Ticker

6/recent/ticker-posts

Bai Hallata A Ce Wa Mai Azumi, Ya Ibada ?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun Alaikum, Dr wai wani malami ne yake cewa bai halatta mutum ya cewa ɗan'uwansa musulmi da azumin nan ba ya ibada ba, wai sai dai ya ce masa ya azumi, Dr. Meye gaskiyar wannan maganar ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Azumi ibada ne tun da Allah ya shar'anta shi ne saboda tsoransa, kamar yadda ya fada a suratul Bakara, Ibada ita ce duk abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi na daga zance ko aiki, na fili da na ɓoye kamar yadda malaman musulunci suka bayyana. 

Azumi ibada ne tun da Allah ya yarda da shi kuma yana nisanta wanda ya yi shi daga wuta, kuma ya keɓance shi da daraja ta musamman wacce babu irinta, kamar yadda hadisai ingantattu suka tabbatar, ga shi kuma sababin shiga aljanna, ibada kuma ita ce hanyar shiga ni'imomin lahira, wannan yake nuna  kuskuran waccar maganar da kuma karancin ilimin wanda ya fade ta.

Allah ne mafi sani.

✍️ Dr Jamilu Zarewa.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments