𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Malam ina da tambaya, mu biyu ne a gurin mijinmu, amma ba mu a tare kowa da garinsa, mukan yi wata uku ba mu haɗu ba sai dai idan za a yi sha'ani tukunna mukan haɗu da juna, to sai wata rana ni na tafi garin da kishiyar tawa take da watan azumi, kuma a lokacin mijin namu yana gurinta, to irin tana zuwa sallar Tahajjud da karfe dayan dare (1:am), to a ranar ma ta tafi sallar, kuma ta tafi ta bar mu a dakinta muna kwance mu biyu da ni da mijina, sai bayan ta tafi sallah sai shi mijina ya nemi ya sadu da ni a gadonta amma sai na ki yarda, na ce ai wannan cin amana ne, to don Allah malam kin amincewan da na yi ina da laifi a gurin Allah? Saboda na roke shi ya yafe min idan na yi ba daidai ba, na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam, Allah ne mafi sanin dai-dai, amma ni
a fahimtata kin yarda da kika yi bai dace ba, saboda kasancewar da yardarta ta
tafi ta bar ku a ɗakin a kwance da ke da mijin naku, saboda ba sharaɗi ba ne sai a ɗakinki sannan zai
iya kusantarki da mu'amalar aure, matuƙar an sami kaiɗaituwar da ba
wanda ya san abin da ke gudana a tsakanin ma'aurata, saboda haka nake fahimtar ƙin amincewarki da shi a matsayin kuskure. Duk da dai
lamarin yana kunshe da shubhohi.
Ya tabbata a littafan hadisi da littafan Tafsiri cewa
Annabi ﷺ ya kusanci
baiwarsa Mariyatul Ƙibɗiyya a ɗakin Nana Hafsa a
lokacin da ta tafi ziyartar iyayenta, sai Nana Hafsa da ta dawo ta same su a ɗakinta, ta dakata
ba ta shiga ba, har sai da Mariya ta fito sai ta shiga ɗakin, da ta shiga
sai ta ce wa Manzon Allah ﷺ ya Manzon Allah a ɗakin nawa, kuma a kan shimfiɗana?
Sai Annabi ﷺ bai ji daɗin haka ba, a ƙarshe ya haramta wa kansa kusantar
Mariya, kuma ya ce kada ta faɗa wa Nana A'isha abin da ya faru, da kuma maganganun da
ya faɗa mata, sai Nana
Hafsa ta yi kuskure ta sirranta wa Nana A'isha abin da ya faru, da faruwar haka
sai Allah ya saukar da suratut Tahreem, wanda a cikinta aka gargaɗi Nana A'isha da
Nana Hafsa a kan wannan abu da ya faru, kuma aka goge haramcin da Annabi ﷺ ya yi wa kansa ba
zai sake kusantar kuyangarsa Mariya ba...
Abin lura a wannan ƙissar shi ne ba a zargi Annabi ﷺ da abin da ya
aikata na kusantar wancan baiwa tasa a ɗakin Nana Hafsa kuma a kan shimfiɗarta ba. Abin ma
da Allah ya ce shi ne: Don me yake haramta wa kansa abin da Allah ya halasta
masa? Duk da ba an ba da ƙofar yin hakan ba ne, amma wannan yana
nuna cewa idan lalura ta sa za a iya yin hakan, sai dai barin hakan shi ya fi
alheri musamman a irin zamantakewarmu na aure na wannan lokaci.
Domin samun cikakken bayanin sai a duba Tafseeeruɗ Ɗabariy ko Tafseerul Ƙurɗabiy, ko Tafseerul
Ƙur'anil Azeem na Ibn Katseer a ƙarƙashin surat Tahreem. Ko a duba Almu'ujamul Ausaɗ na Aɗɗabarániy hadisi
mai lamba ta 2316, ko Sunanud Dáruƙuɗniy hadisi mai lamba ta 4013.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.