𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin sallar idi, shin wanda ya ƙi zuwa da
gan-gan ya yi laifi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Malamai sun yi Saɓani a kan hukuncin Sallar idi abisa zantuka
guda Uku.
1. Zance Nafarko: Sunnah ce Mai ƙarfi, shi ne Mazhabar
Imamu Malik da Shafi'i.
2. Zance Nabiyu: Farillace wacce Wasu na daukewa Wasu, shi
ne Mazhabar Imamu Ahmad.
3. Zance Na Uku:- Wajibice a kan Kowanne Musulmi, wajibice a kan duk Wani namiji, Wanda yaƙi zuwa
batare da Wani Uzuri karbabbe ba, ya aikata zunubi, shi ne Mazhabar Abu Hanifa,
ruwaya daka Ahmad.
Waɗanda Suka zabi cewa wajibice su ne Shaikul Islam Ibnu
taimiyyah da Shaukany, da bin baaz, da Uthaimeen Allah ya jiƙansu da Rahama.
Duba Al-maj-mu'u (5/5) da Al-mugni (3/253) da Al'insaaf
(5/316) da Iktiyaraat Na shaikul Islam Shafi Na (82).
Masu Wannan magana sun kafa hujja da dalilai masu yawa
daka cikinsu akwai faɗin Allah madaukakin Sarki.
فصل لربك وانحر.
Ibnu Ƙudama ya
ce: Abun da ya shahara na tafsirin Ayar shi ne ana Mufin Sallar idi.
Wasu Malaman sukace: Abun da ake nufi da sallah a cikin ayar shi ne, sallah gaba ɗaya,
bawai Sallar idi kawai ake nufi ba.
Ma'anar ayar shi ne: Umarni da kadaita Allah da sallah da
yanka, saiya zama kamar fadinsa .
قل إن صلاتي ونسكي ومحياي ومماتي لله رب العالمين. الأنعام
162.
Wanda ya zabi Wannan magana wajan tafsirin ayar shi ne
ibnu jareer (12/724) da Ibnu kaseer (8/502)
Abisa Wannan babu dalili a cikin Ayar na wajabcin Sallar idi.
Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya UMarci A fita zuwa
sallar idi, Kamar yanda Bukhari (324) da Muslim (890) Suka Ruwaito daka Ummu
adiyyah.
Mata da yara da 'yan mata da Masu haila, Duk Annabi ya yi Umarni su fita Wajan Sallar idi,
a cikin hadisin..
Kafa hujja da Wannan hadisi wajan wajabcin Sallar idi shi
ne mafi Ƙarfin dalili a kan ayar da
ta gabata.
Kamar yanda Shaik Uthaimeen yatafi a kan Wajabcin Sallar idi a cikin maj-mu'u fatawa dinsa (16/214,) da
(16/217).
Hakama Shaik Bin baaz ya bayyana a cikin maj-mu'u fatawa dinsa (7/13).
Gaskiyar zance shi ne sallar idi wajibice a kan kowa, saboda dalilanta Sunfi ƙarfi
da hujja, kuma ya fi kusa da dai-dai.
Wanda yaƙi zuwa sallar idi da gan-gan, wannan asararrene
Kuma mai Saɓo, lallai zai Samu Zunubi mai girma na Ƙin zuwa sallar idi.
WALLAHU A'ALAM
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.