𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam yaya hukuncin sallar jumu'a ranar
idi? Shin ta wajaba ko kuma bata wajaba ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ
ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ.
Idan mutum ya yi sallar
idi tare da liman, toh jumu'at ba ta
wajaba ba, yanada zaɓi guda biyu, idan ya ga dama ya sallace ta idan kuma ya ga
dama yabarta sai ya yi sallar
azahar. Saboda hadisai sun inganta.
ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ:
ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻴﺪﺍﻥ ﻓﻲ ﻳﻮﻣﻜﻢ ﻫﺬﺍ ﻓﻤﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﺟﺰﺃﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻭﺇﻧﺎ ﻣﺠﻤﻌﻮﻥ ﺇﻥ ﺷﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ. ﺭﻭﺍﻩ
ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ، ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﻮﺻﻴﺮﻱ: ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ ﻭﺭﺟﺎﻟﻪ ﺛﻘﺎﺕ.
Daga Ibnn Abbas Allah ka kara musu yarda cewa lalle
Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya ce: sallar idi biyu sun haɗu wannan rana/yini naku (sallar idi da
sallar jumu'at ke nan), Wanda yaso (idi) ta isar masa jumu'a, Amma mu za mu hadasu
(idi da jumu'a ke nan) in Shã Allah.
(Ibn Majah ya ruwaito shi.).
(Albuwaisriy yace isnaadinsa ingantacce ne kuma
maruwaitansa amintattu ne).
عن ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ: ﺍﺟﺘﻤﻊ ﻋﻴﺪﺍﻥ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺼﻠﻰ ﺑﺎﻟﻨﺎﺱ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﻥ ﻳﺄﺗﻲ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻠﻴﺄﺗﻬﺎ، ﻭﻣﻦ ﺷﺎﺀ ﺃﻥ
ﻳﺘﺨﻠﻒ ﻓﻠﻴﺘﺨﻠﻒ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻭﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ.
Daga Ibn Umar Allah ka yarda da su ya ce: Eidi biyu (jumu'a da Eidi) sun haɗu
a zamanin Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) sai ya jagoranci mutane
sallah (sallar idi) sannan yace Wanda yakeson zuwa jumu'a toh yaje (yayi
jumu'arsa), Wanda yakeso ya bazai yi (jumu'a) ba, toh kar ya yi jumu'a ɗin.
(Ibn Majah da Dabaraani suka ruwaito shi).
والله أعلم،
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.