Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne hukuncin yin wuturi a lokacin tarawih bayan kuma mutum yana son yin tahajjud cikin dare?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah. Malam mene ne hukuncin yin wuturi a lokacin taraweeh bayan kuma mutum yana son yin tahajjud cikin dare?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, in har mutum ya san zai yi wata sallar bayan tarawihi, to abin da yake dai dai shi ne ya jinkirta wutirinsa zuwa karshen dare saboda hadisin da Bukari da Muslim suka rawaito cewa: Annabi yana barin wutirin sa in ya yi sallar dare zuwa lokacin sahur, da kuma hadisin da Annabin yake Ku sanya wutiri sallarku ta karshe daddare” Bukari ne ya rawaito da Muslim.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DiXƘRlvdel9IbPpTvLEBYK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments