Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shaƙa Hayaƙi Ga Mai Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Yar'uwata ce take fama da ciwon iska, toh kuma matsalar tana bata wahala sosai an bata maganin turaren hayaƙi, toh yaya azumin ta yake saboda idan ta yi turaren har cikin makoshin ta take jin hayaƙin kuma idan batayi hayaƙin ba, tana fama da jiki sosai.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ.

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،

Babu laifi ga mai azumi ya shanshani kamshi mai kyau, na abinci ko turare ko wani abun, sai dai kada mutum ya shaki hayaƙin bukuur, ko hayakin da yake taimakawa wajan dafa abunci, domin hayakin bukuur yana da wani sina dari na asali wanda yana iya wucewa zuwa uwar hanji.

Ya zo a cikin (Haasiyatul dasuki, 1/525) cewa: Duk lokacin da hayaƙin bukuur ko na tukunya ya wucewa mutum wajibi ne ya rama azumin, idan ta hanyar shakarsa ya wuce masa, shi mai dafa abuncin ne ya shaka da kansa ko waninsa ne ya shaka, amma idan ɗaya daga cikinsu yawucewa mutum zuwa makogwaro batare da zaɓin sa ba ko son ransa ba, babu ramuwa a kan wanda yake dafa abincin ko wanin sa.

An tambayi Shaykh bin Baaz rahimahullah: shin ya halatta amfani da turaren ita ce ko na feshi ko Bukuur?

Sai ya Amsa da cewa: "Na'am ya halatta da sharadin kada mutum ya shaƙi hayaƙin.

(Fataawa bin Baaz, 15/ 267).

An tambayi Shaykh Ibn Uthaimin Rahimahullah: Mene ne hukuncin amfani da kamshin turare da rana a cikin watan ramada?

sai ya amsa da cewa: "Babu laifi amfani da su da rana a watan ramadan kuma babu laifi ya shaƙa sai dai hayakin Bukuur kada ya shaƙa, domin yana da wani sina dari da yake wucewa zuwa uwar hanji shi ne hayakin.

(Fatawa Ramadan, 499).

Ya zo a cikin Fataawah Al-Lajnatul da'imah, 10/271. cewa "Duk wanda ya sa turare kowanne irin nau'i naturare da rana a watan ramadan alhali yana azumi, azumin sa bai lalace ba, sai dai kada ya shaƙi hayaƙin Bukuur ko turare mai kamshi kamar kamshin Almiski".

Saboda haka azumin ta nanan babu abunda ya sameshi domin bada zaɓin ta yake wucewa ba kuma abisa lalura take yinsa, musamman idan babu damar ta yi turaren da asuba lokacin sahur ya yi mata tasiri, amma idan tayishi lokacin sahur kuma yanai mata amfani wannan shi ne ya fi kuma ya fi kubuta daga kokwanto.

Zai lalata mata azumi ne kaɗai idan shaƙa takeyi da kanta, amma idan kawai tanasa maganin a kan garwashi hayaƙin ya bugi jikinta sai take jin sa a makoshin ta wannan babu laifi kuma bada zaɓin ta take yin hakan ba.

لا يكلف الله نفسا إلا وسعها.

Allah baya dorawa rai sai abunda za ta iya.

 

والله أعلم،

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I3vXUPymspzLawMCwJ44H2

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments