Musan Hukunce-Hukuncen Fiƙhu [22] Hukuncin Sallah A Zaune

     SALLAH A ZAUNE

    Sallah a zaune tana inganta a nafila, kuma duk wanda ya yi sallah a zaune yana da rabin ladan wanda ya yi a tsaye, saboda faɗin:

    Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce: Idan mutum ya yi sallah a tsaye wannan shi yafi,

    Wanda kuwa ya yi sallah a zaune, to yana da rabin ladan wanda ya yi a tsaye,

    Wanda kuwa ya yi sallah a kwance, to yana da rabin ladan wanda ya yi a zaune.

    [Bukhari ne ya rawaito shi].

    Idan mutum ya yi sallah a zaune saboda wani uzuri babba, to yana da lada cikakke, saboda faɗin:

    Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce: Idan bawa ya yi rashin lafiya ko ya yi tafiya, za a rubuta masa ladan abin da yake aikatawa idan yana nan, baiyi tafiya ba, ko kuma idan yana da lafiya.

    [Bukhari ne ya rawaito shi].

    Sallah a zaune bata inganta a farillah indai zai iya yin ta tsaye.

    HUKUNCE-HUKUNCEN NIYYA

    Ita Niyya ba'a furtata a baki, ta alwala ce ko ta sallah, ana yin ta ne a cikin zuciya.

    Daga lokacin daka taso izuwa yin tsarki to tun a nan ka ƙudurci niyyar yin tsarki, basai ka furta abaki ba, na wanka ne ko waninsa.

    Daga lokacin daka ɗauki abin alwala, tun a nan ka ƙulla niyyar yin alwala basai ka faɗi a baki ba, domin baka ɗauki abin alwala ba, saida ka kudurta a zuciyarka za ka yi alwala domin kayi sallah.

    Sai dai yana wajaba a kan duk wanda zaiyi alwala ya ce: BISMILLAH, saboda faɗin: Manzon ALLAH {s.a.w} babu sallah ga wanda baida Alwala, babu alwala ga wanda baice BISMILLAH ba.

    [ Abu Dawud].

    Daga lokacin daka tsaya izuwa sallah, wannan tsaiwar taka bata yiwuba, saida kasa a ranka za ka yi sallar azahar ne ko la'asar, to tun a nan ka ƙudurci niyyar sallar da za ka yi, basai ka furta abaki ba, azahar ce ko la'asar ko waninta, ko nafila.

    Baya halatta a yanke niyya ana cikin sallah, wanda duk ya yi niyyar yanke sallah, wato fita daga sallah, to sallarsa ta ɓace, ya wajaba ya sake wata sabuwa.

    Wanda ya yi niyyar sallar nafila, to baya halatta ya mayar da ita sallar farilla yana cikin sallar.

    KARATUN FATIHA

    *******

    Wajibi ne a kan mai sallah ya karanta fatiha, koda kuwa mamu ne, a cikin sallar da ake bayyana karatu ne, ko wacce ake ɓoyewa, saboda hadisin:

    Ubada ɗan Samit (R.A) ya ce: Mun kasance a bayan Annabi {s.a.w} a cikin sallar asuba, sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya yi karatu, kuma karatun ya yi masa nauyi.

    Da ya gama sallar sai ya ce: Wala’alla kuna karatu a bayan limaminku?

    Sai muka ce: Eh, haka ne ya Manzon ALLAH {s.a.w}.

    Sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    Kada ku sake aikatawa, sai dai fatiha, saboda babu sallah ga wanda bai karanta ta ba.

    [Bukhari ne ya rawaito shi].

    ALLAH shi ne mafi sani.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    Duk mai neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.