Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora: Hadarin ƙasa mai maganin sanin kabido, Ali ɗan Amadu.
Yara: Uban Lamiɗo gamji Allah ya jima
da ranka,
Ina mai halin haiba?
Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade
Jagora: Hadarin ƙasa mai maganin sanin
kabido,
Ali na Amadu.
Yara:Uban Lamiɗo gamji ya jima da
ranka.
Jagora: Ɗan sarki mai halin
sarauta Ali Ɗan Barade.
Yara: Mai raba jakkuna da
doki a haɗa da riga.
Jagora: Ɗan sarki mai halin
sarauta Ali Ɗan Barade,
Yara: Mai raba jakkuna da
doki ya haɗa da riga.
Jagora: Allah ya ba ka
lokaci ba sai na hwaɗi ba,
Yara: Miƙe ƙahwahunka wanga ƙarfe wa za ka tsoro,
Ina mai halin haiba?
Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade.
Jagora: Allah ya ba ka
lokaci ba sai na hwaɗi ba,
Yara: Miƙe ƙahwahunka wanga ƙarhe wa za ka tsoro?
Ina mai halin haiba?
Mai girma Alu na gwamna Ali Ɗan Barade.
Jagora: Haɗarin ƙasa mai maganin sanin
kabido Ali na Amadu,
Yara: Uban Lamiɗo gamji Allah ya jima
da ranka.
Jagora: Hadarin ƙasa mai maganin sanin
kabido Ali na Amadu,
Yara: Uban Lamiɗo gamji Allah ya jima
da ranka.
Jagora: Ɗan sarki mai halin
sarauta Ali Ɗan Barade,
Yara: Mai raba jakkuna da
doki ya haɗa da riga.
Jagora: In mafarauta suna
farauta daji,
Da bindigogi,
Da kiban dahinsu,
Da sun zo sun ka iske zaki ba mai tsayawa.
Yara: Dawa ya ɓaci wani mutum ba ya
jiran ƙani nai,
Ina mai halin haiba?
Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade.
Jagora: In mafarauta suna
farauta daji,
Da bindigogi,
Da kiban dahinsu,
Da sun zo sun ka iske zaki ba mai tsayawa
Dawa ya ɓaci.
Yara: Dawa ya ɓaci wani mutum ba ya
jiran Baradai.
Ina mai halin haiba?
Mai girma a gai da gwamna Ali Ɗan Barade.
Jagora:Ɗan Sarki mai halin
sarauta Ali Ɗan Barade,
Yara: Mai raba jakkuna da
doki ya haɗa da riga,
Iana mai halin haiba?
Mai girma a gai da gwamna Ali ɗan Barade.
0 Comments
Post your comment or ask a question.