Ticker

6/recent/ticker-posts

Sadakar Da Allah Yake so Da Wacce Baya so

Haƙƙa ayoyin alƙur'ani mai girma sun zo da kwaɗaitar da Musulmi a kan ciyarwa saboda ALLAH a lokacin Azumi da lokacin da bana azumi ba.

Da taimakawa talakawa da mabuƙata domin yaƙar talauci a tsakanin al'ummar musulmai.

Kuma yin haka na ƙara tabbatar da '‘yan uwantakar musulunci a tsakanin musulmai.

Daga cikin waɗannan ayoyin akwai fadar ALLAH {S.W.T} cewa:

Waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana, ɓoye da bayyane, suna da sakamakon lada a wurin UBANGIJIN su kuma basa tare da kowane irin tsoro ko baƙin ciki a ranar alƙiyama.

[Surah ta: Baƙarah Ayata: 274]

Ku ciyar daga Abin da muka fitar muku na tsirrai daga ƙasa, kada ku nufi marasa kyau a cikinsa kuna ciyar dashi, alhali ku baku

karɓarsa, sai in kun daure kun runtse ido, ku sani ALLAH {S.W.T} mawadaci ne ga abin da duk za ku ciyar kuma wanda ya cancanci yabo ne a cikin ko wani hali.

[Surah Baƙarah Ayata:267]

Ba za ku samu cikakkiyar lada, har sai kun ciyar da abin da kuke so, abin da duk kuka ciyar na alkhayri, to ALLAH Masani ne game da shi.

[Surah ta Nisa'a Ayata: 92]

 Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

Lallai bawa ya taɓe kuma ya yi asara idan ALLAH {S.W.T} bai saka masa tausayin ‘yan Adam a cikin zuciyarsa ba.

[Silsilatus Sahiha: 456]

Manzon ALLAH {s.a w} Ya ce:

Duk wanda ya ciyar da mai Azumi da abin buɗa baki, yana da kwatankwacin ladarsa, ba tare da an tauye wani abuba daga ladar mai Azumin.

[Ahmad 4/114] [Tirmizi, Ibn Majah 1746].

Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

Aikin wanda yafi falala shi ne ka shigar da murna a cikin zuciyar ɗan uwanka mumini ko ka biya masa bashi ko kaciyar dashi.

[Silsilatus sahiha:1494].

Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

Kada ku ciyar da talakawa daga abin da Ku bakwa cinsa.

[Sisilatus sahiha: 2426]

Waɗannan ayoyi da hadisai dukkansu suna mana nuni ne da abubuwa guda biyu,

Falalar ciyarwa ga mai Azumi dama wanda baya Azumi.

Sai kuma nuni da hani da ciyar da ko sadaka da abin da kasan kai idan an ba ka ba za ka karɓa ba.

Kada ka yi kunu ko ƙosai da geron da bai da kyau, ko waken daya lalace, wanda ku ba za kuniya cinsa ba.

Kada ka dafa shinkafar da kai kasan bakacin irinta, kuma ka bawa wani ita sadaka.

Kada ka bayarda abin da kai inda an ba ka ba za kaci ba, kuma ba za ka karɓa ba.

Kada ka yi sadaka da shadda ko Atampha wacce kai idan an ba ka ba za ka iya sawa ba, a maimakon ka sami lada saika sami zunubi.

Kada ku ciyar da abincin daku bashi kuke ciba, bashi kuke ciyar da '‘ya'‘yanku ba.

Kada ku yi sadaka da kuɗin da ya fatattake wanda ku idan anbaku ba za ku karɓa.

Lallai kowa zai sami sakamakon abin da ya bayar wa mauƙata mai kyau ko mara kyau.

ALLAH ya baka da yawa kaima ka bayar da yawa, ALLAH ya baka abu mai kyau kaima ka bayar da mai kyau.

Ba aneman Aljannah da abinci mara kyau, da abinsha mara kyau, da kaya marasa kyau, lallai ALLAH mai shi ne mafi kyawu kuma yanason abu mai kyau.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments