Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Wanda Bashi Da Ikon Zuwa Sallar Idi Yayita Agida?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Ya Halatta Wanda Bashi Da Ikon Zuwa Sallar Idi Yayita Agida?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله والصلاة والسلام على رسول الله.

Sallar idi farillace a kan dukkkan wani namiji wanda yake da iko.

Idan bazaka iya zuwa Wajan sallar idi ba, saboda rashin lafiya ta jiki, Babu komai akanka, To Shin an halarta maka kayita agid?

Akwai Saɓanin malamai akai, Jamhurdin malamai Sukace: ya halatta Saɓanin Hanafiyya, Muzni ya ruwaito daka shafi'i Rahimahullah A cikin Muktasarul Ummu, (8/125) Zai yi Sallar idi shi kaɗai agidansa da matafiyi da bawa da mace duk zasuyi Sallar idi agida.

Alkarshi Almaliki ya ce: Mustahabbine gawanda Sallar idi takubuce masa tare da liman ya sallaceta shi kaɗai, Shin a cikin jama'a zai sallaceta koshi kaɗai? Maganganu biyune Sharshin Kurshi (2/104).

Marudi A cikin (Insaaf) ya ce: Idan sallar idi takubucewa mutum Anso yaramata ayanda take, (Kamar yanda liman yake sallatarta).

Ibnu ƙudama a cikin "Almugni" Ya ce: Wanda Sallar idi takubuce masa yanada zabi, inya ga dama ya sallaceta ajam'i inya ga dama ya sallaceta shi kaɗai.

Ibnu Abidin Alhambali yaec: Bazai Sallaceta Shi kaɗai ba idan takubuce masa.

Shaikul Islam Ibnu taimiyya yazabi maganar Hanafiyya, Shaik Usaimin yarinjayar da ƙaulinsu A cikin Sharhin Mumti'i (5/156).

Ya zo Afatawa Lajnatul Da'ima (8/306) "Sallar idi farilla ce dawani yake daukewa wani ita, idan Wasu Suka yita waɗanda Sun wadatar Zunubi yafadi a kan Sauran Mutane.

Wanda takubuce masa kuma yanasan yaramata Anso masa hakan, Ya sallaceta a Sifarta batare dayin khuduba abayantaba, Kamar yanda Imamu Malik da Shafi'i da Ahmad Da Naka'i dawasunsu daka cikin malamai sukace, Asalin hakan shi ne fadin Annabi sallallahu Alaihi wasallam (Idan zakuje sallah kutafi kuna masu nutsuwa Abun da kuka riska ku Sallata Abun da yakubuce muku ku cikaso).

Da hadisin Anas bin Malik Allah yakara yarda dashi, ya kasance idan Sallar idi takubuce masa yana tara iyalansa da bayinsa, Sannan Sai Abdullahi bin Abi utbah bawansane ya yi musu sallah raka'a biyu, Yana kabbara a cikinsu.

Wanda yaje idi yatarar Angama Sallah liman yana khuduba, Zai saurari khuduba, sannan saiya rama sallar bayan khuduba danya haɗa Maslaha guda biyun, sallah da sauraren khuduba.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments