Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin mai azumi zai iya shafa mai ko turare ko sanya kwalli?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Shin mai azumi zai iya shafa mai ko turare ko sanya kwalli?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam, Haƙiƙa mai azumi zai iya shafa mai ko turare ko sanya kwalli, saboda fatawar babban sahabin nan na Manzon Allah , wato Abdullahi Ibn Mas’ud inda ya ce: “Idan ɗaya daga cikinku zai yi azumi, ya wayi gari alhali ya shafa mai kuma ya taje kansa.” Sahihul Bukhari: babina 25, Kitabas-Siyām.

Imamus Shafi’ī ya ce: babu laifi game azumi ya shafawa gashin bakinsa mai. Domin shaƙar ƙamshi ba ci bane ko sha. Haka kuma, Imamu Ƙatādah ya ce: Mustahabbine mutum ya shafa mai domin ya kawar da ƙura daga jikinsa.

A cikin malaman mazhabar Malikiyya kuwa, Mutrāf, da Ibn Abdulhakam, da Asbag da Ibn Habib (Allah ya yi musu rahama) duk sun ce ya halatta a shafa mai, kuma basu bambance tsakanin mai ƙamshi da mara ƙamshi ba.

Haka kuma sanya kwalli shi ma baya karya azumi. Imamal-Zuhrī da Ibn Majīshūn da Laīth sunce: Babu laifi yin haka. Domin baya cikin abubuwan da suke karya azumi. Mafi yawan su kuma manya manyan malaman  mazhabar Mālikiyyane.

Allah ne mafi sani

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EYxwmBW9U2o1wckaƙ48MƘ4

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments