Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Taimaka mana Jalla magaban Sarki,Taimaka
mana Jalla magaba,
Allah
mai bai wa kowa samu.
Sakkwatawa
an yi ta ƙare,
Ko gobe
Alu ne gwamnan Sakkwatawa.
Sakkwatawa
an yi ta ƙare,
To ko
yanzu Aliyu ne gwamna sabo hul.
Hankali
kaɗan shafa min ya fi,
Ehen!
Alu,
angon Murjaaa angon Murja.
Da
ranarka.
Angon
Arziki mai dubun nasa har kullum.
Angon
Arziki mai dubun nasara har kullum,
Baban
Hodiyo jarumina ne kai komai,
Baban
Mahadi ban manta girmanka,
Yauwa!
Alu
gwamnan Sakkwatawa,
Ina
babab Yasiraaa Allah ya kyauta darshanka,
Ga
addu’ar Ahmad nan na turo,
Ga
addu’ar Ahamad na turo,
Baban
A’ishaaa Allah ya cece ka,
Amin,
amin muna murna na har kullum,
Sannan
kuma Bello Koc,
Bello
Koc a gaishe ka ɗan girma
Bello
Koc a gaishe ka ɗan girma
Shiko
Bello na duba,
Baban
Hindo a gai –
Ohƙ!
Angon
Hindo na duba,
Angon
Hindo mai nasara ɗan girma,
Angon
Hindo mai nasara,
Allah
shi jaaa zamanin sarki.
Baban
Yasira ne,
Baban
Madi a gaishe ka,
Allah
shi biya ka nau Bello,
Baban
Sadiya a gaishe ka,
Kai
komai.
Baban Hodiyo
jarumina ne,
Yauwa!
Domin
Momi ina roƙo,
Bello
ka ba ni tau mota sabuwa kau.
Domin
Momi a ban mota,
Alu
gwamnan Sakkwatawa,
Dauri
‘yan ta-ɓare suna zwatci,
Yanzu
‘yan ta-ɓare suna gureman.
Dauri
‘yan ta-ɓare suna ihu,
Yanzu
‘yan ta-ɓare suna ƙugi ‘yan
nema,
Domin
Alu gwamna ya dawo,
Gaishe
ka mai dubun nasa ɗan girma,
Jama’ar
birni suna son,
Jama’ar
ƙauye
da na ohƙ!
Ko ta
inda niz zaga,
Aliyu
jarumi nau ne sun zaɓo,
Kuma
malamai suna ta faɗi suma, ohƙ!
Kutareee
had da guragu duk suna murna,
An ce
wa Aliyu ar riƙon Sakkwatawa,
Mai
dubun jama’a,
Kana
mai dubun nasa kai komai,
Alhaji
Bello Koc namu,
Yadda
kai Allah ya biyashe ka,
Kuma ɗan Alu gwamnan
Sakkwatawa,
Kuma ɗan Alu gwamnan
Sakkwata,
Girman
kuka ta banza ce,
Don mun
san ba ta yin sanwa,
Ko ɗai-ɗai.
Biri na
tsula an ce ohƙ!
Biri na
tsula mai jaddara,
An ce
koma a can daji ka yi noma,
An ce
aje jad darar taka ka yi noma,
Don mu
sam ba mu son samna ko ɗai-ɗai.
Da ɗan Maraduuuu
Mai
girma muna waƙa,
Don Ali
ag gwamna,
Muna ta
rawa muna ta kiɗa,
Aliyu
Aliyu,
Dogon
daji na gode,
Na
Aliyu na gode,
Na
Aliyu kaaa kyau,
Aliyu
Aliyu,
Dogon
Daji na Aliyu ag gwamna,
Na Alu
a gaishe ka,
Allah
shi tsare ka mun gode har kullum.
