Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yi Sallar Tarawihi Da Earpiece

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu. Wata ce na ga za ta yi sallar tarawih sai ta kunna karatun Ƙur'ani tasa earpiece, wai sai ta rinka bin karatun sabida ta tsawaita sallar. shin yin hakan ba laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ƙwarai kuwa akwai laifi domin kuwa hakan da ta yi bidi'a ta yi babu wanda yasata yin hakan

Alƙur'ani yakamata ta dauka ta riƙe tana kallo tana karantawa, inkuma bata iya karatunba, saita samu wata sura wacce ta haddace koda ƙulhuwallahu ne, sai takama ƙulhuwallahu tayita maimaitawa taita maimaitawa, kai koda aya ɗaya rak ta haddace to ya halasta kiyita maimaita wannan ayar harki gama tsayuwar kamar ilahinnas misali wannan ayar a ce ita kawai ka iya a cikin alƙur'ani toh babu laifi kayita maimaitata har kagama tsayuwan darenda za ka yi, domin hadisi ya tabbata manzon Allah ya yi tsayuwar dare guda babu ayarda yake karantawa face wani yankin wata aya can ƙarshen suratul ma'ida, Intu'azzibhum... Wannan yankin ayar ita ce yayita maimaitawa har ya gama tsayuwar dare, kuma kasan dai tsayuwar Annabi ba irin taka ba ce.

Allah ya sa mu dace

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FMzmuMJvA9sLoGuKNyvJa0

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments