Daga Hafsatu Uwar Mumunai R.A) ta ce:
Haƙiƙa
Manzon ALLAH {ﷺ} ya ce:
Wanda bai kwanta da niyyar azumi kafin alfijir ba, ba shida azumi.
A cikin wani ruwayan Dara ƙuɗini
ya ce:
Babu azumi ga wanda bai farlanta shi ba daga dare.
SHARHI:
Wannan hadisi yana mana nuni da cewa idan mutum yanaso yatashi da Azumi
washe gari, to wajibi ne ya kwanta da niyyar Azumin a zuciyarsa, idan kuwa bai yi hakan ba, to ba shi da Azumin wannan
ranar.
ALLAH ka karɓi ibadunmu, ka gafarta mana zunubanmu
baki ɗayanmu Ameen.
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.