• Akwai wasu mutane suna bacci, amma mala'iku suna rubuta musu zunubi.
• Suna addu'a amma Mala'iku suna
rubuta musu zunubi.
• Suna cin abinci amma Mala'iku suna rubuta musu zunubi.
• Suna tafiya amma Mala'iku suna
rubuta musu zunubi.
• Suna karatun AlÆ™ur'ani amma Mala'iku na rubuta musu zunubi.
• Suna sallah a kan lokacinta amma
Mala'iku suna rubita musu zunubi.
• Suna istigfar amma Mala'iku suna rubuta musu zunubi.
DALILI KUWA SHI NE:
Duk wani wanda yake bayyana al'aurarsa a Social media mace ko namiji ta
hanyar yaÉ—a hotunansa kowa ya kalla, musamman ma
hoton da yake wasu gaɓɓanki suka bayyana a cikinsa.
Irin hoton da za ayi shi da kaya masu kama jiki, ga kayan amma kuma suna
bayyana komai na jikin mace saboda É—ame jikinta da suka
yi, koda kuwa hijabi ne mai É—ame jiki ko
duguwar riga.
Duk lokacin da wani ya wannan hoton Mala'iku zasu rubuta miki zunubi, har
bayan ranki za a cigaba da rubuta miki zunubi, mutukar wannan hoton yana social
media ana ganinsa, to wannan shi ake kira da zunubi jariya, wato zunubi mai
gudana.
Idan kika saka hotonki, mai É—aukar hankali a
social Media maza suka kalla, duk wanda ya yi sha'awarki, to tun daga lokacin za
a fara rubuta miki zunubi, kuma gwargwadon adadin mutanen da suka kalla,
gwargwadon yadda za ki sami tarin zunubi.
Gwargwadon yadda hotonki ya daÉ—e a Social Media,
gwargwadon yadda zunubinki zai rinƙa
bibiyarki har cikin ƙabarinki.
Wannan shi ne zunubi mai gudana, yadda za ki aikata aikin alkhairi ya rinƙa samunki a ƙabarinki
bayan mutuwarki, haka za ki aikata zunubi ya rinƙa samunki a cikin ƙabarinki.
Yadda za ki aikata wani abu na alkhairi ayita tura miki lada kina cikin ƙabarinki, haka zalika za ki aikata wani aiki na sharri
kibarshi a nan duniya ayita tura miki da sakamakonsa har cikin ƙabarinki
Yadda za ka aikata zunubi a nan duniya ko ka koyar da wani aikin zunubi ka
mutu shi kuma yana nan yana aikata wannan aikin, to gwargwadon yadda yake
aikata aikin haka za ka rinƙa
samun sakamakon abin da yake aikatawa kana cikin ƙabarinka.
Idan ka koyar da wani aiki na saɓon ALLAH, wanda ka
koyar ya koyar da wasu, to duk yawansu, kaida ka fara koyar da aikin kaima za
ka rinƙa samun sakamakon abin
da suke aikatawa kana cikin ƙabarinka.
Masu koyar da maÉ—igo da luwaÉ—i,
masu koyar da zina mace da namiji, masu É“ata '‘ya'‘yan
mutane kuji tsoron ALLAH, lahira tasha banban da duniya lallai azabar ALLAH
gaskiya ce.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.
**************************
Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.