Allah
sarkin sarauta,
Allah
taimaki Ali Wamako,
Ko gida
bale daji,
Angon
Arziki mai dubun jama’a,
Angon
Murja mai dubun nasara,
Baban
Hodiyo a gaishe ka,
Ali
Wamako,
Baban
Madi a gaishe ka,
Allah
shi biya ka na gode kai komai,
Baban
su Yasira dattijo,
Baban
A’isha A’i,
Baban
A’isha A’i,
Ilela a
ban fata,
Domin mun
kama aikin gwamnoni,
Aikin
manyan wane yaro,
Yaro ka
ja gefe,
Bello
Koc,
Na Alu
a gaishe ka,
Allah
shi biya ka na gode kai komai,
Yauwaa!
Bello
Koc a gaishe ka,
Ɗa
ga Alu a gaishe ka kai komai,
Bello
Koc a gasihe ka,
Uban
Hindu da ranarka,
Angon
Hindu a gaishe ka kai komai,
Baban
Yasira na gode,
Baban
Mahadi a gaishe ka kai komai,
Baban
Sadiya a jaɓɓama,
Amadu
mun biyo hanyar fillanci.
Baban
Hodiyo na gode,
Ban
raina ma da girma ba kai komai,
Domin
Alu gwamnan Sakkwatawa.
Baban
Momi a gaishe ka,
Alhaji
Bello Koc namu ɗan girma,
Albarkar
Momi a ban mota ta yi.
Sakkwatawa
an yi ta ƙare,
Ko gobe
Aliyu ne gwamna sabo hul.
Sakkwatawa
an yi ta ƙare,
Ko gobe
Aliyu ne gwamna ya dawo.
Aliyu
jarumi,
Ban
raina da girma ba kai komai,
Allah
shi tsare ka na roƙa har kullum,
Allah
shi tsare ka na roƙa har kullum.
In dai
Alu shina gwamna,
Aman ni
ba ni jin kunya ohƙ!
Alhaji
Bello Koc namuuu,
Domin
babanka ag gwamna,
Mun
sami babak ka ag gwamna ɗan girma,
Nuna
mana to Alu gwamnan Sakkwatawa,
Ka ban
Makka ta hi min,
Iii Alu
gwamnan Sakkwatawa,
Kare na
tsula ɗan she, a’a.
To dai
a bar zagi,
Kare na
tsula na gan shi,
Biri na
gan shi can jeji,
Mun
gano muntansa ta heƙe ta yo ja,
Sai na
ce mai kwashe kayanka,
Je can,
Wai
birin Tawa zai koma,
Ya ce
min Tawa zai koma,
Buzun
Tawa an tsere,
Hag
gobe Aliyu ne gwamna,
Don shi
aka so kuma yad dawo.
Allah
mun gode ma,
Ka ba
mu jarumin gwamnaa,
Sadauki
mai cikonnn,
Mai
cikar magana,
Mai
cika da faɗi ohƙ!
Alu in
ya ba ka ya baka,
Halaye
nai idan ka tuna,
Halin
Sardauna ne garai,
Aliyu
na gode,
Allah
shi tsare ka mun roƙa har kullum.
Junaidu
mu’azu na ode,
Allah
shi tsare ka mun roƙa,
Sannan
ga injiniya namu,
Alhaji
Aminu na gode,
Allah
shi tsare ka mun,
Allah
shi yi yi ma Sarkin Musulmi,
Amin!
Aliyu
Aliyu Dogon Daji,
Na gwamna
Alu,
Na
gwamna Ali
Na
gwamna Ali,
In na
kamo waƙar Sarkin Yamma,
Da kuɗɗi yake ba ni,
Allah
shi biya ka na gode,
Dogon
Daji mai kirki.
Mu
komaaa sashen maigida,
Kuma
sashen mai dubun jama’a,
Kuma
ah! Mai dubun nasara,
Aliyu
na gode,
Angon
Murja a gaishe ka,
Angon
Arziki mai dubun nasara,
Ko gobe
Aliyu ne gwamnan Sakkwatawa,
Mai
gurmi muna waƙaaa,
Ga
Aliyu ag gwamna sabo hul.
Masu
farin ciki,
Ku taya
guɗa Alu gwamna ya dawo,
To ku
kuwa ‘yan baƙan muƙura,
Allah
shi tsare mu sheɗaniya ohƙ!
Allah
shi tsare mu sheɗani,
Kai
Aliyu ag gwamna sabo hul,
Baban
Madi a gaishe ka,
Baban
Hodiyo mai dubun nasara kai komai,
Sannan
baban Bello Koc,
Allah
shi biya ka naa gode,
Ah
Alhaji Bello koc namu,
Allah
shi biya ka na gode kai komai,
Don ban
raina ga girma ba,
Angon
Indo a gaishe ka,
Alhaji
Bello Koc namu,
Angon
Indo dattijo,
Angon
Indo dattijo,
Allah
shi biya ka nagode kai komai.
Baban
su Yasira na gode,
Baban
su Yasira na gode,
Baban
Madi a gasihs eka,
Baban
Sadiya a gaishe ka,
Baban
Sadiya da ranarka kai komai,
Babn
Hodiyo na gode,
Ban
raina ma da girma ba,
Ka yo ɗa,
Ka yo
min ɗa,
Baban
Momi,
Baban
Momi,
Momi
Allah ƙara girmanki,
Allah
shigwada mana ran auren Momi,
In
kwashi dau,
Allah
shi gwada mana ɗaurin auren Momi,
To muna
murna har fata,
Alabarkar
Momi na roƙa,
Kai min
mota ake ba ni,
To
albarkar Alu gwamnan Sakkwatawa,
To
albarkar Alu gwamnan Sakkwatawa,
Sakkwatawa
an yi ta ƙare,
Ko gobe
Aliyu ne gwamana sabo .
Canjin
kiɗa da rauji
Allah
dogaran Musulmi,
Mai
sama dogaran Musulmi,
Allah
ka ba mutum sa’a ko a ina yake,
Alu
Magatakarda,
Ɗan
Barade jaɓi,
Alun
Magatakarda,
Angon
Arziki a gaishe ka,
Godiya
nike yi,
Angon
Murja a gaishe ka,
Dattijo
Ali babana,
Aha!
Angon
Arziki masu arziki da yawa,
Na yaba
da ƙauna,
Baban
su Hodiyo,
Hana-ƙarya Aliyu baba,
Sannu
farin cikin Musulmi,
Farin
watan mutane Ali,
Ga
aljanna mai masoya da yawa a duniya,
Iiii
Alu ba!
Aljanna
mai masoya da yawa a duniyan nan,
In rana
ta futo gabas,
Tafin
hannu ba zai tare ba,
Mahassada
kullum,
Ƙaryarku
mahassada,
Kul ɗinku mahassada,
Domin
Aliyu namu shi ag gwamna.
Cikin
jahar nan esko haka,
Amadu
na ba da kyauta,
Baban
su Yasira Aliyu babana,
Baban
su Yasira Aliyu babana,
Baban
A’isha godiya nike yii,
Baban
Bello Koc a gaishe ka,
Aliyu
magatakarda.
Baban
Bello Koc a gaishe ka,
Aliyu
magatakarda.
Bello
Koc a gaishe ka,
Godiya.
Ina
angon Hindu na yaba mai,
Angon
Hindu mun yaba maka.
Allah
shi ƙara ƙauna,
Baban
su Yasira da kai mu kai,
Baban
Momi godiya da ƙauna,
Baban
Sadiyya, Aha!
Baban Halimatussa’adiya,
Baban
su Hodiyo,
Baban
Momi farin masoyi,
Baban
Momi farin masoyi,
Alhaji
Bello Koc gaishe ka,
Ga ɗan Maradu gurmi,
Farin
watan Musulmi,
Farin
cikin mutane Ali,
Alun
magatakarda,
Tauraruwar
gabas da harke,
Cikin
Musulmi,
Icen
agwara a bar matsa mai,
Don ka
san ba ya son garaje,
Ba ya
son garaje,
Alun
magatakarda,
Ga
rijiyar cikin daji,
Magatakarda,
Bayin
Allah su zo su,
Su ɗiba,
Kuma
tsuntsayen dawa su kurɓa,
Su sha
ruwansu sosai.
Amadu
godiya nake yi,
Angon
Arziki a gai da mai dubun jama’a,
Kuma
angon Arziki,
Mai
arziki da yawa,
Angon
Murja da kai muke yi,
Sannu
farin watan mutane esko,
Sannu
farin watan mutanen birni da ƙauyukansu,
Haba!
Yadi
Ilela mai kiɗa,
Shi ma
ga shi nan da ganga,
Mu dai
gaisuwa muke miƙawa ga ɗan Barade,
Ku ja mu
je kiɗanmu,
Sannunku
maga Aliyu Aliyu Dogon Daji,
Ga shi
zaune,
Allah
shi yi ma sarki Musulmi,
Albarkar
magatakarda,
Ya ba
ni ya daɗa min,
Albarkar
magatakarda,
Ya ba
ni ya daɗa,
Ban
raina da arziki nai ba,
Kai dai
ko ba ka yin Alu,
To
babanka na matsa mai,
To ko
ba ka son Alu,
To
babanka na kan so nai,
Koko ba ko ba ka son Alu,
Babanka
na matsa shi,
Idan
uban ba ya son Alu,
To ɗan ɗanshi na matsa mai,
Iii!
Alu
ikon Allah,
Ka wuce
gaban mamaki,
Baban
Hodiyo a gai da kai,
Alu
farin watan Musulmi,
Ga
aljanna mai masoya da yawa a duniya,
Alun
magatakarda,
Alhaji
Bello Koc a gaishe ka,
Godiya
nike yi,
Angon
Hindu da kai muke yi,
Angon
Hindu da kai muke, Bello Koc,
Baban,
baban su Yasira da kai ake,
Baban
su Yasira da kai muke yi,
Baban
Mahadi na yaba,
Ban
raina da arziki ba,
Baban
Halimatussa’adiya,
Da kai
muke yi,
Baban
Hodiyo a gaishe ka.
Bello
Koc masoyi,
Baban
Momi,
Baban
Momi,
Baban
Momi,
Allah
biya ka amin,
Amadu
ya yaba da kyauta,
To
Allah shi ƙara ƙauna,
Mun ce
tafiyar biri ga lilo,
Yaro ba
zai iya ba,
To ko
ya iya,
Mu nai
masa gyara da namu gurmi.
Canjin
sauti da rauji
Allah
Sarki Zuljalali,
Allah
taimaki mai gidana,
Allah
ka ba shirarre,
Ala shi
biya ka kullum,
Ban
raina mar da duk, ohƙ!
Aliyu
ka ba shirarre,
Tun
farkon farin Aliyu,
Mun san
ya danne ‘yan maza,
Aliyu
to ya danne ‘yan maza,
Saboda
gwamnanmu ɗan gari na gode,
Angon
Arziki jarumi,
Mai
arziki da yawa na gode,
Baban
hodiyo jarumina,
Allah
hi biya jarumina,
Baban
Mahadi ban gama da kai ba,
Baban
su Yasira jarumi,
Lillahi
ya taimaka shi raba ka da ‘yan,
Shi
raba ka da ‘yan-‘yan-‘yan,
‘ya’yan
tcegumin banza,
Shi
raba ka da ‘ya’yan tcegumi Alu.
Baban
A’isha A’i,
Ban
raina da kai ba.
Baban
A’isha A’i,
Ban
raina da kai ba.
Sannan kuma baban Bello Koc,
Sannan
kuma baban Bello Koc,
Shi
kuma Bello Koc,
Kuma
angon Hindu ne shi,
Kuma
angon Hindu ne shi,
Allah
shi biya ka na gode,
Baban
su Yasira,
Bello
Koc a gaishe ka,
Ya
Allahu shi taimaka ma,
Baban
su Yasira jarumin maza.
Baban
Mahadi a gaishe ka,
Baban
Sadiyya shirarre,
Baban
Hodiyo jarumina,
Jarumi,
Gaishe
ka baban Hodiyo jarumina,
Baban
Momi a gaishe ka,
Amadu
bai raina da girma ba,
Dogon
DFaji na gode,
Aliyu
Aliyu ka biya.
Idan na
ga waaƙar gwamna,
Ya ba
ni kuɗi ƙwarai-ƙwarai,
Har
riga da yawa ya aiko,
Allah
shi yi ma sarkin Musulmi,
Aliyu
Aliyu Dogon Daji,
Allah
shi biya ka na gode,
Domin
Ali Wamako ya ban riga,
Ɗai-ɗai-ɗai-ɗai-ɗai,
Has sau
goma sha huɗu.
Alhaji
Bello Koc,
Kai ko
albarkar Momi ƙilan,
Mu samo
kasaya,
Ko sabo
dal ko,
Da ni
da yarana guda biyu,
Domin
Bello,
Alhaji
Bello Koc,
Albarkar
gwamna Ali,
Kasiya
nike so ka bayar,
Da ni
da yarana guda biyu,
Domin Ɗan Barade jikan
Ummaru,
Domin
gwamna farin cikin masoya,
Allah
taimaka,
Allah
sa addu’ar da niy yi,
Idan
kuma ta karɓe mu mun ji daɗi,
Allah
shi tsare ka na roƙa,
Alu
shirarre,
Sabon
gwamnanmu ɗan karimɗa,
Sabon
gwamnanmu ɗan karimɗa,
Sakkwatawa
na farin ciki,
Zamfarawa
na farin ciki,
Kabawa
na farin ciki,
An ce
kuma Ali ya dawo.
Amadu Ɗan Maradun,
Mamakin
Ɗan
Maradun nay yo,
A dauri
dai ban bayyana ba,
Amma
sai na bayyana shi,
Har ga
tumaki ɗan Maradun,
Idan
Alu ya dawo,
Su ma,
Mun ga
suna murna,
Suna kaɗa bindi,
Ga Ali
har gida.
To
tsuntsaye suna murna,
Na gida
kuma har da daji,
Balle
mu,
Ban raina
ma da girma ba,
Allah
taimaka Wamako,
Domin
Aliyu ya dawo.
Alhaji
Bello Koc,
Haji
Bello Koc,
Albarkar
Aliyu sabo,
Da ni
da yarana guda biyu,
Da ni
da yarana guda biyu,
Allahu
shi taimaka ma,
Ban
raina ma da girma ba,
Mai
dubun jama’a a gaishe ka,
Gaishe
ka Aliyu sabo,
Angon
Arziki mai gidana,
Angon
Murja jarumina,
Baban
Hodiyo,
Baban
Mahadi a gaishe ka,
Baban
su Yasira,
Yasira
Yasira,
Idan
kin ji ni Yasira,
Mota
nake so ki sai min,
Idan
kin ji ni Yasira,
Ni mota
nake so ki sai min,
A’isah
Ala taimaka A’i,
Wajen
A’i ko,
Amadu
na yi mafalki,
An ce
haure na,
An ce
haurena ya ɗan rawa,
Na ce
haurena ka bar rawa,
Ga
A’isha, A’isaha,
To wataƙil bana Makka nay yi,
Tunda
dai ga A’isha,
To wataƙil bana Makka nay yi,
Sannu
Alhaji Bello Koc,
Amadu
ya gode da girma Bello.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.