Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Mafificin Aikin Da Mai Azumi Zai Dinga Yi ???

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam

Mene ne Mafificin Aikin Da Mai Azumi Zai Dinga Yi ???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Aikin da ya fi falala ga mai azumi shi ne:

1. KARATUN AL'ƘURANI. Ma'ana ya lazimce shi dare da rana, kuma yadinga izna da abin da yake karantawa. Amma idan ba zai iya karatun Al-Ƙurani ba, to sai ya rinka lazimtar inda ake karatun Al-ƙur'anin ko fassarashi domin hadisi ya tabbata daga nana Fadima 'yar Manzon Allah da Abu Huraira yardar Allah ta tabbata a garesu sunce: "Mala'ika Jibrilu ya kasance yana bijirowa da Annabi Al'Kurani sau ɗaya a kowace shekara, sai ya bijiro masa dashi sau biyu a shekarar da zaiyi wafati. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito (1). (1) Bukhari K=66, Book=7, Hadith=4998 da Muslim K=44, B= 15, Hadith=2450.

Wannan yana nuna cewa karatun Al-ƙur'ani shi ne mafificin ibada a cikin watan Ramadan. Allah maɗaukakin Sarki  ya ce: "Lallai mun saukar dashi a daren Lailatul Kadari.

2. KYAUTA: Ya kamata mai Azumi ya yawaita kyauta wajen ciyar da jama'a, da sadaka, da taimakon gajiyayyu da makusanta. Kamar yadda ya tabbata a hadisin ibn Abbas cewa:"Annabi ya fi kowa kyauta, kuma mafi alkhairinsa yana yinsa ne a Ramadan yayin da yake saduwa da Jibrilu. Kuma ibn Abbas (R.A)  ya ce: Alkhairin Manzon Allah ya fi sakakkiyar iska".Bukhari ne ya ruwaito shi (2). (1) Suratul Kadari Aya1 (2) Bukhari K = 1, B = 5, da Muslim K = 43, B = 12, H = 2308.

3. NAFIL-FILI: Anaso mai Azumi ya yawaita Nafil Fili musamman

kiyamul laili Saboda hadisin Abu Hurairah yardar Allah ta kara

tabbata a gareshi  ya ce:Manzon Allah n ya ce: "Duk wanda yatsaya kiyamulaili yana mai imani, da neman lada; an gafarta masa zunubansa da suka gabata"..Bukhari ne ya ruwaito shi(1). Haka kuma Manzon Allah  ya ce: Wanda ya yi sallah dare tare da liman har ya gama za a rubuta masa ladan kiyamullaili. Kuma anfison duk wanda zaiyi kiyamullaili ya tsawaita tsayuwar saboda hadisin Khuzaifa (R.A) Targib Wattarhib wanda Albani yayiwa tahkiki lambar (1078). "Manzon Allah ya kasance yana tsawaita karatu a sallar dare a watan Ramadan fiye da sauran sallolin dare, yace, Manzon Allah yakan karanta Suratul Bakarah da Nisa'I da Ali'Imran a raka'a ɗaya, kuma baya wuce ayar da akayi tsoratarwa a cikinta sai ya tsaya ya roki Ubangiji tsari. Kuma bai gama raka'a biyu ba sai ga Bilalu (R.A) ya zo yana neman izni ayi sallar Asuba. Ahmad ya ruwaito wannan hadisin kuma ya ingan tashi.

4. YAWAN ZIKIRI DA SALATIN ANNABI : Abune mai matukar falala mutum ya yawaita Zikiri da Salati ga Shugaban Halitta irin wanda ya tabbata daga bakin Manzon Allah

5. CIYAR DA MAI AZUMI ABIN BUƊA BAKI: Yana daga cikin mafificiyar ibada mutum ya yi kokari wajen bawa ɗan'uwansa abin Buɗe baki saboda hadisin da Annabi yake cewa: "Duk wanda yaciyar da mai Azumi abin da zaiyi buɗe baki yana da kwatan kwacin ladan wanda ya ciyar batare da an rage ladan wanda ya ciyar ba".Tirmizi yace wannan hadisine hasanun sahih.

6. UMRAH: Yin umrah a cikin watan Ramadan ga wanda Allah ya bashi iko yana daga cikin Aiyukan da ake kwadaitar da mai Azumi yayi. Amma duk da haka bai kamata mutum yatafi umrah ya bar makwabtansa da danginsa da sauran mabukata a cikin yunwa da halin kakani kayi ba. Kuma ya kamata mu fahimci cewa, ciyarwa ita ce abin da Annabi ya fi bawa muhimmanci a cikin watan Ramadan.

Ya Allah kasa muna daga cikin wadanda za ka 'yanta a cikin wannan wata, domin darajar Annabi Muhammad

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/LsA4LWfGSme0umoxks5785

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments