Ticker

6/recent/ticker-posts

Kulafa’u

Kulafa'ur rashiduna

 Zana wake sai ku auna

 Don ku gane dai batuna

 Ba da wasa zana yo ba

 

 Sirikin Manzo Sadiƙu

 Ko Abubakari Atiƙu

 Baba ga uwar unuƙu

 Aisha ce ainu haƙƙu

 Walla zargi ba ga ke ba

 

Shi Badaɗi ne na Manzo

Ko a Ƙur'ani fa ya zo

Sahibi mai jure ƙwazo

Ko a kowasshe da ya zo

 Bai sake da Munafukai ba

 

Ya yi limancin Musulmi

Tun gabanin za ta yaumi

Ta wafatin Al-hakimi

Wa siraɗal mustaƙimi

 Ba a sam wani yai hakan ba

 

Ko a can gun Isira'i

Sanda anka yi yo nida'i

Ga Imamul Anbiya'i

Muryarsa ya yo sama'i

Ga waninsa ba ai hakan ba


USMAN IBRAHIM BULANGU

09064862386

Post a Comment

0 Comments