Hohonku ya Jamu'a!
Mu fito mu sa ƙuri'a
Mu zaɓi mai ƙana'a
Mai kyau na hali ɗa'a
Wanda bai da ‘yar lam'a
Ku mu ƙauracewa
ba'a
Dukkanmu mui Raja'a
A tulo ruwan Ƙuri'a
Mai gaskiyar rala'a
Shi za mu bai Ƙuri'a
‘Yancinmu ne Ƙuri'a
Mui gangamin bara'a
Ga mai siyan Ƙuri'a
Don kar ya samu Sa'a
Harma ya yo Sana'a
Ta siyan tulin Ƙuri'a
Ya Rabbullazi rafa'a
La tudrikuhus-sam'a
Gare Ka nai Adu'a
Shugaba mai ƙana'a
Wanda ke kishin Jamu'a
Mai tattalin Jama'a
Rabbana ka bashi Sa'a
Juma'a, 24 Faibrairu, 2023.
USMAN IBRAHIM BULANGU
09064862386
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.