Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Cikin Saduwa Da Mijina A Ramadan Sai Alfijir Ya Keto

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam muna cikin saduwa da mijina a cikin wannan wata, sai muka ji kiran Sallar Assalatu, mene ne hukuncin Azumin mu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ‘yar uwa, mutuƙar kuna jin kiran Sallar kun maza da sauri kun datse saduwar da kuke yi, to Azumin ku yana nan, amma in har kuka ci gaba da yi koda na second ɗaya ne, to Azumin ku ya karye, kuma za kuyi kaffara ku duka, idan kin yi masa biyayya, in kuma takura miki yayi, to zai yi kaffara ne shi kaɗai.

Duba Almugni: 3/65

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EYxwmBW9U2o1wckaƙ48MƘ4

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments