sabon Birni Ɗan Cadi nai min alheri.

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

Jagora: Sarkin baƙi Yawale ya kyauta.

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

 

Jagora: Sarkin baƙi Yawale ya kyauta.

Yara: Yanda yake mana ya kyauta.

 

 

Jagora: Sardaunan Gobir sanata,

 Sannu masoyin gwamna Alu.

 

Jagora: Sardaunan Gobir sanata,

 Sannu masoyin gwamna Alu.

 

Jagora: Mu mun yi addu’a mun kore gada,

 Had da barewa -

Yara: mun harbe.

 

Jagora: Mu mun yi addu’a mun kore gada,

Yara: Har da barewa mun harbe.

 

Jagora: Ri ‘yan garda masu abin kunya,

 Na iske su gidan mata,

 An sha giya an sha wiwi,

Yara: Har wasu na koyon banjo.

 

Jagora: Ri ‘yan garda masu abin kunya,

 Na iske su gidan mata,

 An sha giya an sha wiwi,

Yara: Har wasu na koyon banjo.

 

Jagora: Alu bai gasar kyan aiki,

 Ɗan Barade na jikan Umar.

Yara: Yo ɗamara Baban Bello.

 

Jagora: Angon Murja angon Arziki,

 Kai,

Yara: Yo ɗamara Baban Bello.

 

Jagora: Angon Arziki angon Murja ne,

Yara: Yo ɗamara Baban Bello.

 

Jagora: Angon Arziki angon Murja ne,

Yara: Yo ɗamara Baban Bello.

 

Jagora: Baban Hodiyo baban Lamiɗi,

 Kai,

Yara: Yo ɗamara baban Bello.

 

Jagora: Baban Hodiyo baban Lamiɗi,

 Kai,

Yara: Yo ɗamara baban Bello.

 

Jagora: Cali alƙawali na naɗ ɗauka,

 Haƙ in dai gada zai gwamna,

 In dan fatin PDP,

Yara: Wanga karon da mun bar shi.

 

Jagora: Cali alƙawali na naɗ ɗauka,

 Haƙ in dai gada zai gwamna,

 In dan fatin PDP,

Yara: Wanga karon da mun bar shi.

 

Jagora: ‘Yan ta-ɓare sun yo kunya,

 Wai nan ce sun ɗau boka,

 Don gurinsu a ka da Alu,

Yara: Ba su iyawa wa su nan.

 

Jagora: Boka ko da ɗan bori,

Wannan bai iya ka da Alu.

Yara: Sai da nufin yardar Allah.

 

Jagora: Boka ko da ɗan bori,

Wannan bai iya ka da Alu.

Yara: Sai da nufin yardar Allah.

 

Jagora: Ummaru Ɗan Ama jigo,

 Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.

Yara: Yanda yake min ya kyauta.

 

Jagora: Ummaru Ɗan Ama jigo,

 Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.

Yara: Yanda yake min ya kyauta.

 

Jagora: Salihu Barade babban sarki na,

 Sannu masoyin gwamna Alu.

Yara: Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.

 

Jagora: Salihu Barade babban sarki na,

 Sannu masoyin gwamna Alu.

Yara: Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.

 

Jagora: Na gode mai gida haji Faruku,

Yara: Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.

 

Jagora: Kwamishinan kuɗi nau dattijo Faruku sannu,

 Kai,

Yara: Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.

 

Jagora: Kwamishinan kuɗi zaki Faruku yai min alheri.

Yara: Ya ba ni gida yab ban kuɗɗi.

 

Jagora: ‘Yan garda masu abin kunya,

 Na iske su gidan mata,

 An sha giya an sha wiwi,

Yara: Ha wasu na koyon banjo.

 

Canjin kiɗa da rauji

 

Jagora: Baba a bar maka yaƙi,

 Aliyu sabon gwamna

Yara: Baba a bar maka yaƙi,

 Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Baba a bar maka yaƙi,

 Aliyu sabon gwamna

Yara: Baba a bar maka yaƙi,

 Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Mu sabka Sakkwato birni,

 Saboda nau Ɗan Ama.

Yara: Tun da dai mun ka riƙe shi,

 Ba mu kukan babu.

 

Jagora: Ga Cali ɗan Lajinge,

 Cali ƙanin ɗan gwamna.

Yara: Mijin Zakiya Mamman,

 A bar ka sarkin waƙa.

 

Jagora: Karen gida da ka ga za ka far ma kurar daji,

Yara: Ka bar shi in sun ka game ƙashin shi sai ya ɓazge.

 

Jagora: Mu sauka Sakkwato birni,

 Saboda nan Ɗan Ama.

Yara: Tun da dai mun ka riƙe shi,

 Ba mu kukan babu.

