Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba A Yin Wutiri Biyu A Dare Ɗaya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum'm, don Allah Malam naji wasu sunce wai idan mutum ya yi wuturi a lukacin da ya yi sallah tarawi, toh wai idan zai yi nafila a cikin dare zai kara raka'a ɗaya ya cika wuturin da ya yi da sallah tarawi. shi ne nake neman karin bayani plxx malam??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, Annabi yana cewa ba awutiri biyu a dare ɗaya, Na'am akwai malaman da suka faɗi siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon shafa'i, tun da wutiri ɗaya ake yi a dare kamar yadda Ibnu Rushd ya ambata a littafinsa na Bidayatul Mujtaheed.

Amma abin da ya fi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama, wannan zai sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin.

Annabi yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare ta zama wutiri"

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FMzmuMJvA9sLoGuKNyvJa0

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments