Ticker

6/recent/ticker-posts

Daren Lailatul Kadari

Ya zo a cikin Hadisi, ana samun Daren Lailatul ƙadari a kwanakin mara na goman ƙarshe na watan Azumi.

A daren ashirin da daya 21, ko

Ashirin da uku 23, ko

Ashirin da biyar 25, ko

Ashirin da bakwai 27, ko

Ashirin da tara 29, da dare na ƙarshen watan Ramadan.

Nana A'isha (R.A) tace, Manzon ALLAH {s.a.w} yace: Ku nemi Daren Lailatul ƙadari a goman ƙarshe.

[Bukhari ne ya rawaito].

Ana so a yawaita addu’a a Daren Lailatul ƙadari, Nana Aisha (R.A) ta ce: Na tambayi Manzon ALLAH {s.a.w} Ta ce:

Ya Rasulullahi, idan naga Daren Lailatul ƙadari me zan faɗa a cikinsa?

Sai Manzon ALLAH {s.a.w} yace:  kice:

 

اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّى.

Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa’afu anni.

Ma’ana:

 Ya UBANGIJI, haƙiƙa, Kai mai afuwa ne, kuma kana ƙaunar yin afuwa, ya ALLAH kayi min afuwa.

[Bukhari da Muslim ne suka rawaito].

Sannan ka roƙi duk wata bukatarka, kayiwa iyayenka da dulkan 'ƴan uwanka addu'a.

Kayiwa ƙasarka da ƙasashen duniyar musulunci addu'a.

Daga cikkn waɗanda basa rabauta da wannan dare sune wanda suke gaba da juna, kana gaba da wani ko kina gaba da wata, don haka ku yafewa juna ko kun rabauta da wannan babban alkhairi.

ALLAH ka azurtamu da ganin wannan dare mai albarka.

ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Daren Lailatul Qadri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam Dan Allah meye alamomin lailatul qadari da falalarsa kuma Ya ake gane daren lailatul qadri?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

Allah ya fifita wani dare a cikin watan Ramadan ya ba shi wata daraja da ɗaukaka ta musamman, kuma ya keɓance shi da wata falala ta musamman wadda bai bawa sauran darare ba, wannan kuma zaɓi ne da ganin dama ne daga gare shi maɗaukakin sarki, domin yana yin abin da ya ga dama a cikin halittarsa.

Allah ya ce

لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِّنْ أَلْفِ شَهْرٍ

Daren Lailatul Qadari ya fi wata dubu alheri” (suratul qadri aya ta 3).

Ma’ana aiki a cikin wannan dare ya fi aikin wata dubu ba a daren Lailatul Qadari ba.

Allah Mai Girma Da Buwaya ya ce

سَلَامٌ هِيَ حَتَّىٰ مَطْلَعِ الْفَجْرِ

Aminci ne a cikinta har zuwa ɓullowa alfijir”. (Suratul Qadr Aya ta : 5)

Ma’ana dukkan wannan dare alheri ne, babu wani sharri a cikinsa tun daga farkonsa har zuwa ɓullowa alfijir.

Dare Ne Mai albarka. Allah Ya ce

إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ

Haqiqa mun saukar da shi a cikin dare mai albarka. Haqiqa mu masu gargadi ne”. (Suratul Dukhan Aya ta 3).

Abdullahi Ɗan Abbas ya ce, “Yana nufin daren lailatul Qadri”.

A Cikinsa Ne Aka Saukar Da Alkur'ani. Allah Yace

إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ

 “Haqiqa Mun saukar da shi a cikin daren Lailatul Qadri” (suratul qadr aya ta 1).

A Cikinsa Ake Qaddara Dukkan Abubuwan Shekara, Allah ya ce

فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ

A cikinsa ake rarrabe kowanne lamari abin hukuntawa” (suratul Dukhan Aya ta 4).

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kasance yana ƙara ɗamara a goman karshe, yana raya dukkan dararrakinsa, kuma yana tada iyalansa.

Wanda ya tsayu ma wannan dare yana mai imani mai neman lada an gafarta masa zunubansa da suka gabata (Bukhary da Muslim).

Allah ya ɓoye wannan dare don musulmi ya yi qoqari da himma a goman qarshe ta Ramadan, musamman ma a dararen da suke mara, waɗanda su ne daren 21, 23, 25, 27, 29, saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Ku kintaci daren Lailatul Qadri a cikin marar goman qarshe ta Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Wasu malamai sun yi bayanin cewa daren Lailatul Qadri yana yawo a tsakanin waɗannan darare (Wata shekarar wannan, wata shekarar wancan) saboda a yi aiki da dalilan da suka zo a kan haka baki ɗaya.

Dare Ne Mai Haske, Babu Zafi Ko Sanyi A Cikinsa. An karbo daga Jabir ɗan Abdullahi – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Haqiqa ni an nuna min daren Lailatul Qadri, sannan an mantar da ni shi, yana goman qarshe na Ramadan, dare ne babu sanyi ko zafi a cikinsa, kuma mai haske ne, ba zafi ba sanyi (mai cutarwa acikinsa)” [Ibn Khuzaima ne ya rawaito shi].

Rana Tana Fitowa Da Safiyar Daren Fara Tas Ba Haske Tare Da Ita. Yayin da aka tambayi Ubayyu ɗan Ka’abu – Allah ya yarda da shi – a kan alamomin daren Lailatul Qadri, sai ya ce, “Alamar da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ba mu labari ita ce, rana tana ɓullowa a wannan rana babu haske tare da ita” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Wanda ya yi tsayuwa daren Lailatul Qadri yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

An karbo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, na ce, ya Rasulallahi, idan na dace da daren Lailatul Qadri, me zan yi addu’a da shi? Sai ya ce, ki ce;

اللّٰهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّيْ

Ma’ana “Ya Allah kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi min afuwa” [Tirmizi ne ya rawaito shi].

Yan uwa! Wannan addu'ar ita za mu yawaita yi a cikin Wadannan kwanaki goma har mu dace da lailatul Qadr in shaa Allah, Addu'a ce da sunnah ta koyar.

Wanda Allah Yasa ya dace da wannan dare, to ya yawaita Ibada da Addu'a, Karatun Alkur'ani.

Allah ya datar damu da dukkanin alkhairin da ke cikin wannan dare mai albarka Allah ya bamu ikon lizimtar ta.

WALLAHU A'ALAM 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments