Ticker

6/recent/ticker-posts

Littafin Zakkah [02] Fa’idar Zakka Ga Mai Bayarwa Da Mai Karɓa

FA’IDARTA GA MAI BAYARWA

Zakka tana da amfani ga wanda ya fitar da ita ta fuskoki kamar haka:

1• Tana koyawa mai fitar da ita kyauta, ta fitar masa da rowa daga cikin zuciyarsa.

 Wato zai koyi yin kyauta ya bar rowa, rowa mummunar ɗabi’a ce wacca ke cutar da mai yin ta.

ALLAH {SW.T}  ya ce:

 Duk wanda aka kareshi daga rowar kansa, to waɗannan su ne masu rabauta.

Manzon ALLAH {s.a.w}  ya ce:

Ku kiyayi rowa, hakiƙa waɗanda suke gabaninku sun halaka ne ta hanyar rowa.

 [Abu Dauda ne ya rawaito shi].

2• Tana fitar da mai bayar da ita daga ƙangin bautawa dukiya, izuwa mallakarta.

Domin duk wanda zai tara dukiya amma ba zai iya bayar da ita ba, to bauta mata yake yi.

Ita, ta mallake shi, bashi ya mallake ta ba.

Manzon ALLAH {sa.w} ya yi addu’a mummuna ga wanda abin duniya ya tsokane masa ido, kamar haka:

Bawan dinare ya halaka, da bawan dirhami, da bawan riga ko mayafi, ALLAH Ya tuntsurar dashi ta fuska.

ALLH ya tuntsurar dashi ta ka,

Kai idan ma ya taka ƙaya, kada ALLAH ya sa ta fita.

[Bukhari ne ya rawaito].

3• Tana koyawa mai bayar da ita godiyar ALLAH a aikace.

Domin idan bawa ya sarrafa ni’imar da ALLAH ya yi masa ta umarninsa to shi ne ya yi godiya a aikace.

Idan har mawadaci zai dubi halin da matalauci ke ciki amma yaƙi taimaka masa, to babu shakka bai gode wa ALLAH ba.

4• Yakan sami ƙaruwar dukiyarsa,

Za ta yi albarka sosai ta zarce har ‘ya’ya da jikoki, wannan ita ce babbar albarka, kuma alkhairinta yana tafiya har lahira.

Kada kuma mu manta cewa ALLAH ya yi rantsuwa da cewa idan muka gode masa zai ƙara mana.

5• Yakan sami soyayya da ƙauna daga mutane.

Domin duk mai taimakawa mutane yana tare da samun ƙaunarsu.

 FA’IDA GA MASU KARƁARTA

Zakkah tana da fa’idoji masu yawa ta ɓangaren masu karɓarta.

Daga ciki akwai:

1• Wanda ya sami zakka, yadda ya kamata a bayar da ita, wato yadda ALLAH yace a bayar da ita, za ta fitar dashi daga talauci ko bauta ko bashi.

2• Tana tsarkake zuciyar matalauta daga yin hassada ga mawadata, da jin ƙiyayya da ƙyashi a garesu.

3.• Tana ƙara mutunci da kuzari ga wanda ya karɓeta.

Domin tsananin talauci yakan kawar da waɗannan suffofi daga mutane.

Musamman ma a wannan zamani da muke ciki.

ALLAH ka ba mu ikon aiki da abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments