𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Warahmatullahi. Dr ina tambaya ne kan
halaccin sallar idi a gida ga waɗanda suke da halin yin haka, sakamakon rashin
yiwuwar zuwa sallar idi, saboda kasantuwar annoba ta corona virus. Allah ya
saka da alkhairi
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam. Sallar Idin karamar Sallah na daga
cikin Shariar Musulunci, Allah ya yi umarni da ita saboda hadin-kan Musulumai
da kuma godewa Allah bisa ni’imar Azumi .
Wasu malaman sun tafi a kan wajabcinta, sai dai a mazhabar Malikiyya Sunna ce mai
muhimmancin gaske.
Asali ana yin sallar Idi ne a Musallah a wajen gari, duk
da cewa ana iya yinta a Masallatai.
Malamai suna cewa wanda bai samu damar yin Sallar idi ba
a cikin Jama’a ya halatta ya rama ta a gida, shi kaɗai ko kuma cikin jam’i,
saboda abin da aka rawaito daga Anas dan Malik (Sahabin Manzo Allah) cewa: yana
rama sallar Idi a gida idan ta kufce masa tare da iyalansa da barorinsa, kamar
yadda Ibnu-abi Shaibah ya rawaito a Musannaf a lamba ta (5853) haka nan Baihaki
a cikin Sunan a lamba ta (6031), yana daga cikin Ka’idojin Sharia sanannu :
aikin Sahabi Hujja ne, mutukar ba’a samu Sahabin da ya Saɓa masa ba kuma ita ce
fatawar Ada’a bn Abi-Rabah daga cikin manyan Tabi’ai kamar yadda ya zo a
Sahihul Bukhari 1/334.
Bisa abin da ya gabata wanda yake jin tsoran Corona ko
kuma aka sanya dokar hana sallar Idi a jaharsa, zai iya yin sallarsa a gida,
idan za ka yi sallar Idi a gida za ka yi ta da sifarta ta raka’a biyu da karatu
a bayyane, da kuma kabbarori Bakwai a raka’ar Farko, shida a raka’a ta biyu, sai dai ba za ka Yi huduba ba.
Don neman karin bayani duba: Mugni Almuhtaaj 2/286
Allah ne mafi sani
Amsawa✍️
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.