 

Jagora: Baba masoyin gwamna,

 Ummaru Ɗan Ama,

 Kai,

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Madawakin jigo na gwamna sarkin Yamma,

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Madawakin roƙo Umaru Ɗan Ama,

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Na ji ‘yan ta ɓare,

 Wai a kan,

 Sun ka ƙi noman rani,

Yara: Shekara ta tashi

 Su sun riga sun watse.

 

Jagora: Na ji ‘yan ta ɓare,

 Wai a kan a ba su muƙami,

 Sun ka ƙi noman rani,

Yara: Shekara ta watse,

 Su sun riga sun watse.

 

Jagora: Muna da ‘yan ga-aiki cikinku nau ‘yan ta-ɓare,

Yara: Tun da ba a da mulki,

 A kama sabon izza.

 

Jagora: Na yaba maka giwa Sahabi Isa Zaki.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Sakataren gwamnati ne Sahabi ɗan Lattijo.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Na yaba maka fam sek Aminu Dikko Sadauki.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Na yaba maka Bello,

 Guiwa uban mai waƙa.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Sakkwatawa asuli ku zo mu zaɓi Aliyu.

Yara: Ka bar su kowa ya wuce,

 

Jagora: Mahassada su ji habshi,

 Aliyu shi ag gwamna.

Yara: Rabbana shi yac ce a bar shi ko don dole.

 

Jagora: Baban Hodiyo zaki

Yara: Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Baban Hodiyo zaki

Yara: Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Baba uban Lamiɗo,

Yara: Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Baba uban Lamiɗo,

Yara: Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Angon Arziki jigo,

Yara: Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Baba angon Murja,

Yara: Aliyu sabon gwamna.

 

Jagora: Baba sabon sarki Salihu ban ran mai ba.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Na yaba maka Walin Gagi nau dattijo.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Na yaba maka Walin Gagi nau dattijo.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Ga wasiƙa na yo a kai ma nau ɗan Ama,

Yara: Sai ya duba ta da kyau,

 Ya kai ta hannun gwamna.

 

Jagora: Ga wasiƙa na yo a kai ma nau ɗan Ama,

Yara: Sai ya duba ta da kyau,

 Ya kai ta hannun gwamna.

 

Jagora:Gwamna nai mishi koke,

 Tun da ba ni da mota,

 Ban da kuɗɗin Mkka,

Yara: Ga gida da yawa a gai da tsohon kwano.

 

Jagora: Sakatarenmu na kirki Aminu Arɗo Sadauki,

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Sakatarenmu na kirki,

 Ibrahim nau Arɗo,

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Ibrahim ɗan Arɗo na zama na gaishe ka,

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Gobirawa asuli ku zo mu zaɓi Aliyu.

Yara: Ka bar su kowak kauce wuya ta kai mai kaya.

 

Jagora: Ashe hukuma INEC ita ka yanke shari’a.

Yara: Sai ta yanke hukunci,

 Ta kore Arnan Togo.

 

Yara: Sai ta yanke hukunci,

 Ta kore Arnan Togo.

 

Jagora: Na ga masu adawa wajen mu sun sha kaye.

Yara: Sun yi kwance ga hanya kamat ɗiyar raƙumma.

 

Jagora: Na ga masu adawa wajen mu sun sha kaye.

Yara: Sun yi kwance ga hanya kamat ɗiyar raƙumma.

 

Jagora: Na yaba maka giwa Faruƙu nau ɗan Yabo.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Na yaba maka giwa Faruƙu nau ɗan Yabo.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Ɗan Cadi zo ka riƙe mu,

 Ka gyara sabon birni.

Yara: Abin da kai mun ka sani,

 A bar ka sai ka kama.

 

Jagora: Mu sabka Sabon Birni,

 Saboda Sarkin Baƙi.

Yara: Tun da dai mun ka riƙe shi,

 Ba mu kukan babu.

 

Jagora: Shugaban PDP Yawale Sarkin Baƙi.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: ga sanata nan jigo Sardauna mai,

 Kai!

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Ga sana nan jigo,

 Sardauna ban ran mar ba.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Na ga ‘yan ta-ɓare du wajenmu sun sha kaye,

Yara: Sun yi kwance ga hanya,

 Kamar ɗiyar raƙumma.

 

Jagora: Shugaban ‘yan ta-ɓare,

 Na ganai ya walga.

Yara:Mun ga yara ka jifan shi,

 Wai kare ya wubce.

 

Jagora: Shugaban mata ko,

 Taƙar ƙashiya ta ɓare.

Yara: Wance ba a da kaya,

 Duwai ga hilin Allah.

 

Jagora: Baba sabon sarki,

 Salihu ban ran mai ba.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Baba Baraden Wamako,

 Mai kgida kyauta,

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Baba Baraden Wamako,

 Maigida na gode.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Arjika nau lattizo Tireta,

 Ban ran mai ba.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

 

Jagora: Arjika nau Lattizo Tireta,

 Nai mini rana.

Yara: Abin da yay ya kyauta,

 Saboda sabon gwamna.

Post a Comment

0 Comments