Ticker

6/recent/ticker-posts

Haƙƙoƙin Aure A Bisa Alƙur'ani Da Sunnah - Darasi Na 34

MATSALOLI GUDA HUƊU DA MATA KE FAMA da su ACIKIN GIDAN AURE

1• Wata mijinta zai wadatata da abinci amma ba za ki sami farin ciki ba, ta hanyar a zauna ayi hirar soyayya ko shawara, koda yaushe ransa a ɓace, idan kin ga fara'arsa to yana buƙatarki ne a lokacin kwanciya, bayan ya sami biyan buƙatarsa to ba za ta ƙara ganin fara'arsa ba sai wani lokaci

2• Wani kuma babu abinci mai kyau komai sai haƙuri a gidan, kuma yanada halin da zai wadata matarsa da komai, amma kawai baya sakin kuɗi kowa ya wadatu a gidan, hatta abinci baya isar matarsa da ‘ya’yansu, kuma gashi da son a girmama shi, gashi da yawan bada umarni ayi kaza ayi kaza.

3• Wani kuma akwai komai da komai, akwai walwala akwai komai a wadace amma kuma baida lafiyar gamsar da iyalinsa, sai ayi sama da sati bai kusance taba, kuma idan ya kusanceta ma, baya iya biya mata tata buƙatar, shi indai ya sami tasa biyan buƙatar shikenan,

 Shi dai kawai idan ya kawar da tasa matsalar bai damu data matarsa ba, idan kuma tace ya nemi magani bazai nema ba, haka za su zauna tana cutuwa, watama harta ta je ta afkawa zina ko Istimina'i ko waninsa.

4• Wani shi kuwa matsalarsa yawan faɗa da hantara, abu kaɗan sai zagi, babu magana mai daɗi, kuma datayi masa laifi ƙarami bazai yi afuwa ba, sai ya ƙauracewa kwanciya da ita, sai ta yi ta bashi haƙuri yaƙi sauraronta, idan kuma ya fusata har dukanta zai iyayi.

 Lallai duk namijin daya suffanta da ɗaya daga cikin waɗannan ɗabi'un kuma yaƙi gyara ɗabi'unsa, to bazai kuɓata ba a gaban ALLAH harsai ya biya dukkan hakkinta dake kansa,

 Kuma zai biyata ne da ayyukansa na lada, idan kuna baida lada sai a kwashi zunubanta a lafta masa.

 Yaku maza muji tsoron ALLAH, mu daina cutar da ‘ya’yan wasu, lallai muma fa munada ‘ya’ya kuma munada ƙanne, dssr suma za a iya yi musu ninkin abinda mukaiwa na wasu.

ALLAH ka ba mu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments