Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zubar Da Cikin Sikila Ko Waninsa

Malamai sun yi ijma'i a kan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

Amma sun yi saɓani game da zubar da ciki kafin ya kai wata huɗu, wasu sun haramta, wasu sun halatta wasu kuma sun karhanta.

Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata huɗu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin.

Sikila ba dole ya zama lalura ba, tunda ana iya haifarsa ya rayu, ya bautawa ALLAH ya amfani al'uma, don haka barin cikin shi ne yafi, sai dai idan aka zubar kafin ya cika wata huɗu saboda matsalar da ake tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa.

Ko kuma mace tana shayar da yaron da baiyi ƙwari ba, kuma saita sami wani cikin, gashi wanda take shayarwa ya fara shan nonon sabon cikin, sai ya zama yana cutuwa daga nonon, ita ma mahaifiyar tasa tana cutuwa sosai.

Sannan kuma ba zai yiwu a yaye wanda ake shayarwa ba, saboda ba zai iya cin abinci ba, to shi ma idan an rasa wata mafita, sai an cire cikin, ya halatta acireshi, mutuƙar baikai wata huɗu ba.

Sannan kuma ba za a ce anyi laifi ba, tunda bai zama mutum ba, kuma ba za a tashe shi ranar Alƙiyama ba.

Domin neman ƙarin bayani duba Ahkamu Al-janin Fil-fiƙhil Islami na Umar Ganam.

Ko kuma a yi mana magana ta private.

ALLAH  shi ne mafi sani.

*****************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments